NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 31 of 42

ane sha'ani batare da gajiyawa ba". Jikinta yayi sanyi tabbas ta gaddame masa yana dab da zargin wani abu, don haka sai ta karkace ta gyara zamanta ta kalle shi “Idan dama taki sai koma hagu maganarka gaskiya ce, fatanmu ka kasance cikin karsashi kamar koda yaushe?" Tana fadin haka yayi shiru idanuwansa na kallon guri guda, gaba daya hankalinta ya bar wajen jira take yi kawai Zulehat ko Hauletu su karaso cikin lambu ta mike dan zuwa ta sa a yi mata kiran Mustafa ta kuma gana da waziri. 'Yarsa ce Gimbiya Zahra, ta nufo lambon cikin ado barori biyu na taki mata baya, tsawon nisan tafiya taku gomasha biyu da inda Sarki yake barorin suka tsaya gami da sunkuyar da kawunansu kar, don kada su kalli inda Sarki yake, daga nan ne Gimbiya Zahra ta ci gaba da tafiya har ta iso wajen da ake tanadarwa mahaifinta dan hutuwa da yammaci sakaliya. Gimbiya Zahra ta sunkuyar da kai kasa ta yi gaisuwa ga mahaifinta, ya amsa mata cikin murmushi da nuna mata waje kusa da shi ya ce "Zo ki zauna”. bature 86 Page Ta tafi cikin ladabi ta samu wajen zama ta zauna daf da ashi ya dafa bayan "Ya Zahra ta, kyakkyawar diya ta, mene ne damuwarki?" Ta yi murmushi ta kalli Sarauniya Siyama dake a takure waje guda duk hankalinta ya dagule ta rasa mene ne abin da zata yi don magance matsalar da za a jefa su ciki. Ta tuna wasu lokutan can baya a lokacin da Likitan Sarki Mustafa ya fito daga sashin sarki yana kokarin duk damuwa ta dame shi adai-dai lokaci Siyama ta biyo bayansa bayan ta fuskanci ya fahimci abin da yake damun Sarki yaki yin Magana ne saboda bai san yadda maganar zata zama a cikin gidan ka iya yiwuwa ya yi laifin da zai ja masa kisa, ko wani dauren saboda babu wani likita amintacce da Sarki ya yadda da shi kamar Mustafa. ta yi sauri ta sha gabansa a lokacin da ta lura da babu mai ganinsu, su ka yi ido biyu gege domin da Mustafa. Mustafa yana muzurai yana kallon gefe da kadaice da matan Sarki matukar ba dakin gani ba haramun ne kuma kisa ne a kanka saboda hakan sai hankalinsa ya tashi. "Kwantar da hankalinka babu wani da zai gan mu”. Ya dube ta da alamun tambaya ta riga shi kara wata maganar "Akwai wani abu dangane da ciwon Sarki me yake faruwa?" Ya fara nuku-nuku ta daka masa tsawa "Ka fada min me ka fuskanta?" Babu yadda zai yi yace "Aikin sihiri ne, da aka yi amfani da shi a bargon da karkashin matashin kansa tsawon lokaci su ne suka haifar masa da ciwonsa, daga kwakwala zuwa karfin jiki, sihiri ne mai karfe da ya kashe masa karfin jiki ya kuma kashe masa karfin ^ nazari da hangen nesa". R Ta dube shi tana nazarinsa domin tana da sakon da zata bashi "Me kake tunanin aikatawa yanzu ina nufin me za a yiwa Sarki da zai samu lafiya”. bature 87 Page "Ina son sanar da likita kuma sirikinsa bin Abbas ne domin shi ne likita mafi rinjaye kuma yana aikin sihiri don haka shi ne kadai zai iya da wannan al'amari da izinin Allah". "Ibn Abbas, to ahir, ka da ka kuskura ka kawo wani cikin gidan nan domin kula da Mai martaba kai ne za ka ci gaba da kulawa da shi". Ya dubeta yana son yi mata cikakken bayani bayan ya hadiye wani yawo ya ce “Bani da kwarewar da zan iya magance matsaalar Sarki ranki ya dade, matukar ana son Sarki ya samu lafiya dole ne sai mun yi amfani da jarraba malamai wadanda suke da ilimi wajen yakar sihiri, wannan yana ci masa jiki zuciya da kwakwalwa za ta iya kai Sarki ya rasa hankalinsa wata rana ko kuma ya karfin lakar jikinsa ta daina amfani, hakan zai iya sawa a rasa Sarki". Ta Harare shi "Matukar ka sanar da wani wannan al'amari abin da kake tsoro shi zai faru gare ka, domin zan maka sharrin kai ne ka hadawa Sarki wannan sihirin idan kuma ka hakura ka ci gaba da bashi taimako zan saka maka da mafificin alkairi ko bayan babu rayuwar Sarki z aka ci gaba da kulawa da na Yarima Yazid. Cikin rudani da tashin dade?" hakali ya ce "Me kike nufi ranki ya "Ba sauri nake yi ba, na baka lokacin yin nazari da tunani, sakamakon bijirewa za a dauki rayuwarka kacokan daga duk ranar da ka yi tunanin sanarwa wani, duk sahun da zaka taka mutanenmu na bibiyar lamarinka dan haka tunaninka da yankewa hukuncinka a hannunmu yake" Tana fadin haka ta nuna masa hanya domin ya ci gaba da tafiya, sannu a hankali da sanyin jiki ya bar wajen.. Ta dawo daga wannan tunanin da ta yi hakan ya sa ta yi karfinhali mikewa domin fita daga lambon Sarki. “Ranka ya dade, bari na barka ‘yarka”. bature 88 | Page Batare da yayi mata Magana kai kawai ya jinjina mata ta mike ta fita barorinta na bakin hanya suka bi bayanta don mata rakiya cikin gida. "Baba tun da ka zama babu lafiya horar dani a matsayin jaruma ya tsaya, babu mai kula ni ko Yaya Yazid ko Abbas". “Uhmm shine damuwar, rabu da su kin ji farin cikin idanuwana, zan samo likita ingantacce domin kulamin da lafiyata, ko don na ci gaba da baki horo, ai na gaya miki za mu tafi yaki tare kina bisa doki da takobi a hannunki kina wulwalata sama kina cire kan munafukan Allah ta Allah' "Da gaske Baba?" "Sosai"
🏠