.
Ta yi shiru tana wani tunani “Naji Mama ta ce ciwonka Sihiri
ne ba cuta ce daga Allah ba kirkirarta aka yi”.
"Me kika ce?"
Ta kalle shi "Na ji suna hira da Hindu, ta ce tana yi maka magani a boye batare da sanin kowa ba, tana addu'a tana tofa maka
duk ranar da ta kasance kana tare da ita, a turakarka".
Maganar ta dake zuciyarsa sai da har ya samu wani lokaci
sannan ya dawo hayyacinsa ya dubi Zahra ya ce "Na gaji da zama ki rike hannayena mu koma ciki, ga magriba nan ta karato”. Lokacin da sarauniya Siyama ta koma dakinta sai ta samu
kuyanganta abokiyar sirrinta ta kut da kut ta zauna ta rubuta sako
zuwa ga Waziri na bukatar son ganinsa cikin gaggawa da bayanin a
takaice abin da ya sa ta ke son haduwar ta su saboda kada yayi
kasala.
Da fitar wannan hadimar tata kuwa sai ga wata yar sako daga
shugaban masu aikin gidan zuwa gare ta. Ta shigo falon ta fadi ta yi
gaisuwar ban girma gami da cewa "Yarima Yazid ya dawo, yana
kwance a dakinsa".
bȧture
89 Page
Ta zaro ido cikin tsoro da fargaba "Me ya same shi me ya
faru da shi? Bata jira jin ba'asi ba ta riga wannan yar sakon fita daga
dakin ta fice zuwa sashin 'ya'yan Sarki maza ta wata karamar kofa
wacce ita take sadaka da bangarensu, kuma bisa al'ada babu wadda
yake shiga ta kofar sai Yarima shi ma sai yayi izini an kuma amshi
izinin nasa am bashi dama, iyayensu da 'yan uwansa mata na iya kai
musu ziyara duk lokacin da suka so, ta isa falonsa a lokacin yana
kishingide a kan gadonsa na alfarmababu riga a jikinsa ga hannunsa
an daure masa da wani farin kyalle" da sauri ta kara sa "Dana
Yarima, me ya faru da kai?"
Ta kama hannun tana kallo "Ba wani abu bane yanka ne kar
ki damu?"
"Me ya faru kagaya min wasu ne suka tare ku?"
"Shugaban dakarun Benjamin.. amma kar ki damu na bishi na
dasa masa ciwon da ya fi karfin wadda ya dasa min akwai katon
yanka a cikinsa?"
Tana kallonsa tana saurarensa cikin rashin fahimta "She
Benjamin ya iya yi maka wannan raunin a wane dalili kar ka bata
komai dana Sarki yana tura ku ne domin ku je ku gwada fasaharku ta
iya siyasa da da yadda za ku iya kwantar da kai ku samu nasara
wajen makiyanku, idan ya tura ku yaki, yana so ku je ku nuna
tsantsar jarumta ta damatsa, da karfintakobi, ammaa duk sanda ya
tura ku sulhu sulhun nan kadai yake bukata, ba yaki, me ka je ka
aikata ya kai dana".
Ya girgiza kai yana ciccije baki “Mama nasani, ki kwantar da
hankalinki, ba yaki nay i ba, Benjamin yayi haka ne domin ya turo
sako zuwa ga Sarki, don ganin sun shirya yaki Mama, sun daina
shakkar masarautarmu, saboda baba ya gaza tabuka komai, lokaci
yayi da Baba zai dauki kujerar mulkinsa ya dankamin domin kada
martabar kasarmu da Kalmar Allah ta yi kasa a wannan nahiyar
bature
90 Page
kasashen da suke tsoron koda inuwarmu yanzu suna iya fito na fito
da mu kaico"
"Ka tafka kuskure Yazid ka tafka kuskure wannan nakasu ne
wannan nakusu ne,me ya faru".
Duk abin da ya faru ya sanar da ita ta kama girgiza kai "Kayi
kuskure, wannan labarin ba zai je kunnen Sarki ba, dole a rufe baki a
kan maganar fadanka da Benjamin za mu basu labarin saranka da
yayi ne kadai a kafada".
"Ba ni da ko shakka ban yi wani abu a bisa kuskure ba, nay i
abu ne domin nuna karfin ran jinin musulmi Benjamin yana daukar
cewa shi zarra ne, na kuma ladaftar da shi na nuna masa ruwa ba
sa'an Kwando bane, ki kwantar da hankalinki babu wani abu da zai
sauya".
Ta ci gaba da girgiza kai “Baka san komai a kai ba Yazid,
baka san mene ne burin da manufar mahaifinka ba, tura ka gwaji da
yayi kai da dan uwanka yana son ya auna tunaninku da kuma
hikimarku ne, idan Abbas yayi nasara ba z aka taba zamowa Sarki
ba, domin Sarki zai bada sunan Yazid".
Yayi shiru yana kallonta "Mene ne idan Abbas ya zama Sarki
ni ban zama ba, me kike shakka da shayi, Abbas kani na ne, ina
alfahari da shi, idan har fi ni cancanta zamowa Sarki zan goya masa
baya kamar yadda shi ma na san idan na fishi cancanta zai goya min
baya".
"Baka da wayu baka san abin da kake yi ba Yazid, idan har
Abbas ya zama Sarki zai tarwatsa komai namu, zai salwantar da
ruhin duk wani dana a doron kasa?"
"A wacce hujjar, da dalili, waye ya gaya miki wannan Mama
ki guje maganganun irin wadannan domin rayuwarki zata zama
gajera, 'ya'ya Sarki Muhammad ne jikokin Farsi masu Sarauta daular
musulunci, tarbiya da kaunar juna a jinin jikinmu, take, matukar
bature
91 | Page
bamu zalunci dan uwanmu ko nuna masa rashin goyan baya, ko
fitowa mu yake shi ba na tabbata zai ba mu kariya zai kuma daga
darajarmu".
Ya koma ya kwanta tayi suroro tana dubansa wannan lamari
shi ke tayar mata da hankali bata da wata mafita illa ta fice daga
dakin zuwa ga jin ba'asi dangane da sakonta data aika.
Lokacin da Sarki Muhammad ya isa fadarsa sai ya yi wata
irin shiga ta irin attajirai ba sarakai ba, ba tare da kowa ya sani ba ya
fice ta kofar da ya saba fita in zai yi irin wannan fitar ta basaja. Kai
tsaye gidan Imam Muslim ya isa, tunda ya lura mutane na fitowa
daga dakin