NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 28 of 42

ladabi ka kuma lura da kanka da ke kan gangar jikinka, koda na bar makamina a waje zan iya amfani da naka cikin 'yan dakikai na sare wuyanka a take a yanzu". bature 77 Page Wasu dakaru da suke tsaye a fusace suka motsa suna shirin su afkawa Zayed, sai Shugaban Benjamin yayi dariya ya ce "Karfin gwiwarku da kurinku yake tsoratar da matsora ta, na fi ka tsanar rubutaccen alkawarin zaman lafiya domin bana bukatar zaman lafiya na fito a kodayaushe na ganni inashawagin cikin musulmi ina cire kansa kamar ina sassabe a gona, ka yi sa'a saboda wannan yarjejeniyar zaman lafiyar da baka isa ka fita daga cikin fadar nan a raye.... Kamar an jefa kibiya daga cikin gwafarta Yazid yayi tsalle kan Benjamin,dukkaninsu cikin shirin farmakarjuna suke sai shima Benjamin yayi kururuwa ya taho suka gwabzo, kowa ya ji jikin dan uwansa,dakarun Benjamin da bawan Yazid kowa yayi yunkurin tasowa. Benjamin ya daga musu hannu "Kada wadda ya motsa, wannan bai sabaka'ida ko yarjejeniya ba, yaro ne yake so ya gwada gwanjinsa don haka ku bar shi”. Ran Yazid ya kara fusata hankalinsa ya dugunzuma ainun ya kara farmakar Benjamin akaro na biyu suka kaure da yakar juna kamar wasu zakaru a fagen fafatawa. Yazid na da jarumta ta ban mamaki ko da yake dama babu wani matashi a kasar Bahara da ya kasance rago musamman jinin sarauta babu takobi a hannunsa, cikin kwarewa ya zare daya daga jikin wani matashin badakare da ya ZO kusa dank are shugabansa,amma shi kansa bai san lokacin da takobinsa ba, saboda tsananin zafin nama. Yazid ya zare Suka kaure da yake suna kaiwa juna sara da suka kowa yana karewa iya karfinsa, idan Benjamin ya matsa kai sara da suka har ya kusa kure Yazid sai Yazid shima ya kufula ya harzuka ya taso da nashi sara da suka har sai ya kai Benjamin mukura aka dauki kusan rabin sa'a batare da wani ya samu lagon dan uwansa ba. bature 78 Page Kafin kace mene ne sun zamar da fada tamkar wacca aka kwana ana yaki, kuma duk da haka ba a samu wani ya samu nasarar sarar dan uwansa ba, duk irin mugun nufin da suke kai wa junansu. Tsamari yayi tsamari har ya kai har da yawa daga cikin manyan dakarun Benjamin sun iso fadar Sarki amma Benjamin ya dakatar dasu da niyar daukarmataki, a na cikin wannan fafatawar ne Benjamin ya kuntata Yazid da sara da inda ya kai masa wani sara a lokacin Yazid ya kwanta a kasa, sun hada kaifin takubbansu inda Yazid yana kasa yana kokarin yayi amfani da damtsensa wajen wancakalar da Benjami amma Benjamin ya daddage domin so yake ya fi karfin Yazid ya ya kais hi karshe ana cikin hakada Benjamin yaga ya gagara kaiwa ga gaci gashi kuma karfinsa na neman karewa sai yayi dabara ya zare wata wuka daga kubensaya yanke hannun daman Yazid. Yazid yayi kara gami da sagewa har Benjamin ya kusa kai takubban kan wuya Yazid, sai Yazid yayi wata kabbara wani sabon karfi ya zo masa duk da yankan da yake hannunsa ya fara fitar da jini amma hakaya wuncakalar da Benjamin ya mike tsaye ya dubi wajen yankan,amma cikin jarumta ya kara gyara takobinsa ya farwa Benjamin dake kasa, amma kafin ya kai kansa ya mike tsaye ya zame banda zamewar da yayi da sara ne mummunan zai tsagashi gida biyu. Benjamin ya rufo bayan Yazid da niyar ya farmake shi ta baya, sai Yazid ya wani juye Benjamin ya wuce kamar iska, a wannan yanayin Yazid yayi amfani da kwarewarsa ya saka takobinsa ta yanke kuben cikin Benjamin, Benjamin ya rike wajen ya duba hannunsa yaga jini face face, yayi murmushi shi ma Yazid yayi murmushi ya ce "Ka ci darajar ^ yarjejeniya da wannan yanka farke cikinka zanyi hatta da hanji su fito su bata fadarka, to amma ba wannan ne ya kawo ni, na zo gare ka domin na ji dalilin dayasa kuka farmaki Yar Sarki Ababakari”. bature 79 Page Shugaba Bejamin ya jinjina kwazo da bajinta irin ta Yazid sannan ya ce "Ka koma ka sanarwa da Sarki mun kama ta ne saboda muna son mu kaita ga Sarki Mu'azzam domin soyayyarta da yake yi tun shekarun baya da suka wuce, don haka mu a kan kin kanmu ba mu da wata alaka da ita face hada soyayya tsakaninsu da Sarki Mu'azzam da ke mulki birnin Sarraf, yarana sun dauketa su kaita Bahara sannan su dankata da hadiman Sarki Mu'azzamda so kai masa ita ya aureta". Koda Yarima Yazid ya ji wannan batu sai ya cika da mamaki domin Sarki Mu'azzam dan uwan ne ga mahaifina, wadda yake dan ne shi ga Yayanshi, sannan kuma Sarki Mu'azzam bashi da son rai yana bin mahaifinsu batare da wata boyayyen munafunci a zuciyarsa ba, Sarki Mu'azzam ya bada rayuwarsa ga Sarki Muhammad farsi don haka ya ce "Wannan yana daga cikin aikin shaidanci da fajirci irin naku, saboda haka karya kake, idan Mua'zam zai nemi auren 'yar Sarki Ababakari, kai tsaye bazai fito ta wannan sigar har ya hada kai da ku". Benjamin ya ce "Ji ya zama dole ka bukata na sanar da kai, wannan matsalolinku ne, kamar yadda aka so ka zo ka ji na sanar da kai, idan Sarki Muhammad farsi yana bukatar shaidawa muna ita, domin ba ma yin kwanmu sai da zakara”. Koda jin wannan batu daga bakin
🏠