NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 39 of 42

in idan da an yake su an gama da babin wata fitina, amma Ahlul kitab su ne suka yi uwa da makarbiya wajen tabbatar da wannan sulhu, a lokacin da Nabaru ya fadi gaban Sarki na wancan lokacin ya ce ka da a taba yadda da wannan sulhu tunda an nemi a farko sun ki suka fito yaki aka yake su. Amma Sarki da yake yana son zaman lafiya yana ganin abin kamar aikin gama ya gama an riga an ruguje su, sai ya yadda da sulhu tun kafin a je ko ina ana samun matsaloli kadan kadan daga Mangalawa, da suka tumbatša sai da suka nemi yadda za ayi a kasa dukiyar kasa a basu kasansu nan ma aka yi musu lamuni, akan wannan haraji an sha samun sabani da su, amm son zaman lafiya ake biye su, saboda a zauna lafiya. Yau ita ce ranar da irin Sadauki Nabaru suke gudu. Na tabbata ba alkairi ne ya kawo su Bahara ba, masu leken asirinmu sun tabbatar mana cewar sun kewaye kauyekan sashin nan domin su mamaye su, da tsokanar fada za su fara, don haka koda kayi yaki da su ko baka yi ba na san za su zodomin tuni labara ya zo sun bazo a ko ina, sai dai wata dabara ta zo min cikin raina yanzu a game da batunka". bature 106 Page 107 Page Hakimi Abdullahi ya jinjina kai ya ce "Ka tafi izuwa Kogon Sulkui kai da abokan tafiyarka, domin janye su daga cikin kauyen nan, saboda yara da manya za mu biyo sahunka ni da mayaka a yi karan batta a can, zanyi haka ne domin mu magance shirinsu na afkamana gari". Koda Jarumi Umar ya ji wannan batu sai dadi ya kamashi ya ce “Na ji dadin da ka fahimce ni ya mahaifina, zanyi duk mai yiwuwa wajen ganin na tsere musu har mu hadu a can Kogon Sulkui. Koda gama fadin haka sai ya mike cikin sauri ya fita ya samu abokansa ya tabbatar musu da cewar mahaifinsa ya aminta da shawararsa batare da sanin kowa ba suka haye dawakai suka nufi hanyar barin gari tare da neman hanyar da 'yan leken asirin Mangalawa suke labe domin gano waye Umar daga ina yake ina zai je. A lokacin da umar ya baro inda ya yake su a jiya kamar ya san cewar su biyo sahunsa sai ya sauka daga kan dokinsa adai-dai mararrabar hanyar da zata sadaka da hanya uku. Ya yanken reshen katuware bishiya ya saka igiya mai tsaye ya daure reshan sannan ya daure a kogunsa yadda zai zama yana janye da bishiyar idan yana tafiya a dokinsa har zuwa inda zai je batare da sun tantance sawayen dokin ba zai kasance yana tafiya reshen yana share sawayen dokin sannan sai ya ki bin mikakkiyar hanya yake bi ta tsakankanin koramai da ciyaye a haka ya je har gida, wannan dalili ne yasa da suka zo suka kasa tantance inda za su samu Jarumi Umar. Don haka ba za su tafi ba saboda suna zargin hanyoyin da yabi suna cikin hanyoyin da suke wannan waje to amma rashin tabbas yasa suka tsaya suna jiran abin da hali yayi don basu isa su koma su sanarwa da Shugabansu cewar basu ga wannan Jarumi ba domin amsawar mutuwa ce a gare su suna kwance cikin kwantan bauna irin na Mangalawa masana sirrin jeji sai suka ji sukuwar dawakai da karfi tana kusanto in da suke nan suka kara sunkuyawa kasa domin a tunaninsu wata runduna guda ceke tafe, bisamamakinsu sai suka ga wannan Jarumi da aka turo don zuwa bin diddiginsa a gaba wasu majiya karfi Jarumai na biye da shi suna sarrafa dawakai kamar tun da suka zo duniya basu da aiki sai tukin dawakai, sun wuce wajen kamar walkiya, aikuwa batare da bata lokaci ba suka kama dawakansu suka bi bayansu, basu suka daina binsu ba har sai da suka tabbatar da cewa sun isa Kogon Sulkui. Daga can nesa da su suna kallon lokacin da suka shige cikin wannan kogon. Koda ganin wannan ala'amari suka tsaya a can nesa sai daya daga cikin dakarun Mangalawa y ace "Mutum daya ya komaga Rundunar Ulgurt ka sanar da shi cewar ga inda wannan Jarumi yake don haka muna bature | Page saurarenku a nan idan kuma sun matsa daga nan wani daga cikin mu zai babu yadda za mu bari su bibiye su yayin da wasu za su jira harku kara so, bace mana". Suleman wani tsohon hakimi ne da a yanzu babu wani daga cikin masu mulki a daular Bahara da suka kaishe tarin shekaru don a kalla ya kai kusan shekaru dari da biyar mayaki ne na kwatace a zamani Sarki Farsi saboda haka yanzu ya kasance wani mutum mai fadi a ji a dukkanin Daular Fansi saboda girmansa da kuma dattako irin nashi. Hakimi Sulelam Bn Auyub na zaune a kofar gidansa bisa wani dakali da ya saba zama da jikokinsa yana musu tarihi sai dakaru da ke kewaye wajen don yin aikinsu, masu fita gona, masu fita kiwo duk in sun fito su kan zo su yi gaisuwa sannan su wuce. Yana nan zaune ya ji ihun mutu ne da guje guje dawakai jin hakan ke da wuya ya mike tsaye ya kuma fara tattara 'yan kanun jikokinsa da tattabekunnensa yana tura su zuwa cikin gidansa. Domin tun da ya ji wannan amsa kuwa ya san cewar hari ne aka kawo musu. Batare da bata lokaci ba dakaru suka cika a gabansa domin tsare lafiyarsa ya zare wata takobinsa domin shirin fafatawa da wadan nan mahaya da suka shigo cikin garinsa. Lokacin da yayi ido biyu da Mangalawa sai hankalinsa ya tashi ainun take ya umarci daya daga cikin dakarunsa cewa ya je ya
🏠