dubi juna, uwar gidan tata ta jinjina
mata kai alamar karfin gwiwa ita ma ta mayar da martani amma a
cikin dar-dar.
Har ta fita ta na kallon ta. Ta nufi wajen da zata samu ta tsirar
da rayuwarta gadan-gadan majiya karfi na biye da ita aikuwa cikin
sa'a sai ta fyalla da gudu bana wasa ba, su ma su ka bazama suna bin
ta ta cikin ciyaye take suka zare Kwari da baka domin su harbe ta a
kafada.
bature
9 Page
Dayan daga cikinsu ya sakankance cewar ya gama samunta
sai kawai ji yayi ya yarda kwari dinsa kasa ga mashi nan ya huda
hannunsa ya fito ta baya, ya kwala ihu, dayan bai san ta ina aka yi
wannan harbin ba sai ya zare takobi yana jiran ganin ta inda
maharbin zai fito, kwatsam bai yi aune ba ya gan shi a gaban wani
katon sadauki mai suffer karfi Karo Jarumi Umar yayi masa da kai
kawai ya baje kasa a sheme.
Nan da nan ya bi bayan wannan budurwa inda ta diririce ta
ma rasa hanyar da za ta bi. Kwatsam ta yi ido biyu da Jarumi Umar a
gabanta kamar wani ifiritu Aljani.
Abin duka take nema domin ta kwaci kanta ya ce "Kwantar
da hankalinki, bana daya daga cikinsu, wadanda suka biyo bayan ki
na kwantar dasu jinya suna neman agajin 'yan uwansu, tun dazu
nake biye da ku”.
Kafin ta yi Magana wasu masu, masu hatsarin gaske sun nufo
in da yake da alamar dauke masa numfashi, kai tsaye ya zare takobi
ya kifar da masu guda biyu zuwa gefe yayi a dingore zuwa ga
budurwa ya fille kafafuwanta don ta samu zaman dirshan ka da
kibiya ta same ta. "Kar ki motsa".
Abin da kawai ta ji y ace ke nan sai ta neme shi ta rasa ashe
waani tsalle ya sake yi ya fita da gudu kamar walkiya ji kawai ta yi
mai harbin kibiyar yana ihu sai daga bisani ta ji karar karyewar
kashinsa ɓass! Da sauri ya dawo gare ta "Ta shi mu je na kwabotar
da ke suna da yawa, su iya cimmana".
"Gimbiya" abin da ya ji ta faɗa ke nan".
“Gimbiya” ya nanata gami da duban Keken dokin da kuma
dakarun da suka durfafo shi "Bari na jarrabawa sa'a Da izinin Allah.
Abin da ya furta ke nan ya zare takbobinsa ya tunkare su kai
tsaye ba tare da tsoro ba Jarumi Umar yana ji da karfin jiki don haka
ne a duk lokacin da zai kai wa mutum hari to sai ya saka jikinsa ya
bature
10 Page
bangaje a matakin farko kafin yayi amfani da takobi yan fara ɓasgar
fuskarsa da ɓalla kasusuwansa, ta haka ya fara kafin daga bisani ya
hau sara da suka da haka ya bazar da mutum goma kasa batare da
sara ko suka ba, gadan-gadan yayi kan sauran sadaukan su ma suka®
nufo shi cikin shiri ba tare da ɓata lokaci aka yamutse mutum ɗaya
ya zamar musu kamar shaiɗan, ko wacce zuciya tunanin yadda za a
magance matsalarsa ake yi addu'o'I su ke yi domin ganin yadda za
su kwaci rayuwarsu daga hannun Jarumi Umar Bin Abdallah kafin
ka ce mene ne wannan ya bazar da ragowar dakarun saura
shugabansu da ke bisa doki yana zazzare ido da barazana “Idan ka so
rayuwarka ta ci gaba da tafiya a doron kasa ka sallama idan kuma ka
so ka bi sawun yaranka da suke kwance cikin jinya mu je zuwa"
Duk in da jarumi yake yi baya ganin gazawa kullum gani
yake zai iya domin a ganinsa shi ma za a iya tara masa dakaru sama
da hamsin ya bazar da su, kamar yadda Jarumi Umar ya yi don haka
sai ya kyalkyale da dariya ya ce “Kai Jarumin kauye masunci
manomi kai gani kake wani abin bajinta ne domin ka salwantar da
yarana, to maza bisa kanka".
Ya rugo da gudu ya na ihu cikin salo ya fara kaiwa Jarumi
Umar sara da suka, Jarumi Umar yana kare sara ya na mayar masa da
kwarewa aka samu rabuwa ta martani shima yana karewa cikin
dan lokaci kowa ya fuskanci lagon juna bai san waye Jarumi Umar
ba shi yasa yake tsammanin zai zo masa da wannan salon ammaa
lokacin da ya yiwa Jarumi Umar wata shiga sai Jarumi Umar yayi
walankeluwa ya zille masaya wuce cikin iska fuu amma sai ya
tangaje shi da kafada aikuwa wannan shugaban Barada yayi wata
mummunan faduwa tamkar ya yi karo da dutse, tsoro da fargaba suka
ziyarce shi a karon farko ya so ya saduda amma sai ya tuna shi ma
Jarumi,cikin a zama ya mike tsaye ya fara neman takobinsa ya gyara
mata riko ya kara dawo wani shammace Jarumi Umar yayi ya gabza
baturė
11 Page
masa naushi wanda yayi sanadiyar fitar hakoransa, yaransa da da
suka samu ikon fardaduwa daga dakuwar da suka yi suka rirrike
shugabansu.
"Mai girma Jesus mu gudu wannan ba mutum ba ne".
Ya na dagewa haka suka ja shi suka haye dawakai suka gudu
Jarumi Umar yayi godiya ga ubangiji da ya bashi nasara ko da ya
waiga inda budurwa take ashe tuni ta kwance yar uwarta daga cikin
Keji ta kuma fito da ita.
A hankali ya kara so inda suke su biyu suna kallonsa su kansu
sun tsora ta da lamarinsa Gimbiyar ce ta ce "Waye kai? Ka sayar da
rayuwarka a kan ceton ta mu alhalin baka san mu ba,mene ne
bukatarka?"
Maganar ta cikin izza ta masarauta, haka akwai tunkaho da
isa a ciki, wato dole sai don wata bukata za a taimake su.
"Ni suna na Jarumi Umar, daga kauyenmu zuwa in da na
hange ku babu nisa, na saka ido ne a kan tawagar ku saboda tunanin
akwai wani abu da aka boye na