Benjamin sai Yarima Yazid
ya jinjina kai daga nan kuma sai ya girgiza kai yace "Kayi babban
kuskure, ko kana da laifi ko baka da shi, wa'adin mutuwa ya zo
gareka, ka jira martani”.
Daga fadin haka ya fice daga cikin birnin koda Yazid ya fita
sai babban mai kula da cocin birnin dakuma manyan dakaru suka zo
gaban Benjamin Babban shugaban coci ya ce "Kayi ganganci ya
shugaba, shin baka tunanin matsalar da zata biyo baya".
bature
80 Page
"Ban so abubuwan nan suka faru ba, domin ba abu ne mai kyau ba, ya ci a ce mun bi shirinmu a hankali, tabbas dole mu kara tsaro da kuma garkame birninmu sannan dole a samu a aikawa da
masarauta rum sako".
Benjamin ya ce "Masarauta ta gaji da zamowarmu bayin musulunci, ita da kanta ta so mu aikata fitinar da za mu warware
yarjejeniya saboda mun tanadi mayaka marasa iyaka za mu iya yaki
da su a yanzu".
Dukkaninsu suka yi shiru suna nazarin maganganun da yake
fada,amma a zuciyarsu suna cike da tsoro domin Sarki Muhammad
farsi ba kanwar lasa bane, ba a taba gane shirinsa sai a ranar da ya
tunkare ka domin yaki
Basu bar wajen ba sai da aka tura sako zuwa rum sannan aka
tura sakonne zuwa birane uku da suke makota da su wadanda za su
basu taimakon gaggawa kafin isar sakon zuwa rum. **
Al'amarin Jarumi Jarumi Umar lokacin da suka nufo hanyar
gida kai tsaye batare da jira ko bata lokaci ba, sai gasu a kauyen
Annur cikin annuri akan fuskokinsu, a na cikin zaman yamma na
Majalisi sai gasu sun shigo cikin kauyen. Kowa dake cikin kauyen
sai ya kasance cikin farin ciki ganin jarumi Jarumi Umar da
abokansa sun dawo cikin koshin lafiya batare da an daukowani akan
gadon marasa lafiya ba.
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya mike tsaye ya fara furta
Shukran ya rabbi, Alhamdullahi, godiya ta tabbata da mai bawa rana
Jarumi Umarni ta fitowa da kuma koma, ubangiji mutane da Aljanu
mai iko akan kowa da komai, masha Allahu ya rabbi.
Lokacin da Jarumi Umar ya karaso ya sauka daga kan
dokinsa kai tsaye ya nufi mahaifinsa, ya gaida dattijan fada sannan
ya matsa ga mahaifinsa, duk abin da ya faru ya sanar da shi, tun daga
bature
81 Page
kan tafiyasu zuwa Birnin SHamnun har zuwa lokacin da aka yi
kokarin rataye shi, har zuwa da Yarima Abbas ya zo ya kubutar da
shi har ma da yadda Abbas din ya gudanar da bincike har ya zartar da
hukuncin da yake da ikon yin.
Dukkanin jama'ar fadar sun jinjinawa Yarima Abbas kuma
sun yi murna da ya zamo aikinsa na farko na matsayin Yarima nuna
halin girma da kuma nuna cewarshi jagaba ne mai adalci.
Gimbiya Suhaila bin Ababakari na nesa tana hango Jarumi
Jarumi Umar jira take yi kawai ya baro fada ya zo wuce wa zai shiga
gidata tare shi ta yi masa Magana don jin abin da ke faruwa, aikuwa
cikin ikon Allah bisa mamakinta sai ta ga ya yi sallamada manyan
fadar Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya nufo hanyar da zata sada shi
ga cikin gida. Dukkanin abokansa sun tafi na su sashin da sauri ta
nufe shi. Kwatsam ya ganta a gabansa tare da zakuwa a cikin ranta
Ya sakar mata murmushi mai taushi, hade da jin kwarin
gwiwa samar mata da farin ciki na bata daddan labari.
"Dan uwanki yayi nasara zama sarki”.
Nan take ta durkusa kasa ta yi sujjadar shukra ta dago tana
yiwa Allah kirari da sunayensa tsarkaka kallonta kawai ya tsaya yake
yii yana wannan murmushi wadda shi kansa bai san yana yinsu.
Sai da ta kamala sannan ta dago ta ce "Da me zan saka maka
ya kai Jarumi Umar".
Ji ya yi kamar yace wani abu amma sai ya dauke idanuwansa
da barin kallonta domin ya fara yi mata wani kallo wadda shi da
kansa ya fahimci ya wuce gona da iri ba wacce suka yi sabon da zai
mata wannan kallon bace domin a tsakaninsu kawai taimako ne”.
"Da ni da ke duk mu godewa Allah mu kuma godewa
masarautar Bahara, da yarima Abbas, ban da zuwan da yayi a kan
lokaci da tuni na rasa rayuwata".
bature
Ta kara fadada murmushinta "Kai ne kataimake ni daga
fadawa tarkon kafure, ka kubutar da ni daga hannunsu, ka tseratar da
rikicin da zai hadu tsakanin kasashen musulunci.
Kai ne ka sayar da rank aka tafi kasar da ake neman mai
goyan bayanmu, domin su hallaka shi, kai ne ka cancanci yabo da
godiya a gare ni, ina mai kara gode maka, kuma watarana zan rama
maka wannan halacci"
Bai san Gimbiya Suhaila bin Ababakari na da matukar kyau
irin na yau ba, sai da ta kasance cikin nishadi tana dariya, koda yake
murmushi shi ke tona asirin kyawun dan adam, saboda haka ya zama
wani saakarai wajen kallon kyawun fuskarta, har sai da ta tsayar da
kallonta a kanshi ta fuskanci yadda yake kallonta, ya dimauce ya
kasa samun yadda zai sarrafa kansa har sai da ta dan jima itama tana
kallonsa a ranta ta ce Jarumi Jarumi Umar shi ne namijin da take buri
ta samu a matsayin mijia gareta yana da zati irin na mazajen gaske
dirin jikinsa ya amsa, yanayin jarumtarsa abin burgewa, shine mijin
da zai iya kare iyalinsa daga dukkan karfinsa, yana da kirki da kunya
kamar yadda take da buri, shi kansa ya manta da yanayin da yake
ciki, kwakwalwarsa mai saurin kawomasa shawarwari t