NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 41 of 42

mu sauye sauye na daga ci gaban musulunci, lallai Zakin da ya rayuwa a baya, zai ci gaba da wanzuwa a nan gaba, domin akwai bayin Allah da suka rayuwa suna kyautatawa suna aikin kirki amma a karshen rayuwarsu suka juya ba suka koma shaidanu, wa'iyazubillahi Ya Allah ina rokonka karshe na ya zama ya fi farko na kyawu, ya ubangiji ka agaji ne ka karfafeni domin na ci gaba da dira birnin Bahara a kan tafarki gaskiya da sauran kasashen duniya mu ci gaba da yadawa da'awa mu kai musulunci inda bai je ba". Ya zare takobinsa a dai-dai wannan lokaci ya daga sama yayi kabbara nan take wajen ya kaure da Kabbara "Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! Guri ya dauki shiru bayan an kaure da kabbara ana sauraren Sarki Muhammad Farsi. “Mun yi aike ga Benjamin yayi rashin ladabi ga dan aikinmu, duk da dan aikin ya kasance jinin sarautar birnin Bahara, wannan kuskure ne a gare su, kuma tsokanar fada ce bisa gayya a ka yi, ya zama dole mu kwace Hairama domin ta dawo karkashin ikonmu. bature 111 Page Babu musayar zance a tsakaninmu, babu yarjejeniya ko zama ashimfidar sulhu face kaifin takobi ta ratsa jini da tsoka domin mu kausasa su fahimci har yanzu Bahara na nan a raye bata mutu ba, tabbas sai an nufi Rum da gungun zunzurutun gawarwakin sama da dubu. Daga karshe ina mai sanarwa ga shugaban dakarunmu ya tura sako zuwa kowanne kauye cewa za a aje a kwace hairam, domin In danka mulkinta ga dana Yazid. Birnin da suka zubar masa da kima da mutumci zai zama jagoran birnin anan da kwana biyar masu gabatowa". Gaban gimbiya Siyama ya kara faduwa hankalinta ya kara dugunzuma dogon burinta na ganin danta ya mallaki birnin Bahara ya na neman ya salwanta saboda tabbas aka danka masa mulkin Haiman shi kenan sai idan har rabo ya rantse na tabbatuwar sa Sarki. A hargitse ta fice daga cikin dakin da take iya juyo maganganun da ake a zaman fada ranta a bace suka koma cikin gida. Daga wannan Sarki ya sallami kowa domin tun daga yau ba sai gobe ba a fara shiri duk wani mayaki ya gyara takobinsa duk wani maharbi ya gyara kwarinsa, mai duba lafiyar dawakan birnin ya ci gaba da aikinsa, makera masu kera makamai su wanzu batare da sun hut aba wajen samar da sabbin makamin yaki. Domin yaki babu fashi, don haka gari ya rikice da zaryar bakin kauyekan nesa, mata suka wanzu suna yiwa mazajensu shiri, mazaje suka dukufa wajen ganin sun barwa iyalinsu abin da za su ci su sha har Allah ya dawo da su, masu rauni suna kuka rabuwa da iyalansu. Yara wadansa karfinsu bai kai a fita yaki da su ba hankalinsu ya tashi suka koma gefe suna kunci da takaici domin babu yadda za su iya har sai jarumi ya kai shekaru ashirin a dokar birnin kafin a fita da shi yaki. Sarauniya Siyama ta rasa tsuntsu ta rasa tarko dole ne ta yi wani abin da zai haddasa dakatar da fita wannan yakin saboda yinsa babbar asara rayuwaka za a yi wanda kuma tana da tabbacin sai an yashe birnin Haiman an kwace shi ya kuma karkashin kulawar mijinta, tabbas yin hakan babbar asara ce a gare su, dole tana bukatar yin sirri da babu wani mahaluki da ya sani a cikin birnin Bahara, dole bature 112 | Page za ta fita ta gana da mahaifinta don ta san shi ma yanzu ya san yakin sannan hankalinsa yana dugunzume kamar yadda nata dugunzume me, dole ta shirya fita domin ganawa da shi ko da wata dabara da za ta hana wannan fita yakin. Ta kai gauro ta kai mari tana zagaye tana son ta samu yanay? mai kyau don ta tsayar da tunani da za ta yi amfani da da damarta kafin lokaci ya kure mata. Yanzu ne maso ma labarin Daular musulunci An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to downl
🏠