NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 34 of 42

suna tafiya suna tattaunawa a cikin tafiyarsu ne aka zo wani majalisi inda wasu dattawa suke zaune suna hirarrakin yau da gobe da alamun makotan juna ne, Sai Shehul Islam ya ce "Mu ziyarci wancan majalisi ko za mu iski wani labarin sarautar birnin daga gare su ** Lokacin da Umar bin Abdallah ya fito daga cikin gida domin yin shirinsa na fita zagayen jeji kamar yadda suka saba shi da abokansa a kowacce yammaci suna zuwa Jeji su yi karamar farautar abin da za su zo da dare su gasa a naman da suka samo, suna gasawa suna ci suna hirarsu cikin aminci da kaunar junansu. Koda ya fito Shema'u na gefe guda tana kallonsa, har ya isa bargar dawakai ya kwance dokinsa ya jawoshi izuwa farfajiyar tsakar gidan. Ya saka masa siddi yana shafa gashin dokin, kamar ance daga kanka ya daga kai domin duba turakar da aka sauke su gimbiya Suhaila, dafda lokacin ta fito daga cikin turakar suka yi ido biyu sun dan jima suna kallon juna. Kunya ta kamata a lokacin da ta dawo hayyacinta ba, ta yi gyaran murya gami da karasowa inda yake. Shema'u tana tsaye wani haushi ya kamata ta ji kamar ta je ta shake ta ta mutu, dole sai ta yi maganin wannan yarinya dole ta fada cikin ranta. Gimbiya Suhaila ta kara so dauke da murmushi da kuma kunya rungume a fuskarta, kyakkyawa ce Suhaila a fagen kyawu, tana da zati da haiba matuka gaya tana shafa bayan dokin “Jarumi ina kake shirin tafiya?" bature 2 95 Page Ya tsaya da shafa wuyan dokin cikin murmushi ya ce "Yar Sarki zan tafita farauta ne ni da abokaina?" Ta daga idanuwanta dara dara kamarmadara farare sol ta kara da tattausan murmushi "Farauta a wannan lokacin?" Ya ji wani abu ya soke shi a cikin ransa hankalin kwance ya ji yana rage shakkarta domin yana ji a ransa akwai wani abu dangane da ita "Muna zuwa farautar yammaci domin samar da abin zai ta ya mu zama a daren da zai gabata". "Uhmm" Ta daina shafa dokin ta rike hannuwanta guda biyu waje guda "Yaushe ka huta daga doguwar tafiya da har zaka fita, farauta kar kamanta tafiya sa'a biyar ka shafe a hanya zuwa nan me zaihana ku hakura ku huta, hutu yana da dangantaka da samun karfin gobe”. Ya yi murmushi "Na so haka, to amma shi ma yawaita motsi yana kara samar da horarwa a kowane irin hali, ban sani ba ko abokan tafiya ta za su iya biyo don ban sani ba”. Tana tunanin wani abu a ranta amma babu lokacin nazari ta ji bakinta yana fadin abin da ke ranta "Dama za su ki zuwa su barka kai kadai". hakan". Murmushi yayi "Idan basu je ba ke zaki yi min rakiya?" Ya fada cikin karfin gwiwa domin yana tunanin tana bukatar Ta kara fadada murmushinta "Zan so na fita farauta domin na kara ganin salonka". Murmushi ya kara yi ya mika mata linzamin dokin don ta rike ya nufi bargar dawakai da murmushi a ransa ya jawo wani kyakkyawan farin doki ya ce "Batare da na ta kura sub a mu je nay o mana farautar?" Murmushi kawai ta yi ta kama dokin ta haye, shima ya haye nasa dokin suka jera Kubrat na daga cikin babbar turaka tana bature kallonsu, murmushi ta yi kawai ta jinjina lamarin domin ta gama karantar yanayin. Tun daga farfajiyar gida suka fara tafiya sai da suka fita cikin gari sannan ne ta zaburi dokinta domin ta jangwalo shi su yi tsere yanayin yadda ta hau kan dokin tun a fari ya fahimci kwarewarta da iya sukuwa, don haka bai yi mamaki ba domin duk ma'abocin doki mafi kwarewa ya samu fili to zai sake shi ne, bai gama murmushi ba shi ma ya rufa mata baya. Gudu suke suna kara dawakai kwari gwiwa suna tsale da shillo. Da wasa ya dauki abin har suka isa inda nan ne za su dakata amma bata tsaya ba yana mata alama da ta tsaya domin an zo gejin da tsallaka shi zai iya zama matsala amma bata fahimci abin da yake nufi ba, ya karawa dokin kaimi a karon farko ya tisa ta a gaba,daf da zai isa inda take ya hango wata rundunar mayaka marasa iyaka sun yanyame ko'ina tana waigensa bata Ankara ba tana kara tunkarar wadannan mayakan, batare da ya dakata baya ci gaba da zaburar dokinsa don ya hanata isa wannan wajen ya zamana bai fi kiris ya rage ta isagare su ta juya ta cigaba da kallon gabanta sai idon ta yayi tozali da dakaru sun tsaitsaye suna kallonsa har ma wani dake gabansu ya amshi kibiya ya saita ta yana shirin harbota. Umar yayi wata kabbara dokinsa ya shakan nata dokin ya ja hannunta don ta yi gefe aikuwa tana kaucewa kibiyar ta wuce fuu!. Ya sake hannunta ya ce da ita "Juya" A tare suka juya dawakansu suka kara zaburarsu a fusace "Zaki iya ko na dawo da ke nan?” Cikin nuna jarumta ta amsa "Mu je zuwa". Shugaban dakarun Mangalawa Sashin ULGUT ya dakawa wasu dakaru goma tsawa "Ku zo min da su". Nan take suka su ka bi bayansu a tsiyace gudu na kece raini aka dauka ana fafatawa ga harbi da suke yi da kibiya da jifa da mashi, hakan yasa zuciyar Umar ta karaya domin yana ganin Gimbiya Suhaila zata iya sarewa don haka ya ce da "Ki yi maza ki bature 96 Page 97 Page karasa gida abokaina ki sanar da su cewar ina cikin halin fada da Mangalawa lallai su kawo dauki kafin su cin min?
🏠