da yake bata karatu sai ya tunkari cikin dakin karatun.
Yana zaune a durksuhe da dalibai a gabansa sun tsirawa guri guda
ido inda yake musu bayanin game da addini, kai tsaye ya samu wajen
ya zauna a ka zagaye malam da shi batare da kowa ya fahimci wane
ne ba"
"Ilimi wajebi ne ga musulmi, domin da ilimi kadai ne zaka
fahimci wane ne addininka wane ne mahaliccinka, sannan zaka
fahimci wanene shugaban halitta, idan hark a bar kanka babu ilimi
lokaci zai zo da za a yi ta sabawa koyarwar ma'aiki domin kawo
rudu daga cikin addininmu, ga ka musulmi a riga amma kafuri a
zuciya, abin da zai kawo maka kariya daga wannan gubar ka san
Allah kuma ka san Manzanninsa, Annabi Isa (Alaihil salam) bawan
Allah ne, kuma manzon sa ne, wadda Allah ya turo domin isar da
sakonsa, ya isar sun kashe shi, daga bisani an sauya labarin me ya
faru, shine suke bautawa a matsayin Allah, wannan aikin shirka ne,
darasi ne a gare mu, da muka zamo a cikin al'ummar Annabi mafi
girman daraja a wajen Allah, akwai mushirikai da suka juya wancan
lamarin ya koma Allah, ba za su yi kasa a gwiwa ba za su yi ta kafa
siradi har duniya ta nade ba za su fasa ba, za su dinga danganta Allah
da Annabinsa, wasu za su yi kokarin canza labarin to amma ilimi
bature
kadai ne zai zame mana mafi amfani a rayuwarmu da ta al'ummar
nan gaba".
A nan ne malam ya dago kai yana duban dalibansa ya zurawa mutumin da ya zauna ido bai ganeshi ba har sai da ya dago kai sukayi ido biyu da Sarki Muhammad Sarki Muhammad ya yiwa
SHehul Islam alamun yayi shiru ya ci gaba.
Wani daga cikin dalibai ya ce "Ya shehul Islam an ce Ka
bautawa Allah shi kadai ka roke shi biyan dukkanin bukata ba za iya
rokon Annabin Allah ba kenan?”
“Shehul islam yayi murmushi ya ce "Allah da bakinsa ya
furta cewa (Ihdinalsiradalmustakin) babu wani wadda za ka roka
biyan bukata face Allah babu wani da zaka bautawa face Allah,
shirka ce ka hada Allah da wani. An je ma'aikin Allah yana fushi da
hani akan hakan, ya shaida mana cewa shi manzon Allah ne wato
dan aikin Allah ne, Allah mabuwayi yayi bayani a al'kur'ani game
da zuwan Annabi Muhammad,ya gaya mana fifikonsa da sauran
Annabawa, shi ne Annabi mafi daraja yi masa karya, kafirci ne, bare
kuma ka bauta masa ko ka hada shi da Allah".
Wannan mutumin yayi shiru ya ce "Malam ni daga Dusara
nake tafe yau kwana nan arba'in a Birnin Bahara, kuma ina yawaita
zuwa karatunka, duk inda na ji ana wa’azi na kan tsaya na saurara, na
ci karo da wani malami a dusara yana mai fadin “Idan har baka hada
rokon Allah da sunayen Annabi ba, to addu'arka ba za ta taba
karbuwa ba?"
Malam ya dube shi ya ce "Kamar yaya?"
"Ya ce Sai dole Annabi Muhammad (SAW) ya amsa sannan
Allah zai amsa."
"
?"
Malam ya furta kai tsaye ya ci gaba da cewa "Annabi
Muhammad (SAW) shi ne mafificin manzon a cikin Annabawan
bature
92 Page
93 Page
Allah kuma shi ne mafi daraja. Saba masa sabawa Allah ne, a cikin
saba masa kuma akwai masu yi masa kage, duk wadda ya yiwa
Annabi kagi ya kafirta, duk wadda ya bautawa wani ba Allah baya
kafirta, Ka so annabi mafi kololuwar soyayya ka bi dukkanin
umarninsa a cikin umarninsa ba za ka ci karo da shirya ko wani abu
da zai sabawa al'kur'ani saboda haka karya suke shi yasa nake sanar
da ku ku yi karatu, a cikin ilimi ne kadai za ku karkade wannan datti,
domin abubuwa suna da yawa wadanda suka nuna karya ce karara
ake yi masa wannan ya ta faruwa bayan wafatinsa, za mu samu
lokaci da daliban ilimi masu zuwa garuruwa don wa'azantarwa da
da'awa domin su fara yaki da irin wadannan muggun 'yan ta'adda
acikin addinin musulunci Insha" ya dan yi shiru yana duban jama'a
daga bisani ya ce "Za ku iya tafiya sai bayan magriba za mu dora”.
Bayan kowa ya watse a masallacin jikin gidan Shehul Islam,
Shehul Islam ya ce "Ranka ya dade kai ne da kanka cikin wannan
badda kama?"
Sarki Muhammad yayi shiru yana kallon Shehul Islam har
Shehul Islam yayi tsammanin akwai abin da Sarki yake nazari akansa
har yayi shirin yi masa Magana sai Sarki Muhammad ya ce "Ya kai
Shehul Islam, na zo gare ka ne domin ka gaya min gaskiya, ka kuma
gaya min laifukana da Hakimi Nur ne kadai ke iya tunkara ta ya
sanar da ni, a fadin duniya, na san ina da matsaloli da suke yawo a
cikin hakimai na, suna tattaunawa a junansu, talakawana suna
tattaunawa a junansu Sarakai suna tattaunawa a junansu, amma
matsalar da nake da ita ana tsoron tunkara ta da ita,wacce koma baya
nakai birnin Bahara, wane ci gaba na kai Birnin Bahara?"
Koda Shehul Islam ya ji wannan batu sai ya dago da kai ya
dubi Sarki ya ce "Ranka ya dade, na ganka cikin shiga ta badda
kama, ko zan iya mikewa mu tashi mu shiga gari mu zagaya majalisu
na talakawa, mu shiga kasuwa mu ji kukensu?"
bature
94 Page
Sarki Muhammad ya ce "Ba ni da karfin jiki domin yanayin
jikina amma zan jure ka shirya mu je?" Ba tare da bata lokaci ba Shehul Islam ya mike gami da zuwa cikin gida yayi shiri yadda ba kowa zai gane shi ba, ya fito ya samu sarki suka kama hanya a dawakai