NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 42

uro mata wuta cikin tashin hankali ta yi watsi da wani karamin ma'adanin abubuwanta komai dake kan abin ya waste ta kara rusa kuka mai tsanani ta fada kan shimfidarta. Babu wacce ta isa ta auri Jarumi Umar matukar tana raye, sai ta yi sanadiyar kashe ta, it ace zata auri Jarumi Umar duk rintse idan kuwa bata aure shi ba to kuwa sai dai su rayu a haka, babu wadda zai yi aure. A bangaren dakin da Suhaila bin Ababakari suke Uwar gida Kubra na tsaye a kanta don kwantar mata da hankali "Kiyi hakuri ki bature 62 Page kwantar da hankalinki babu wani abu haka take bata da nutsuwa akan komai kuma zan tsawatar mata". Suhaila bin Ababakari ta dubi uwargida Kubra ta kuma fahimci abin da take kokarin yi na son kwantar mata da hankali ta ce "Ba wani abu Mama, ko ubangijinmu baya kama dan adam da laifin cikin rashin sani, wannan ba komai bane, akwai damuwa sosai rasa jarumi kamar Jarumi Umar a cikin al'umma, na fahimci damuwarta sosai kuma na yafe mata". Uwar gida Kubra ta ce "Kina da zuciya mai kyau, nagode da fahimta, in kin kimtsa idan Hakimi ya fito fadar tsakar gida ki je ki gaida shi". Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta jinjina kai alamar zata je. Sannan ne uwa Kubra ta fita daga cikin dakin ta kuma nufi dakin Hamdiya tana kwance tana garzar kuka ta zauna kusa da ita. "Ban san me yake damun zuciyarki kike bijirewa koyarwar mu ba, akodayaushe muna koyar da ku muhimmancin bako a wannan masarauta amma bakya ji, duk ranar da za a yi bakuwa komai girmanta ko matsayinta sai kin nuna mata halinki na rashin kauna, ki saita zuciyarki ki iya mu'amalar kirki da mutane musamman 'yan uwanki mata ace a duk fadin garin nan da wajensa baki da wata kawa ko aminiya, ke kullum cikin rigima kike da 'yan mata, dan Allah ki gyara halayenki ki guje abin da zai sa na kara dora hannu akan fuskarki, kin san ina son ki, ina kaunar ki ko da ba ni ce na tsuggunna na haife ki ba, ina jin matsananciyar damuwar da kike ciki". Idan kina jin damuwar da nake ji da tuni kin tilasta aurena da Jarumi Umar tunda kin sani sarai babu wani mahaluki da nake so in ba shi ba Ta fada a cikin zuciyarta har Kubra ta gama yi mata nasihar ta gaji ta fita ba tace mata ta tafasa ba, jira take ta fita ta bata guri bature 631 64 | Page domin ta fara shirin da zata yi domin kawar da Gimbiya Suhaila bin Ababakari. Aka dauki Jarumi Jarumi Umar zuwa cikin dakin magani cikin sauri da gudu gudu, da fari aka fara da zuba masa ruwa domin ya dawo hayyacinsa, cikin ikon Allah numfashinsa ya dawo a hankali, suka dinga godewa Allah, a hankali ya fara budewa idanuwansa ya ganshi tare da abokansa duk fuskarsu hawaye ne ke kwaranya. Batare da sun lura da ya bude idanuwansa ba, daga can suka ji muryarsa na amsa amo da cewar "Na gaya muku zuwan mutuwa a gare ni ba sauki bace". Suka dube shi cikin farin ciki da annushuwa murmushi yake yana shafa wuyansa saboda zafin da wajen yake masa ga shati sosai wajen yayi jawur. "Su ka hada baki saboda duk wasu lokutan da ya kutsa hadari ya samu ya kubuta irin Kalmar da ya kesanar da su kenan cewar Zuwan mutuwa ba sauke ce a gare nib a, maʼana mutuwa ba za ta zo ta dauke shi cikin sauki ba, sai an sha artabu, wannan addu'arsa ce ta neman yaddar Allah akan yay i mutuwa a cikin abokan gaba yana yaki domin daga Kalmar Allah". Suka rungume shi, har sai da mai saka masa magani ya gama hada maganin sannan suka rabu da jikinsa ya saka masa maganin a wuyansa. F "Me ya faru?" Ya yi musu tambayar a lokacin da ake saka masa magani. Adai-dai wannan lokacin Yarima Abbas ya shigo cikin daki da dakaru na biye da shi. Ya kara so duk suka zuba masa idanu, har ya kara so kusa da Jarumi Umar ya zauna ya mika masa hannu domin su bature 65 Page yi musabaha Jarumi Umar ya dube shi da mamaki ya ce "Ranka ya dade" Bai dauki hannun ba ya kara jinjina kai ga Jarumi Umar domin ya aminta su gaisa. Jarumi Umar ya mika masa hannu cikin girmamawa shi ma yarima ya amsa yana mai cewa "Mahaifinka ya sanar da ni cewar nayi kokari na kubutar da kai daga sarkakiyar dake cikin kasar nan. Lallai Allah ya nufa da kwanan ka a gaba”. Jarumi Umar ya dube abokansa alamun tambaya domin bai san cewar yarima ne ya cece shi ba, suka daga masa kai alamar tabbatarwa. Jarumi Jarumi Umar ya jinjina kai “Ina godiya ranka ya dade, ya mahaifina yake dafatan yana cikin koshin lafiya?" "Yanzu haka ya koma gida tun jiya mun rabu da shi, kuma ya san da cewar kana cikin hadari tun da ya fuskanci Waziri Ja'afar ya san cewar ka taho birnin don haka da zan zo nan ya bani amanarka, nagode wa Allah da ya sa na riske ka a kan lokaci. Yanzu abin da nake da bukata da kai ka kwanta ka samu hutawa, duk wani abu da za a zartar da shi ko fahimta a birnnin Shamnun yana gare ni, kuma zan aiwatar da shi bisa yaddar Allah, wannan nauyin mahaifina ya dora min kuma shi ne gwaji na farko daga samun nagartar sarauta ta”. Yarima Abbas ya mike tsaye cikin sauri ya juya ya fita tare da dakarunsa ya barsu a tsaye anan. Kai tsaye ya
🏠