yake dan wane kauye ne".
Ya na gama fadin haka wani mutum biyar daga cikinsu suka
fadi gabansa "Za mu cika umarninka ya kai shugaba Ulgut,da iznini wuta mafi girman daraja”.
Daga fadin haka kawai sai suka mike suka sauya kamanin suka haye dawakansu suna tafe suna bin sawayen dokin Umar. **
Lokacin da Sarki Muhammad da Shehul Islam suka ajiye dawakansu suka nufi inda majalisar dattawan nan suke in da suke
tattauna al'amuran rayuwa sai Sarki Muhammad da Shehul islam
suka tsaya daga nesa kadan kamar suna jiran waani har ya zamana wadanan mutane basu lura da su ba domin hirar da suke yi ta dauke
musu hankali daya daga cikinsu yana Magana suna saurarensa dattijo
ne mai kimanin shekaru hamsin yake baya ni "Daular Dut ta ruguje
ne dalilin auratayya da Sarki Shamnar yayi, bayan ya bijirewa yan
uwansa ya aure bayahudiya a hankali ta dinga jawo 'yan uwanta
cikin masarauta har ya zmana Yahudawa sun yi tasiri a cikin sarautar
DaularDut suka dinga aiwatar da komai babu wadda ake jin
bature
P
99
maganarsa face ya hudu batare da kowa ya san yahudawan bane,
kuma a karshe majiya ta zo matarsa da ya auro ce take samar da su a
cikin birnin ta karkashin kasa tare da sahalewar wasu mutane a cikin
daular.
To ina mai tabbatar maka cewa sarautar Bahara idan has
Sarki Muhammad bai tashi tsaye ba, abin da ya faru a wancan daular
tabbas za ta iya faruwa a nan, duba da yanayin da kasar mu ke ciki
yanzu,ka duba fa ka ga, yadda dansa ne yayi tattaki zuwa birnin
shamnur ya samar da adalci ga 'yan uwan juna ya kafa mulki ya yaki
adalci ya kori tsinanne Waziri Adnan, shi yana kwance a gida banda
Hakimi ABdallah ya ziyarce shi da bai san da wutar da ake tonawa
ba".
Sarki da Shehul Islam suka dubi juna cikin mamaki da
taʼajjibin yadda maganar ta yadu a kankanin lokaci.
Jin za su ci gaba da katobara Shehul Islam ya ce "Ranka ya
dade mu je gaba❞
Har sun fara tafiya wani daga cikinsu yake cewa "Ba ma
wannan ba, yanzu ka duba fa ka ga, yawancin Kauyukanmu sun
daina shigowa da samarinsu zuwa kasuwancin babban birni tunda
ana shan giya, ana caca, ana yin duk wani nau’in zunubi har gidan mata masu zaman kansu akwai a boye a cikin birnin mai tsarki kamar
Bahara da shekaru da dama bayin Allah suka samar masa da nutsuwa
lokaci guda mutum daya ya ruguza mulki shi yasa Mahaifiyata ta
taba cewa da ni "Isma'il Farsi shi ne ya dace da mulkin Bahara
amma aka batar da shi aka wulakanta shi a wata majiyar ma ana
tunani sun haukatar da shi."
Hankalin Sarki Muhammad farsi yayi mummunan tashi a lokacin da aka tuna masa da dan uwansa Isma'il batare da SHehul
Islam fara tafiya ba shi ya fara tattaki ya bar wajen. karkashin Idan mulki al'amura munana sun rincabe a
mulkinka ka kasa gano mafit, ka yi badda kama ka sulale ka shiga cikin al'umma batare da sanin ko kai waye ba, domin duk lokacin da mulkinka yake kan doron zalunci ba zaka yi nisan kiwo ba za ga
bature
100 Page
101 Page
fuskanci matsaolinka, idan kuma mulkinka na tafiya daidai akan
gadon baccinka ma zaka iya fahimtal
Wannan tunanin ya fado masa a rai a lokaci guda, lallai yayi sakaci mai girma.
Tsakiyar gari suka nufa suka ga cincirindon mutane sun
kewaye wani farin mutum mai cikar kamala da haiba, yana sanye da tufafi farare tas, da rawani a kansa baki, kayansa har zuwa idon
sahunsa na kafa, da kyakkyawan murmushi a kan fuskarsa yana
bayani dalla-dallah. Basu zame ko ina ba sai a wannan wajen.
"Tabbas bayan annabi Muhammadu, babu wani annabi da zai
kara bayyana, kur'ani ya tabbatar mana da wannan shi ne annabin
karshen kamar yadda kur'ani ya tabbatar mana da cewar Annabi
Adam shi ne annabin farko. To amma fa ba ana nufin shi kenan
bayin Allah sun kare ba, shi kenan Allah ba zai kara turo wani ba,
bayan manzo, akwai mutane halittu da suke zuwa duniya da
karamomi su ma duk daga Allah suke, sannan akwai na'u'ikan
mutane masu daraja da suke zuwar da sababbin abubuwa wadda
Allah yayi musu baiwar da Ihlama Allah yana sanar da su, ta fanno
ni da dama yadda za su gyara waal'umma ibada, bayan wafatin
ma'aiki an samu sahabai da suka gyara wasu al'amura na addini,
jama'a da dama suna karyata Shehun malami Albardi Ibn Ru'uyan
wadda yau shekaru dari uku da rasuwarsa wadda ya zo da tabbatuwar
auren wadda ya bi addinin kiristanci ba daidai yake da wadda ya
zauna babu addini ba, ya tabbatar da kirista zai shiga aljanna kamar
yadda musulmi wadanda suka yi zunubi za su shiga aljanna illa dole
sai an saka su a wuta an an yi musu hukuncin da ya dace da su”.
Sarki Da shehul Islamsuka kalli juna gami da cewa
"Auzubillahi minalshaidanir raj'em" har Sarki zai motsa sai Shehul
Islam ya ce "Dakata ranka ya dade, idan har mun dauki mataki anan
dukka damarmakin da ya dace za mu rasa su, muna bukatar sanin su
waye su, daga ina suke? Mene ne ilimin da suke son isarwa....
Wani nutsattsen matashi ya ce "Malaman addinin musulunci
da suka gabata sun tabbatar mana da cewar duk wadda ya hada wani
da Allah kafiri ne, kuma kafiri ba zai taba shiga aljanna