NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 42

a fara shawartarsa a game da wani abu dangane da gimbiya Suhaila bin Ababakari, amma bangaren zuciya mara karfin gwiwa na bashi labarin matsayinta da na sa matsayin wannan tunanin ya dawo masa da mafarkin da yake kokarin dorawa ransa. "Dan uwana rabin raina”. Muryar Hamdiya ya karade kunnuwansu kuma ya dawo dasu cikin hayyacinsu, cikin rashin gaskiyar da gimbiya take ciki na tunani dole Hamdiya ta fuskanci abin da ke wakana don haka ta yi sim-sim ta bar wajen. Ya dubi Hamdiya, da take kokari yi masa Magana "Ban san me yasa kake son ka bada rayuwarka ga mutunen da basu da amfani a gare k aba, dan uwa na sha kukan rashinka". bature 82 Page 83 Page Ya dube ta duba na mamaki "Ban fahimta ba,su waye basu da marasa amfani a rayuwata?" Ta juya ta dubi Gimbya da takekokarin shiga cikin gida shi maya kalle ta tare da suka dawo da dubansu ga juna ya riga ta Magana ya san abin da take son sanar da shi “Kin ga Hamdiya rayuwarta ta kowane dan adamce matukar ya bada gaskiya ga ubangijin talikai, babu wani dan adam da za a zalunta ina kallo batare da na taimakeshi ba, ina so ki koyi hana kanki shiga cikin lamurana, ki zauna a matsayinki na 'yar uwata, ki koya wa ranki sanin cewa ban taba fita daga gida da saka san cewa lallai zan dawo na same ku ba, saboda haka ban saka ki lalubamin mutanen da suke da muhimmanci ko wadanda basu da shi a cikin lamurana". Yana fadin haka ya bar wajen ya bata waje tana kallonsa kamar ta fasa ihu don takaici. ** Sarki Muhammad farsi Farsi shugaban kafatanin nahiyar larabawa a zamaninsa, yana zaune cikin kulawar matarsa Siyama tana shayar da shi kayan alatu a kyakkyawan lambon gidansa suna taba hira sama sama, ta lura da akwai tarin damuwa ga Mijinta Muhammad Farsi, don haka sai ta fara tunanin ta yadda za ta shawo kansa ya sanar da ita damuwarsa, saboda ita ya nuna mata kaguwa da son sanin damuwarsa zai iya share ta, ta kawo maganar barin 'ya'yansa birnin don zuwa cika aikinsa, ta fahimci damuwarsa ba ta wannan bangaren bane, saboda haka sai ta tuna da zuwan Abdullahi bin bin Sharjas da ya zo garin yau kwana uku da suka wuce don haka sai ta fahimci lallai akwai wani abu dangane da zuwan nasa a cikin bacin ran Sarki, ta yi nisa ta mika masa wani karamin kofi da yake cike da tataccen ruwan inibi, bayan ya amsa ta ce "Zuwan Abdullahi bature 841 Page bin Sharjas birnin nan ya zo da batutuwa da dama, a game da zargin Waziri Ja'afar, ya sarkin duniya mai kake tunani game da lamarin?" Kamar ta sosa masa inda yake masa kaikayi, ya kurbi lemon ya mika mata kofin ta amsa ta ajiye a gefe sannan ya ce "Rashin walwalar da nake ciki ta rashin jin dadin jikina a shekaru biyu baya zuwa yanzu, na kasa katabus a harkokin mulki na ya fara taba min martaba da kima, da yawan mutane suna tunanin na gaza yin riko da adalci, suna min ganin na gaza samar da ci gaban musulunci, ina damuwa matuka da wanzuwar lamarin da suke zuwa kunnuwana ina takaici da abu guda, makusanta na basa iya fayyace min duk abin da yake yawo a birnin bare koma sauran kasashen da muke mulka, har sakacina ya kai ga mutuwar ga ‘ya'yan Sarki dan uwana suna kokarin kashe junansu a kan mulkin masarautar da muka danka musu batare da sun zo don a yi musu sulhu ba, mene ne amfanin waziri Ja'afar da ya zamo wakilina akan komai, mene ne amfani shugaban dakarun na birni da kauyekan wannan birni har ace kafurai za su kafa wata rashin gaskiya su aiwatar a cikin kasuwar da afarma mukayi musu suke zuwa su yi saye hajojinmu, mun yi cece kuce da Hakiman Kauye akan basa bukatar shigowar kafurai amma mun danne su da karfin mulki saboda muna musu fatan samun tagomashi daga ababen da suke sana'antarwa, kuma ga ni a raye ban mutu ba, mene ne yake damuna ne? ba cuta nake yi kamar ajali ba, mene ne yake sakani na zama kamar sakarai". "Ranka ya dade". Ta tare shi da murya mai cike da shagwaba, yanga jan hankali da kuma kwantar da hankalin ma'abocin saurare, ya tsayar da kansa ^ a kanta a nutse yana son ta ce wani abu. "Ranka ya dade" ta kara maimaita cikin sigar muryar jan hankali “Ka yanke wani hukunci wadda ya yi min dadin ji a zaman fada na ranakun da suka gabata, cewar ‘ya'yanka duka za su fara shiga sabgogin mulkinka kai tsaye bature 85 Page na tabbata jininka ba zai yaudare ka ko gaza wa da abin da ka umarce sub a, batu akan Waziri shi ne karfinsa bai zamo kamar na Sarki ba, amma karfin da ke hannu yaranka tamkar naka karfin don haka ka yanke hukunci mai kyau, sannan kuma na san tun daga yau in sun iso za mu samu kyakkyawan labari”. Ya dan yadda da maganar ta, amma dai ya kalli kansa "Me na rasa ni da ba zan yi da kaina ba mene ne damuwa ta, lallai zan canza mai duba lafiyata". Gabanta ya yanke ya fadi domin hakan na daf da tonowar asirinta ta ce "Kana zargin wani abu ne?" "Bana zargin Mustafha da komai face tsufa da kuma kamar bai da kwarewa a game da abin da ke damuna tunda ba cuta nakeyi ta rashin lafiya ba, cut ace ta rashin sukuni, karfin gwiwaa, karsashi shiga kow
🏠