bayansa. Ana Masa lakabi da BAGULBASI. Su ne arnan daji na cikin daular musulunci wadanda
aka ci su da yaki suka koma rayuwar kauye tun shekaru masu aka
fatattake su da shirkokinsu da Allolinsu aka kusan karar da su,
wadanda suka kubuta ne suka koma jeji, suka dauki gina sabuwar
rayuwa tun a baya da shekaru masu yawan gaske, su kan fita su sato
jarire su maishe da su nasu, su dora su akan yaki, baya da shekara
dari biyu suka fara bayyana a duniya aka fahimci suna nan basu kare
ba, su kan zo kauye su farmake su su kwashe dukkanin yara su kashe
tsoffai su kwashe mata. A wannan lokacin su ka addabi duniya ba
musulmi babu kafirai ko ina yaka suke yi, sai aka samu hadin kai na
kafurai da musulunci a lokacin Sarki Ahmad aka yi mummunan
yakin da ta sa kowa yayi asarar rayuka.
Da aka fahimci yaki da sub a zai ba su ma suka tabbatar da
aka ci gaba da yakin za a kara mai da su baya sai Kiristoci su ka
nema shawarar sarki Ahmad akan cewa sulhu shi ne mafita, to a
wannan lokacin aka zauna sulhu aka yi da su, zasu dinga amsar
haraji daga bakin da suke zuwa daga bangaren bakaken fata wadanda su ne a bangarensu, sannan babban birnin zai basu wajen rayuwa a
zauna a tare. Sai suka ki yadda cewar su ba sa zama a cikin gini basa
su rayu a cikin birni da aka kayata shi baza su koma jeji su ci gaba da
rayuwarsu, sannan kuma sun amince da za a dinga amsar haraji kaso daya cikin kaso hudu, za su yi kasuwanci na noma suna shigowa da
shi, amma sub a za a shigo musu da komai.
1
bature
75 | Page
Aka yadda da sharadinsu, aka zauna lafiya da su amma a
cikin kasan zuciyarsu suna nan suna hayayyafa suna kai farmaki
wajejen sin suna kamo jarirai suna manyan fashe a bangaren teku, da
haka suka kara hada babbar fada suka tumbatsa suka bada horo mafi
tsananin ga dakarunsu domin suna son yin shirin na gaske da sai sun
fitar da musulmi daga cikin birnin tunda birninsu ne tun asali.
Su kan jima basu kawo matsaloli a birnin ba, sai jefa jefa
kuma da an je an zauna da shugabansu zasu nuna bada goyan
bayansu ba, a nemi wasu daga cikin dakaru a yi musu hukunci
acewar su ne suka aikata da haka suka mamaye jejin tsoro da fargaba
kowa a duniya ta fita daga zuciyarsu.
A yau shugabansu Sarki Alifkato ya fara turo runduna guda
domin fara mamaya shi ne wannan fitowa domin fara nunawa birnin
cewar sun shirya domin yin fito na fito da su. Don haka suke tafe
cikin izza da takama, kai tsaye wasu irin makamai ne a hannun
kowacce ruduna da take tafe, wasu za ga duk yawansu Gatari ne mai
sheke da walwali a hannunsa, wasu kuma za ka gansu da mashi,
fikakku masu tsayen gaske,wasu rukuni duk kwari da bakoki ne a
hannayensu cikin shiri,wasu takobba, wasu kuma al'amudi ne,suna
tafe suna yiwa abin bautarsu kirari don neman yaddarsa a fitowarsu. **
Lokacin da Yarima Zaid isa bakin kofar shiga birnin Haiman
karkashin jagorancin Benjamin sai yayi Jarumi Umarni da a tsaya da
dawakai domin neman iso. A ka bude karamar kofar birnin Sarkin
kofar ya fito a bisa dawakai mutum biyu na biye da shi. Fararen
dawakai ne sun ado na kawa da gani kasan akwai kyalli da
kyalekyale a cikin birnin tun daga tufafin dakarun birnin da yadda
aka yi wadaka da dukiya wajen ginin katangar birnin. Lokacin da
dakarun suka iso sai shugaban dakarun kofar ya iso gaban Yarima
Hilal ya ce "Lalle marhaba da zuwan dan Sarki Muhammad farsi,
bature
76 Page
tun saura rabin sa'a muka san da zuwanka domin masu kula da
dajijjikanmu sun kawo mana labari, Shugaba Benjamin na maka
maraba, amma ya sanar da ni cewa ka shigo cikin birnin daga kai sai
mai yi maka hidima wato bawanka domin tsari da birnin mu yake da
shin a son zaman lafiya shiga da dakaru irin wadannan zai sa firgici
da tsoro a zuciyar mutane mazauna birnina"
Koda Yarima Zaid wannan batu daga bakin bakin shugaban
dakaru sai yayyi murmushi ya ce "Dukkanin nahiyar nan mallakin
birnin mu ce, dukkanin iko da Jarumi Umarni yana karkashin
masarautar mu, saboda haka sa'a daya kaci har da zan bi wannan
Jarumi Umarni, dama ban zo da niyar na shiga birninku da dakaru
ba, na zone domin na shiga ni daya, saboda haka mu je zuwa”.
Shugaban dakarun yayi murmushi shi ma sannan ya juya
dokinsa Yarima da Hadiminsa Arif suka bi bayansa.
A haka suka isa har babbar fadar Benjamin, a lokacin
Benjamin na zaune akan karagar mulkinsa Yarima Hilal ya shigo
cikin fadar cikin Gadara da isa irin ta masu mulki. Benjamin bai tashi
daga kan karagar mulkinsa ba har sai da Yarima ya zo daf da shi,
sannan ya saki fuskarsa gami da murmushi na rainin wayo ya ce
"Sarkin Muhammad farsi ya aiko ka ne domin jin ta bakina game da
neman 'yar Sarki Ababakari, idan na canka zan baka gamsasshiyar
amsa".
Yarima ya kufulo da halin Gadara da Benjamin yake yi masa
ya ce "Kai kafiri maʼabocin bautar wanin da ba Allah ba, ka yi sani
cewa alfarmar zaman lafiyar da yake rubuce akan tafarkin takarda
yake zaune da kai a wannan kujerar har kake iya yin wani motsi,
baya ga haka da ire irenku basa numfashi, ka yi biyayya cikin