NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 26 of 42

z aka iya zama Sarkin birni guda ba, tunda har za ka iya kauda kai a yi duk abin da aka ga dama,saboda haka baka cancanta da zama Sarki ba kai da duk wadda yake da hannu a cikin birnin nan za a rufe ku sannan za a rantsar da Yarima Salman a matsayin sarki a gobe hukunci yana hannunsa" Koda ya zo nan a batunsa sai ya fice daga cikin fadar dakarunsa suka bi masa baya. Dakarun da suke bawa Yarima Hilal tsaro suka dawo bayan Salman. Bai tsaye ko a’ina sai kofar fada a lokacin da Jarumi Jarumi Umar ya samu kansa sosai har an bashi abinci da ruwa ya ci ya koshi, da sauran abokansa, Yarima Abbas ya kasance tare da su, ta hirar jarumtaka da yadda za a kawo gyara da sauyin tsarin birnin gaba daya. Jarumi Umar yayi nisa cike da damuwar abin da yake taba masa zuciya yace “Ranka ya dade, Kasar mu na cikin mawuyacin halin kuma tana gab da zubewa matukar aka kasance a haka, ku ne masu iko da gyara komai na sarauta da kuma juya akalar al'umma zuwa ga bin tafarkin gaskiya. A tarihin da muka samu a shekarun baya lokacin da Kakanku na mulki, babu wani kafiri da ya isa ya shigo cikin birnin Bahara har bature 72 | Page sai an yi da shi ya kuma saka hannun cewar ba zai sabaka'idar birnin ba, ba kuma zai yi shigar banza ba, sannan ba zai yi addininsa a bainar jama'a ba, a wannan lokaci ba a samun musulmi yana shan giya, ba a samun musulmi yana canca, ba a samun musulmi yana aikata zina, musulmai na lokacin Kakanka sun kasance masu matukar tsoron hukunci, koda a ce babu tsoron Allah a ranka to la shakka kana tsoron hukunci daga masarauta, masu bin addinin kuma suna tafiya a tafarki daya babu rabe raben kawuna, idan an ga wata kowa yana yadda kamar yadda Sarki zai yi bayani, haka zai dauki azumi kamar kowa, babu malamai masu zuwa da sukar hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, babu masu zagi da cin mutumci wasu ahli da manzo ya zauna da su a matsayin 'yan uwa ana matukar tunkarar birnin Bahara da yaudara domin kowanne malami ko bayahude da ya yi baddakama ya shigo birnin ya san karshen kaifin takobi ce karshen numfashinsa, amma yanzu kauyukan irin namu na tsoron shiga cikin kasuwar birnin domin tsoron kada yara su dauko munana akidu daga kafirai yahudu, ranka ya dade yaushe ne wannan makircin da yahudu ya shiryawa birninmu zai kau daga doron kasa. Maganganun sun shiga zuciyar Yarima Abbas kuma ya ji su har cikin ransa, tabbas Jarumi Umar bashi da tsoro ko fargaba kamar mahaifinsa, domin dukkan mutanen birnin suna tsoron zuwa yiwa Sarki wannan tambaya amma sun kasa, sai Abdullahi bin Sharjas ne kadai yake iya gaba da gaba da Sarki ya gaya masa gaskiya, yau gashi dansa bai ji shakkarsa ba,shi maya tare shi ya sanar da shi. "Lallai komai yana da lokaci, kuma yana da karshe, insha Allahu za mu yi maganin komai da yaddar Allah. Yanzu na san a kagauce kuke da kuka ma hanya don komawa gida. Za ku iya tafiya, Ya kai Jarumi Umar ina son sanar da kai cewar a duk lokacin da na bukaceka da kai da abokan tafiyarka lallai na ji dadin kasancewa tare bature 2 73 | Page da ku,domin a rayuwata na tsani munafunci, kuma ina son mutum gaya min gaskiya duk dacinta, saboda hakaina bukatarku a tare da ni, kuma ina nan zan kawo maku ziyara bayan na kamala da ayyukan da mahaifina ya sakani". Suka jinjina kai alamar gamsuwa da maganarsa. Jarumi Umar ya ce "Na ji dadin yadda ka gyara lamuran birnin SHamnun a kankanin lokaci, ina fatan ka taimakawa Sarki Muhammad farsi a dukkan tafiyar da lamuran kasarsa Allah ya taimake ka" Yana fadin haka suka mike tsaye Yarima ya dube su "Insha Allahu za mu yaki kafirai kafada da kafada tare da ku, za mu fatattake su daga birninmu insha Allahu, Allah ubangiji ya tsare hanya". Suka amsa da amin su dukansu sannan suka nufi hanyar fita yana tsaye yana kallonsu, yana ji a ransa akwai nasara a rayuwarsa ta zama Sarki a haduwa da ahlin Abdullahi bin Sharjas, domin ya fuskanci ta inda zai gyara tafiyar birninsa ta hanyar shawarwari ga mahaifinsa sannan kuma ya samu tsakwakuren da zai yi tare da su har suka fice yana murmushi. ** Wata irin bakar runduna ce mai tsananin yawa ta taso daga yammacin birnin Bahara, wasu gungun bataliyar dakaru ne iya ganinka rukuni rukuni sun kai rukuni goma, duk rukuni daya z aka tadda su birjik kamar gudaje, sanye suke da bakaken kaya da aka sana'antashi da batar bakar damisa, idanuwansu jajaye da hula na akansu wadanda suke da kahon saniya guda daya daya a tsakiyar goshinsu. Dawakansu ma bakake ne wuluk babban cikinsu na tafe, yayi wasu zaneka da baki a kan fuskarsa wadda alamun hakan yaki ne labbansa bakinkirin, yana muzurai yana zare ido. bature 74 Page Babban Dakare na kare dange daga cikin Dakarun Hangalawa ne ke tafe a gaba da kamar taku shida sannan dakarun nasa na biye da shi a baya kato ne na gaske, haka dokinsa jibgege ba karamin namijin gaske bane zai yi idi biyu da wannan katon bai koma da bay aba, yan da suma kamar mahaukaci a kansa sannan akwai wata jelargashi guda daya ta ka har gadon
🏠