shiga bangaren
sarautar gidan. Bai tsaye ko ina ba sai karagar mulkin gasar
Shamnun.
Babbar fada da ce da aka kawatata da gini na alfarma waje ne
mai girman gaske, da yake mallaki ne na Rum, a shekaru masu yawa
kafin yaki sarkin wancan zamani a dawo da ita karkashin ikon
musulmi sun yi matuka batar da dukiya da basira wajen gina wannan
fadar can nesa kujerar mulki take, sannan daga hagu da dama akwai
kujerun alfarma na waziri dakuma Babban Dakaren birnin sannan ga
bature
66 Page
'yan majalisar sarki su ma kujerunsu da aka kerata da zallan zinare a
shimfide sahu sahu a gaban kujerar Sarki.
Kai tsaye Yarima ya je bakin kujerar mulki ya zagaye ta
wajen sau uku kafin ya samu wajen zama. Ya zauna sosai yana
kallon kofar shigowa wacce take kallon saitin kujera bai dauke
idanuwansa daga wajen ba har sai da Yarima Hilal da kuma Waziri
suka shigo cikin fadar.
Ganinsa a kan karagar mulki duk hankulansu ya ta shi ainun
suka tsorata matuka. Ba wani abin tsoro bane domin wani mai
babban matsayi ya zo karamar masarauta ya zauna a kujerar mulki
hakan dama yana faruwa, idan Sarki Muhammad farsi zai je kowacce
kasa da take karkashinsa shi ne zai gudanar da komai har ya bar
kasar, amma abin da yasa suka tsora a wannan lokaci suna jin cewar
Sarki Muhammad farsi ya aiko dansa Yarima Abbas ne domin ya
kwace masarauta a datseta, har sai an kamala bincike wadda hakan
idan ya faru, babu shakka sai sun rasa kujerar mulkinsu, domin za a
iya dauko wasu daga cikin jinin sarautar a basu tun da sun kasa
daidaita kansu.
Waziri Adnan ya kara so cikin sunkuyar da kai kasa shima
Yarima Hilal.
'Ranka dade ina mai maka maraba da zuwa birnin Shamnun".
Yarima ya kalle shi cikin nutsuwa. Ya mayar da kansa kan
Yarima Hilal Yarimaya dube shi a dari dari “Barka da zuwa dan
uwana Yarima Abbas".
Yarima Abba yace "Na zo takasanas daga Babban birnin
zuwa birnin Shamnur domin aiki mafi muhimmanci a gare ni, na zo
domin na fitar da gaskiya na kori karya, kuma nayi alkawari ba zan
bar birnin ban sai na tabbatar da adalci, na kuma danka mulki ga
wadda ya cancanta. Yanzu mene ne laifin Jarumi Umar da kuka yi
kokari kashe shi? Shin baku san waye shi bane?"
bature
67 Page
Waziri ya dago da kai a tsorace ya ce "Ranka ya dade ba mu
san wane ne shi ba".
"Shin bai sanar da ku ba?"
Waziri yayi shiru har sai da Yarima Abbas ya kara maimaita
tambayar, sannan ne Waziri Adnan ya ce "Ya sanar damu amma
saboda halin da muke ciki na bukatar Yarima Salman da tsoron
shirin da zai zo mana da shi ya sa muka yi tunanin karya ya shiryo
mana don ya samu ya kawo mana sharri cikin masarauta”.
Yarima Abbas ya jinjina kai “Wane bincike kukayi domin ku
tabbatar da hakikanin gaskiyarsa ko akasin haka?"
Waziri Adnan yayi shiru domin bai da tacewa "Mun yi
babban kuskure ranka ya dade a gafarce mu?"
Yarima Abbas ya mike daga kan kujerar mulki Shamnun ya
nufo inda waziri Adnan yake yana cewa “Kai ne magajin birnin
Shamnun, kai ne abokin Sarki Kawu na Ababakari shekarunka sun yi
tasirin da zaka wanzar da masalaha a tsakanin wasiyar da Sarki ya
bari, kai ne za ka yi bi duk hanyoyin da za yiwa 'yan uwa juna
adalci, amma kai ne mai kuskure aiwatarwa, da ace a lokacin yarima
Hilal ya fara mulki ne za a iya yi masa afuwa bisa ajizanci da kuma
girma irin na sarauta da rashin kwarewa zai iya kuskure, amma babu
wani abu da baka sani ba, saboda haka baka cancanta da zama Waziri
birnin Shamnun ba”.
Ya zube kasa ya fara neman kama kafafuwan Yarima Abbas
"Kayi hakuri ranka ya dade shekaru ashirin ina kan matsayina ka
tausaya min na mutu, ina zan kai darajata kima da ake kallo na da shi
a cikin birnin na".
“Ka koma ka yi bautar Allah kajira lokacin da Allah zai dauki
rayuwarka, ko ka samu ka rabauta zuwa ceton Manzon Allah amma
babu wani dalili da me kuskure irin wannan ya ci gaba da zama
waziri birnin Shamnun."
bature
Dakarun hudu suka shigo cikin fadar suka bambare shi daga
jikin yarima Abbas suka fitar da shi yana ci gaba da magiya amma
Yarima Abbas ko kallon inda yake bai kara yi ba.
Ana fita da shi sai ga dattijan birnin sun shigo wadanda suke
da alhaki akan zaban Sarki, Yarima Hilal yana dubansa gabansa, sai
da suka gama shigowa suka samu waje suka zauna sai Yarima Abbas
ya fara tafiya cikin takama da izza irin ta saraki, har sai da ya ya isa
inda suke kansu a sunkuye alamar girmama Yarima Abbas.
"Ina Adalcin ku, ina iliminku, ina tsoron Allah da shi ne ya
baku cancanta aka dauki kujerun nan aka baku, tabbas kun ci amanar
Allah kuma kunci amanar masarauta dole sai hukunci ya tabbata a
gare ku, domin ba ku zamo adalai kamar yadda ake tsammani ba."
Shugaban Dattijan majalisar Abu Kaisar yayi ajiyar zuciya
gami da "In an bani izini ina da Magana."
Yarima Abba ya dube shi ya ce "Da sauran lokaci kafin wani
ya yi Magana".
Abu Kaisar ya jinjina kai gami amsawa da girmamawa.
Yarima Abbas ya dubi yarima Hilal yace da shi "Na yi kokari gano
inda Yarima Salman yake boye a jiya da yamma shi ne dalilin d