a
yasa na samu kurewar lokaci ban shigo birnin nan ba a daren jiya,
sannan na samu aiko da sako zuwa ga wasu yan majalisar Sarki don
su shaidamin dalilin da yasa yarima Salman ya gudu, na samu
dukkanin labari, abin da ya faru, sannan dukkanin alʼamarin da ya
faru na samu hujja mai karfi wacce zan iya yanke hukunci kai tsaye,
amma bisa adalci ba zan yanke hukunci kai tsaye akan ku ba, saboda
laifinku na tilastawa ne ba kamar Waziri ba da na samu dumu-dumu
da laifi barkatai, "Ka shigo min yarima Salman".
Ya dubi daya daga cikin dakaren da yake tsaron lafiyarsa. Kai
tsaye dakaren ya tafi zuwa bakin kofar fadar yana zuwa yayi Jarumi
Umarni da hannu aka shigo Yarima Salman cikin fadar. A nutse yake
bature
68 Page
69 Page
tafiya cikin izza ta mulki babu tashin hankali ko firgici a tare da shi,
ya zo gaban Yarima Abbas ya tsaya cikin girmamawa, Yarima
Abbas ya dube shi cikin kulawa sannan yace "Me yasa ka bar birnin
Shamnun
"Na bar birnin Shamnun wane dare da na kwana da zargin
cewar akwai makarkashiyar daga fada, na gano cewar an shirya
hallaka ni ne, saboda yadda na isa sansanin dakaru, na duba yadda su
ka amshi ne a matsayina na wadda mahaifina ya bar suna na a
matsayin magajinsa, har sai idan akwai wani abin cutarwa da na taba
aikatawa bayan ba ransa kafin nadin sarauta, na shirya zama da yan
Majalisar dattawa na gidan Sarauta, ban samu hadin kan kowa daga
cikinsu ba, sai wasika a cikin dare da wani daga cikin majalisar
dattijai ya turo min da ita"
Koda ya zo nan a zancensa sai ya dauko wannan takardar da
aka rubuta wasika ya fara karantawa don kowa ya ji
Ka bar birnin Shamnun a daren yau, ka da ka bari ka kwana,
babu yadda za mu iya ta dole da sa hannun kowane dattijon majalisa
saka hannu a kashe ka bisa zargin da za a dora maka na cin amanar
kasar wadda za a turawa Sarki Muhammad farsi a matsayin laifi.
Bai bayyana ko wane ne shi ba saboda tsoro na so nayi tirjiya
na dake na ki guduwa amma kuma sai na tuna matukar bakuna sun
hadu to bani da wani karfi da zan iya tunkarar su, sai nayi amfani da
wannan shawara ta wannan mai turo min da sakon takarda na bar
birnin, haka kuma ya kara tura min sakon na janye yar uwata daga
birnin Shamnun saboda ana kokari ayi amfani da ita don gano inda
kake, wannan dalili yasa na bar birnin nan nab ace cikin wani
rukunin kauye a cikin birnin Shamnun yadda babu wadda ya isa ya
gano inda nake, sai a lokacin da nag a tawagar Yarima Abbas na
daren jiya na bayyana a gare shi domin zayyane masa dukkan abin da
ke faruwa.
bature
70 Page
Koda Yarima Salman ya gama jawabinsa, sai yarima Abbas
ya juya kan yarima Abu Kausar yace "Kana da damar da za ka fadi
albarkacin bakinka".
Shugaban zauren majalisar dattaje abu Kausar ya mike tsaye
gami da cewa "Mun yi babban kuskure a bisa al'ada na dan adamda
tsoro yake bin jinin jikinsa da son duniya, na yabawa dattijai na
karkashina da a karon farko sun turje, duk da cewar an dauki silalla
masu daraja an basu, an kuma yi musu alkawarun masu nauyi duk da
hakasun turje sai akafarayi musu barazanar kisa, sannan aka hana
tura mu sako ko kuma fita daga birnin ta kowacce hanya, ni ne nayi
amfani da wani bawa na da babu wadda ya san shi nake aikawa
Yarima Salman sako, sako na farko da na biyu, mun gaza a
matsayinmu na masu karfi a masarauta, mun saka tsoro a
rayuwakanmu, na so mun jajurce koda za a jininmu zai zuba a doron
kasa amma dayake mun yadda Allah daya ne kuma zai kawo mafita
sai muka dage da addu'a Allah ya wargaza wannan al'amari, a
kullum mukan hadu mu sauke alkur'ani mai girma, babu taba
gajiyawa ba, cikin sauki Allah ya kawo mana mafita, ya kai Yarima
mai daraja, muna sanar da kai babu wani ko wani da ya ci koda daya
daga cikin sulallan da suka ba mu, sannan muna farin ciki a yi
gaggawar yi mana hukunci mafi dacewa saboda mu masu laifi ne".
Koda ya zo nan a zancensa sai Yarima Abbas ya jinjina kai
gami da duba lamarinsu da kuma kokarinsu na kai kuka ga ubangiji,
sai ya ce "Na bar lamarinku ga mahaifina, domin bazan iya yanke
wannanhukuncin ba, a kai tsaye zan iya yi muku adalci, amma ban
sani ba ko masarauta za ta iya yafe wannan laifin amma a bangarena
na jinjina muku”.
Sai a wannan lokacin Yarima ya koma ga Yarima Hilal ya ce
"Me z ace dangane da al'amarin da ya afku, shin akwai sharri ko
kage a ciki?"
bature
71 Page
Yarima Hilal yayi shiru kansa a kasa daga bisani ya dago kai
ya dubi Yarima Abbas yace "Ba ni da wani kudiri da na kunsa a
raina illa na gaji mahaifina, dalilina kuwa shi ne tsoron makoma ta
da kullum ake tsorata ni da shi shi ne idan Yarima salman ya zama
Sarki zai kashe mahaifiyata, sannan zai kashe ni da yan uwana,
saboda tsoron za mu zama barazana a gare shi, na yadda na amince
cewar zan zama Sarki amma ba hannu na a cikin duk wadannan
al'amarin da aka aikata na bada sulalla, na yunkurin kashe yarima
Salman, da ma tara dattijai domin tilasta su, abin da na yadda da shi
zan zama Sarki wannan kuma shi ne fatana".
"Tun anan ta tabbata ba