NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 5 of 42

tura abokina domin sanarwa Sarkin garinmu cewar abiyo bayanmu saboda ga tawagar kafurai tare da Keji waddaban yadda da shi ba ashekuwa wannan Keji dauke yake daku. Nan da kauyenmu babu nisa, mu je na isar da ku wajen Sarki domin a baku kulawa ta musamman' " Gimbiya ta ce "Mu na da nisa, sannan idan mun je kauyenku tamkar mun kai muku jaraba ne domin dole sai an bibiyi sahunmu, zuwa yanzu da ka tseratan da mu mun gode kabar mu mu shiga jeje mu tafi can wani waje inda ba za a taba gano mu ba mu boya har mu koma Kasarmu, ka sani cewa wannan tafiya da ake yi damu ita ce tafiya ta karshe zuwa birnin nan don kai mu in da ake bukatar kai mu,shi ne ka yi sa'ar dakatar da mu”. Koda Jarumi Umar Bin Abdallah ya ji wannan zance daga bakin gimbiya sai y ace da ita "Rayuwa kala biyu ce in ma a zauna a bature 12 | Page yi nazari mai kyau domin a samu a kubuta in ma a yi dirshan da shawara mara kyau daga baya a yi danasani,zuwa fadar Abdalla tsira ce daga gare ku, sannan Fadar Sarki Abdallah ba ta gudun Farmakin abokan gaba, ba kuma ta juya baya daga ceton mai nema, idan haŋ silar cetonku zai zame mana yaki, to za mu daura damara, idan kuma sulhu ne za mu zauna a kujerar sulhu ya ke gimbiya kada ki yi jiji dakai datakama ki biyo ni ba za ki tabe ba" Da Gimbiya ta ji kalamansa sai ta samu yadda da abin da yake fada mata amma a wata zuciyar sai ta ji wata kagawa ta zo mata don me zai yi mata Magana a haka ba ladabi. Don haka sai ta yi niyar kin daukar shawararsa. Duk da yayi gaba ya fara tafiya abinsa. Yar uwar tafiyarta wato Hadimarta HANZIYA ta dube ta ta ce "Ya ke gimbiya kamar muna neman mu yi wa kanmu rashin adalci, a hakika nin gaskiya muna neman dauki, ba don komai ba ko dan mu tsira da rayuwarmu da kuma fadawa Koma Sarki Nasir kin sani sarai matukar sun kai mu fadar Sarki Nasir duk wani takama da wani buri naki ya kare babu wata mafita da ta wuce mu bi wannan sadauki”. Gimbiya ta dube ta cikin alamun amsar shawarartada akasin haka, daga bisani ta ce "Haka ne amma bakya ganin yadda yake mana Gadara". Hanziya ta yi murmushi “Ki manta da iko da takamamuna halin neman ceton ne daga ubangiji kuma ya kawo mana wannan Sadauki, lallai bujirewa wannan kamar rashin godiyar Allah ne". Ba tare da ta kara cewa komai ba suka haye dawakai suka nufi hanyar da ya bi suna biye da shi yana gaba a bisa Doki. ** Birnin Bahara birnin albarka a wannan karni, kowane rai yana fatan ya kasance a cikin birnin Bahara, saboda kasuwancin dake gudana, sannan babu Kirista babu Arna, kowa yana iya rayuwa a cikin birnin ya yi kasuwancinsa, sai dai bisa sharadi karya dokar 1 bature 1 28 Page su kashe shi shi ne ya sa a wannan lokacin ba ni da wani sukuni tun fara ciwo yau gobe lafiya gabana ki faduwa". da Sarki yaHindu ta yi shiru cikin dan gajeren lokaci har sai da ta ji uwar dakin nata ta share hawayen ta ja shessheka sannan ta ce "Neman taimakon Hakimin Annur daidai ne a gare ki, domin shi mutum ne adali kuma mai matukar son gaskiya, idan Allah zai baka kariya ba da kansa zai zo ya baka kariya ba, amma shi ne zai zama sanadin haka, kin fi ni sani duk wani ilimi a wajen kin a samo shi, tsantsaini da tsoron fadawa halaka yake sawa kike wannan tunanin ai saka miki damuwar da kuma tunanin nemo wadda zai tsayawa danki ki dauka ubangiji ne yake haska miki, a da can ban da karfin gwiwa a game da Yarima Abbas amma wannan maganar take ta sa na fara jin karfin gwiwa, tabbas mu yi hanzari ka da mu yi kasa a gwiwa”. "Maganar ki gaskiya ce, wannan haka yake, to amma yake Hindu ya kike gani za mu yi wajen ganawa da Hakimi Abdullahi bin SHarjasllah, ki sani cewar matukar sun san wani shiri to za su gyara na su shirin, abin da nake tunani wani amintacce za ki nemo min wadda zai kai masa ziyara wadda shi da kansa Hakimi zai nemi yarima ni kuma zan gayawa yarima sakon da zai je masa da shi". ** Lokacin da Jarumi Umar ya iso babban turakar mahaifinsa, a daidai lokacin Hakimi na nazari game da bakuwar Suhaila bin ✓ Ababakari da kuma tunanin sakon da Sarauniya Hauletu ta zo masa da shi na son haduwa da Yarima Abbas. A wannan lokacin ya yanke kai ziyara babban birnin domin ganawa ta musamman da Sarki a game da sabuwar masarautar da ake rigima a kai, sannan kuma zai yi amfani da wannan dama ya gana da Yarima Abbas. bature 14 Page Ya tsaya yana jiran umarni daga Waziri Jafar. Batare da Jafar ya ba shi umarni ba ya mike tsaye cikin izza da isa sai da ya yi taku biyu zuwa uku sannan ya dakata yana kallon Jarfis sannan ya ce “Ina sokon da kake tafe da shi?" Jarfis ya gyara tsayuwa ya ce "An taho da Gimbiya zuwa wannan birnin zuwa dan takin lokaci yarana za su iso da ita kamar yadda ka umarta za a kaita masaukin da ka umarci a a jiye ta a can”. Waziri Ja'afar ya ce "Ka tabbata ka zabi kwararrun kuma masana wajen aiwatar da wannan aikin kamar yadda muka yi da Sarki Jarmusu Jakub". Jarfis ya ce "Kamar yadda ya umarce mu haka komai ya gudana, daga nan zuwa kowane lokaci dan
🏠