NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 42

ba?" bature 102 | Page Nan take Shehul Islam da Sarki suka kara nutsuwa domin jin amsar da wannan mutumin zai bayar sai ya ce "Ilimi kogi ne dan samari, ni ma a nawa bangaren ina da ja akan maganar malam Albardi to amma da nayi zurfin ilimi nayi bincike sai na gano cewar akwai litattafai na addinin Islama da aka kifar a ruwa aka salwantas menene dalili kifarda su, mene ne dalilin da yasa aka salwantar da su, dalilili yana kan litattafan malam albardi wadanda nan gaba kadan za su ke yawo a tsakaninku, da kanku za ku cimma wannan hujja”. Mutane suka fara maganganu a junansu har Malam yayi musu sallama haye Rakuminsa gami da tafiya yana mai yi musu murmushi cikin salama Sarki ya dubi Shehul Islam yace "Ya kake ganin za a yi da wannan kafirin?" Shehul Islam yace "Idan muka daure shi ko kama shi wani zai zo ya fara wa'azin cewar saboda zai fadi gaskiya an boye shi ko an kashe shi, abin da ya za mu yi yanzu mu baza idanunmu a duk inda za a yi wa'azi mu kirawo wadannan mutane domin zama dasu, a bainan nasi mu kunyata su mu karyata su da ilimi ba ta kaifin takobi ba, muna saka takobi a cikin wannan lamarin komaiya lalace". Koda Sarki Muhammad Farsi ya ji wannan batu sai ya jinjina kai ya kuma yi amanna da shehil Islam daga haka sukaci gaba dazagaye gari har zuwa daf da magriba adaidai kofar wani gida suka tsaya suna son su samu ruwan da za su yi alwala su yi sallah domin kada lokaci ya kufce musu. Suna nan tsaye suna tunanin abin da za su yi gida ne gua daya tal a wajen daga haka sai filaye Shehul Islam ganin hayaki yana tasowa daga cikin gidan ya ce "Da alama akwai mutane a cikin gidan nan don haka bari mu nemi su taimaka mana da ruwa domin mu yi alwala. Kafin ya ji ta cewar Sarki ya kwala sallama aka amsa masa dakyar daga jin murya tsoho ne ko tsohuwa. Suna nan tsaye suna jiran a leko sai ga tsohuwa tana takowa da sanda dakyar ta kara so gare su "Ku ne kuke sallama?" Suka amsa "Sannunki" Ta amsa "Yawwa, wa kuke nema?” bature 103 | Page "Shehul Islam ya ce "Muna neman ruwa ne domin sallah ta riskemu a halin tafiya”. "Sallah za ku yi?" Shehul islam ya amsa da cewar "Sallah za mu yi, ko akwai masallaci nan kusa?" "A'a babu masallaci, yanzu masu arziki sun rabu da gina masallaci, masarautu ma sun rabu da ginin masallaci sai gidajen rawa, gidajen bakin haure ma'abota littafi, daga nan tafiyar da za ku yi ku riski masallaci har sai kun danganta da cikin gari sosai". Sarki Muhammad Farsi ya ji kamar ta soka masa kibiya a cikin kokon zuciya, yaushe rabonsa da gina masallaci, a kullum da kodayaushe gini ake yin a bakikamaryadda ta fada". Su ka hada ido da SHehul Islam ya tuna lokacin da Shehul Islam ya ziyarce shi Idan aka ci gaba a haka ya Sarkin duniya za mu tsinci kanmu a koma baya sosai, mun bar gina Abubuwan ci gaban musulunci mun zauna muna gina rayuwar baki, ban ce baki kada a basu masauki ba, amma hakan kada ya dakatar da mu aikata abin da zai bawa addininmu ci gaban, makarantu don koyar da al'umma, masallatai don samun wadatar bautar Allah" Dukkaninsu sai da suka tuna wannan maganar a tare suka sauke ajiyar zuciya Sarki Muhammad Farsi ya dubi Shehul Islam a lokacin matar ta koma domin daukar musu ruwan alwala "Matukar Daular Musulunci ta fadi ni ne alhakin komai, domin ire irenku kun yi min bayanin da ya dace nayi dogon tunani da nazari amma hakan ya gagare ni, tabbas na cancanci tuhuma, na kuma amshe laifukana". Shehul islam bai ce da shi ko ta tafasa ba saboda a lokacin tsohuwar nan ta zomusu da ruwa suka yi alwala suka gabatar da sallah sannan suka ci gaba da tafiya ** Tun lokacin da Waziri Ja'afarya ji sakon da Sarauniya ta aiko masa da shi hankalinsa yayi mummunan tashi ko baccin kirki bai iya yi ba, haka washe gari ya kago rana ta raba domin ya samu isa wajen Sarauniya domin su tattauna abin da yake akwai aikuwa lokaci na isa bai tsaya bata wani dogon lokaci ba ya haye dokinsa sai gidan Sarki bature 104 | Page Muhammad Farsi. Yana isa kamar yadda yake cewar ya kagauta lokacin nan yayi ita ma sarauniya Siyamata saka hadimanta mafi kusanci da ita cewar a duk lokacin da waziri ya iso su sanar mata domin ta gaggauta fitowa dakin gani, aikuwa yana bargar ajiyar dawakai sai ga wani cikin masu yiwa Sarauniya hidima daga wajer gidan Sarki ya zo ga Waziri ya sanar da shi cewar yayi maza ya isa dakin gani tana saurarensa a can. J Batare da bata lokaci ba ya isa wannan guri. Babu wani dogon bayani ko gaisuwa ta dubi Waziri Ja'afar ta ce "Muna cikin babbar matsala da musifa abu biyu ya faru a lokaci guda wadanda dukkaninsa asara ce mu a wajenmu, Yarima Yazid yayi mummunan kuskure inda ya je ya fafata da Benjamin harma sun yiwa juna rauni, labara ya zo mana cewar Yarima Abbas ya isa birnin Shamnum ya kuma gyara dukkanin matsalolin da muka kunna a cikin birnin abin tashin hankali ace Sarki ya gano muna da hannu wajen zuga Waziri Ja'afarda mahaifiyar yarima Hilal, idan har Sarki Muhammad ya ji wannan a lokacin da ya nemo lafiyarsa ka
🏠