shinmu ni da kai ya bushe
sannan burinmu a kan Yarima Yazid bazai taba yiwuwa ba, abu na
biyu kuma yanzu haka Sarki ya fara zargin akwai wani kulli da aka
yi masa amfani da shi dan dauke hankali a kan mulkinsa da yake yi
kasalada gajiyawa da rashin maida hankali da aka yiwa
kwakwalwarsa aiki, ya fara tunanin neman magani don ya ce dani zai
nemi magani har ma a jiyan ya fita da yammaci na sa abin bayansa
bai tsaya ko ina ba sai gidan Shuhul Islam, bayan nan kuma suka
zaga gari suka dawo gida, yanzu ya kai Waziri Ja'afar mene ne abin
da kake ganin za mu yi domin magancematsalolin nan da za su saka
mu asarar duk tanadinmu?"
Waziri Ja'afar yayi a jiyar zuciya gami da cewa “Ranki ya
dade akwai babbar barazana da matsaloli da sai mun yi da gaske za
mu iya kawo karshensu, abu na farko shi ne rashin kwarewa ne muraran
yarima ya aikata wajen fito na fito da Benjamin, abu na biyu kuma ba mu
isa mu hana Sarki neman magani ba, idan har muka ci gaba da hanawa ko
Magana da likitocinsa ba kowane likita bane zai ji shakka ko tsoronmu
kamar yadda na baya suka yi, ba ma musan a ina zai samu likitan ba bare
mu yi tunanin wasu dabarun tsoratarwa ko zuba dukiya don hana aikin na
bature
105 | Page
hakika, a shawarce mu ja da baya, matukar ba so muke mu kwana kiyama
ba, mu taya Sarki neman magani idan ya so daga baya sai mu sake sabon
shiri".
Tun da ya fara Magana zufa take keto mata domin ta san dama zai
iya biyowa ta wannan bangaren domin shi kansa ta siye shi ne ta dalilin zai
ci gaba da zamaa matsayinsa na waziri matukar in Sarki ya mutu danta ya
zama Sarki, tana amfani da shi ne saboda soyayyarsa da mulki da kuma
kudi, da mugun kishin da yake da shi ga duk wadda yaga ya fishi kusanci
da Sarki, sannan ta sa Sarki ya yafe masa kurakure masu yawa.
"Kana ganin idan Sarki ya dawo hayyacinsa, zai ci gaba da zama
da kai amatsayin wazirinsa bayan akwai korafe korafe akanka da dama,, ka
da ka manta badakalar kasuwa, masarautar Shamnumda hadakar da kake yi
da kafurai".
Ya dube ta cike da mamaki, ya san ta san yana da alaka da
shamnum da wasu korafe korafe amma bai san ta san badakalar da yake yi
a kasuwa ba, da kuma hadaka da yake da su da kafurai. Nan take
hankalinsa ya tashi ya bude baki zai musa mata "Waziri Ja'afar babu wani
taku da kake yi a cikin masarautar Bahara da ban san da it aba, na zabeka
ne saboda na san za cika min burina na ganin mun gaji sarautar bahara
daula ta dawo hannun dana, idan har ka ce zaka juyamin baya kwana biyu
uku kacal yayi yawa kanka zai rabu da gangarjikinka domin kalma daya tak
na sanar da sarki na kafa shaidun na gaskiya kashinka zai bushe, ka ci gaba
da amsarumarni daga wajena mu gudu tare mu tsira tare”.
Ya saka babbar rigarsa ya share gumin da yake tsattsafowa daga
jikinsa hankalinsa ya kara ta shi y ace "Ranki ya dade wane ni na juya miki
baya, baki fahimce ni ba ne...."
"Na fahimceka, tunda za ka ci gaba da zama da Sarki a matsayin
waziri baka da damuwa, za ka koma kalallaba Yarima Abbas ka dinga yi
masa biyayya domin ganin cewar ya taka matsayin zama Sarki daga nan
shikenan ka tafi kabarmu duk ukubar da ta zo kan mu za ta afka, idan har
ka yi ganganci to la shakka kwana uku kacal mutuwa za ta yi maka
sallama".
Ta na fadin hakan ta mike daga inda take bata kara saurarensa ba ta
wuce cikin gida, jikinsa a sanyaye haka ya mike lallai mata shaidanu ne na
gasken-gaske zikirin shaidancin matan nan da su ya isa fada kwata-kwata
jikinsa babu kwari.
bature
Tun a daren jiya da Jarumi Umar ya dawo daga fafatawa da
Mangalawa ya zamana cewar cikin kauyen Nur suke cikin shirin domin
suna da tabbacin matukar sun fahimci daya ne daga cikin kauyan ya yake.
su,to babu shakka za su biyo sahu, don haka tun daga farkon shigowa garin
aka kara masu tsaro da masu kai rahoton farmaki, saboda kasancewar cikin
shiri.
Lokacin da Umar suka kadaita da mahaifinsa sai ya ce "Ya
Abbana, ka yi sani cewar zan iya ja da bataliyar Mangalawa guda ni da
abokaina, akwai yara kanana da mata a cikin birnin nan, saboda haka zama
na a tare da ku akwai babban hatsari, musamman in sun gano cewar ni din
danka ne, zai fi kyau da muhimmanci na fita daga garin nan na nausa wani
wajen yadda za su biyo bayana..."
Abdullahi ya jinjina kai game da duban dan nasa ya ce "Ya kai
dana, shin baka yi sani cewar rayuwa kashi biyu ta kasu ba, rayuwa ko
mutuwa, Mangalawa sun iso cikin yankin Bahara da mayaka runduna
runduna, wannan alama ce ta gagarumin yaki ya tunkaro kasar Bahara,
sulhu da Mangalawa ba zai taba zama alkairi ba, domin idan har
Mangalawa sun nemi a yi sulhu wahala suka sha kuma sun nemi sulhu ne
domin a kyale su su je su kara shiri. Allahi ya ji kan Sadauki Nabaru, a
waccan lokaci tarihi ya nuna cewar kada a bar kowane Bamangale a doron
kasa, matukar bai yi imani da ubangiji musulunci ba domin ba za su taba
saduda ba, a lokacin da yaki ya ci su aka kashe sama da kaso takwas cikin
goma na mayakansu, sai suka yadda da a zauna a yi sulhu, wadda a wannan
lokac