NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 35 of 42

" Ta dube shi "Ba za ka iya ka". fada dasu kai kadai b azan taya "Idan baki yi maza kin je min dukkaninmu za mu iya rasa rayuwarmu, ki yi maza wannan ita kadaice mafita". Suna gudu a dawakai suna maganar ganin za ta yi masa taurin kai yasa ya dakamata tsawa “umarni nake baki ki tafi”. Takobinsa ya zare tashin farko ya kade wani mashi da yayi dokin wuyanta, har sai da ta yi wata 'yar kara saboda firgita. "Ki tafi". Ya kara maimaita mata ta karawa dokinta kaimi domin bin umarnin Umar amma tana tafiya tana juyo tana kallon yadda ya bi wasu mutum uku da suke son biyo bayantaya tsare musu hanya suka fara dauki ba dadi da su. Mangalawa suna damasifaffen naci da dagiya wajen yaki basa iya bijerewa umarnin shugabansu koda mutuwa ce ta gabace su. Don haka su ka rufe sun hana shi sukunikamar yadda ya hana ko dayansu ya bi bayan gimbiya Suhaila. Har sai da ta kuleya daina hangeta sannan ya kara rikon takobinsa "Ka mutu ka mutu ka mutu" a bin da kawai suke fadi. Yana da tarihin fada da Mangalawa domin tsananin yawansu, idan kana yaki da kadan akwai da yawa bisa hanya don haka dole ya yi aiki tukuru ya kararda wadannan mutum goman a cikin kankanin lokaci. Wani da ya raina Jarumi Umar ya fito cikin daukar numfashin Umar da niyar suka masa mashi, Umar ya goce ya daki bayansa, nan take ya fado daga kan dokinsa, kafin ya mike wani ma ya kara kusanto umar a fusace, da niyar Sarensa da gatari, cikin karfin hali Umar ya dake hannunsa gatarin yayi sama Umar ya riga shi kama gatari take ya sara masa shi a goshi ya barmasa shi a tsakiyar kai wanda ya fado daga kan dokin ya yunkura yana kokarin cillo Umar daga doki, kafin yunkurinsa Umar ya saka masa takobi a tsakiyar kirjinsa, duka a cikin dakika ya kamala kasha mutum biyu. bature " Wasu fusatattu hudu suka taso masa domin daukar fansar mutum biyu ya zabiri dokinsa yayi zarya da su domin su bashi sarari, yana jinjina takobinsa akan iska fusataccen ciki ne ya ma dogon mashi a hannu ya karaso yana ihu da karaje ya kawo suka ya goce, ya wuce fuu Umar bai yi sa'ar sare masa kai domin gocewa sarar da. yayi, hakan ya bashi damar jin kansa amatsayin wanda zai gama da Umar falan daya domin sun yi turmi daya kowa bai samu nasara ba. 3 Ya juyo da dokinsa kamar yadda Umar yayi suka fuskanci juna wani ma daga bayan Umar ya nufo shi domin su saka shi a tsakiya su lahanta shi, amma Umar sai ya kara gyara tsayuwarsa wancan dake gabansa saito dogon mashin ya kara sukwano dokinsa domin ya tsire Umar shi kuma daya ya nufoshi domin su hadashi su masa farat daya,cikin matsinancin wanda ko bamakami in har an hadu sai an ji jiki aikuwa Umar yayi amfani da dabara ya saka takobinsa ya dakemashi ya sauya mashin hanya take na bayansa shi da ya zo da mugun nufi sai mashin ya tsire shi a idonsa na hagu. Ya kwala ihu mai tsanani Umar ta dake dokin mai mashin dokinya ci kasa dakaren ya zube kasa kasa ta turnuke ta rufe masa fuska yana laluben hanyar bi idanuwan da bai kara bude su ba ke nan, Umar ya saka takobi ya dauke masa kai. Mutum hudu sun kwanta dama saura shida Cikin fushi shida suka zagaye umar nan take wajen ya karade da karar karafa idan wannan ya kaiwaUmar sara sai wannan ya kai masa suka da mashi, su shidan haka yake ji da su kamar wani shaidan gurin ya yamutse Umar da ya kara tunawa kowanelokaci za a kara turo wasu sai ya kara zama cikin kankanin lokaci ya barsu cikin munanan raunika wadda basu isa su biyo shi ba saboda sara da suka da ya dinga yi musu, yana da tabbacin sai dai rayawa ta Allah amma ba kowane zai iya rayuwa ba, ganin wannan nasara da ya samu yasa ya kara wa dokinsa kai mi ya bar wajen ya nufi Kauyensu domin zuwa ya kwantar musu da hankali kafin sui so kowa ya san su waye mangalawa addababbun mutane ne masu son kashemutane bagaira ba dalili shan jini duk wani wadda baya bautar abin bautarsu shi ne jahadinsu, zaman lafiya da su babbar asara ce a gare ku. bature 98 Page | Page Bayan Jarumi Umar ya bar wannan wajen da suka fafata yaki da shi da mangalawa ya bar wasu tuni sun jima da komawa ga Allah ya bar wasu suna zaune cikin jini da magagin mutuwa. Kwatsam sai ga tawagar shugaban dakarun watao Ulgut ya kara so. Ya sauka daga kan dokinsa yana duban matattun mutane da rayayye wadan da suke cikin mawuyaciyar rayuwa, Ulgut yayi ihu yayi gunji mai tsananin amsa amo, wasu kalamai marasa kangado ya ci gaba da furtawa kamar mai kokarin tayar da aljanu yana zazzare idanu yana muzurai, yana gama wadannan surutai nasa sai ya zare wata karamar wuka a jikinsa ya fara yankamagoraon raggowar dakarun da basu hallaka ba, daya bayan daya yana fadin "Rahmata tabbata a gare ku". Sai da ya gama wadannan surutai nasa sannan ya dubi dakarunsa “Ku tabbata kun nemomin labarin wannan jarumi da ya kashemin mutum goma daga cikin mutum dari da shugaba ya turo ni da su wannan yanki, lallai ko su waye sai an gurfanarmin da su na hallakashi sannan na kone kauyensu da duk ahlinsa, lallai a bi sahunsa a gano min ina zai je daga ina
🏠