NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 42

domin su ne manoma, su ne masu kiwo su ke kiwata mana mana dawakai mu hau, su kiwata mana shanu, raguna, mu ci, saboda haka ku sani yaki yaune muka fara da, ba kuma za mu daina ba, har duniya ta tashi, domin mun yi imani baza su taba karewa ba, an faro bature 6 Page yakoki sama da shekaru miliyoyi haka za a ci gaba da yi a nan da miliyoyin shekaru amma a wannan nawa ne yaki na ne, sai na kafa tarihi mafi kuncin a dukkanin zuciyar wani musulmi duniya a duk inda yake kowane yanki na duniya sai mun karar da su, domin sai na rushe shirinsu, kamar yadda giwa zata take ginin toka. Kai zababben Sarki wadda na wakilta JAREMI zuwa jagorancin Birnin Hairam, maza ka koma birninka tare da rundunarka rundunar da zan taso ta izuwa masarautarka ta ishe ka tsari daga Azabar Sarki Muhammad farsi Kai Philips ka Koma masarautarka cikin izza babu shakka ko tsoro domin kana tare da kariyar Babban Sarkin duniya, kai ne kake jagorantar yanki mafi hatsari yin wasarere da wannan yankin ba karamar asara bace domin tanan muke mika guba zuwa ga babban birnin Musulunci. Na dawo gare ku Geogi da Gillasi, yakin da kuke yi da kauyen dake cikin birnin Ka da ku fasa na san sako zai iske ni daga Sarki Muhammad farsi, a wannan lokacin da Sakon zai yi iso wajena, a nan ne zan a jiye babban martani wanda yakin zai tashi daga kawunanku zuwa gare ni, kowannen ku na sallame shi. Sarakai huɗu waɗanda aka assasasu a jikin kasar Bahara domin wanzar da rikici da rashin son zaman lafiya suka mike tsaye domin komawa masarautansu. JARUMIN UMAR Lokacin da Jarumi Umar ya ga wannan rundunar dakarun na kafurai sun nufi babban birni tare da wasu zaratan karata majiya karfi, adadinsu zai kai kimanin mutum ashirin da bakwai sai wani Kije wadda da alamu shi ne wani abu ke ciki ake bashi tsaro mutane da ke kewaye da Kejin ya sa baya iya tantance mene ne a ciki. A hankali yake bin bayansu domin tuni yayi aike ga abokin tafiyarsa bature 7| Page zuwa gida don sanarwa da mahaifinsa halin da ake ciki, sai da tafiya ta yi nisa. A dai dai lokacin da ya fara tunanin matukar an shiga birnin Bahara an kai ga kasuwar Nur inda ba a banbance tsakanin kafuri da musulmi komai zai iya kwace masa sai hankalinsaya tashi yake ji ma kamar ya afka musu shi kaɗai domin ya ga shirin da suka zo da shi, yana cikin wannan damuwar ne sai ya ga rundunar ta tsaya. Shugaban tawagar ya bada Umarni a tsaya, duk da cewar tafiyar bai ce ace an yada zango ba domin baza ta wuce ta sa'a ɗaya ba. Don haka a ransa yake tunanin mene ne dalili tsayawar ta su. Wani mahayi da sauri ya zaburi dokin su ya baro cikinsu ya dawo hanyar bayan ganin haka ya sa Jarumi Umar dakatawa ya kuma boye sosai a maboyarsa domin ka da wannan mahayi da taho ya gan shi, mahayin ya zo daidai in da Jarumi Umar ke tsaye ya ja dokinsa ya tsaya yana dube dube hakan ya tabbatarwa Jarumi Umar cewa lallai akwai dalili, don hakaya kara boye kansa jim kadan mahayin ya kara zaburar dokinsa ya sukwane shi zuwa inda ya baro su. Tafiya ce ta ba ta wuce rabin sa'a a ce an kai ga babban birni ba, don haka babban cikinsu sai ya nufi wannan babban keken dokin mai dauke da Keji take majiya karfin da suke tsare a bakin kofar suka bude kofar Kejin. Wasu kyawawan mata ne suka bayyana su biyu masu sanye da fararen kaya da shiga ta mutumci "Ina da bukata". "Kina da bukatar me?" "Ina da bukatar yin fitsari". Sai babban cikinsu ya dubi na kusa da shi ya kece da dariya ya ce "Akan wannan bukatar kika sa muka tsaya, bakya kallon a hanya muke ki yi kayanki a cikin Kejin mana kamar yadda doki yake yi". bature 8|Page Dayar da take gefe daya ta ce "Ai mu ba dabbobi bane irin ku, in za mu yi bukata waje muke samu killatacce a mutunce mu yi A nan take ya ɗaga bulalar hannunsa ya jinjina zai shauɗa mata sai Babban na su ya rike hannunsa ya ce "Ba mu da wannan ikon domin an Umarce mu da mu kai su cikin koshin lafiya ba tare da cin zarafi ba, yanzu abin da za a yi shi ne rufe kofa mu ci gaba da tafiya,in ta ga dama ta yi in bata ga dam aba ta zauna da shi saura kalilan lokaci mu karasa Bahara mu danka su ga tawagar Waziri Ja'afar domin tura su wata masarauta". Daga nesa da Jarumi Umar yake bai iya hango abin da ke faruwa amma jikinsa ya shi fursunoni a cikin kejin kuma daga dukkanin alamu wani babban al'amari ne shi yasa aka sashi a keji wadda yake a rufe to ma mai zai kai su birnin Bahara da fursunoni haka? Ya tambayi kansa amsar da bai da masaniyarta ke nan Dai dai lokacin Wannan budurwa ta cikin Keji ta saka kafa ta tare kafin Barden ya ida rufi kofar ta ce “Ni ce matsalar ku, wannan da take da bukata baku da damuwar kubcewa daga hannunku, domin ba ita ce kuke nema ba ni ce, don haka ina mai umartarku da ku ba ta dama ta je ta yi uzurinta ta dawo sannan mu ci gaba da tafiya”. Da shugaban da mai rufe kofar suka kalli juna a lokaci guda ko me shugaban ya tuna sai kumaya gyaɗa kai alamar a bar ta, sannan a saka mutum biyu su yi mata rakiya, Dukka matan biyu suka
🏠