cikin tsana abokan tafiyarsa a dai-dai lokacin Mu'az ya kasa jure wa
yayi kukan kura ya kwalla kabbar, dukkanin su uku suka zare
takubbansu suka dauki kan Jarumi Umar. Dakaru suka sha kanšu
suka tare su ana kokari fara dauki ba dadi. Wata kibibiya kamar
walkiya ta ta wuce ta saman kawunan mutane daidai igiyar da aka
daure Jarumi Umar ta shigar burgu ta yanke ta, kai kace takobi aka
saka aka yanke igiyar, Jarumi Umar ya fadi kasa ko shurawa baya yi.
bature
56 Page
57 Page
Sarauniya Ruma da Waziri suka mike da kallo cikin kaduwa
da tunanin waye ya zo ya katse wannan al'amari.
Idanuwansu akan Yarima Abbas yana tsaye da kwari a
hannunsa idanuwansa na kallon gangar jikin Jarumi Umar.
Koda ganin Yarima Abbas sai kowa dake wajen ya rissina kai
kasa alamar girmamawa, hatta Waziri da Sarauniya Ruma, sai da
suka sunkuyar da kai kasa, cikinsu ya duri ruwa.
A Wannan lokacin Mu'az da su Dawan suka yi sauri suka
ratsa mutane suka isa kan gawar Jarumi Umar suna masu ihu da
kururuwa.
Dawan ya fada kansa ya dago shi ya cire masa bakar hular
rufe fuska da take sanye akanshi, duk ya hada majina idanuwansa
sun yi tulu-tulu kamar zai zazzago.
Dawan ya saka hannunsa kan jijiyar wuyansa. Saklahu ya
saka a hannunsa, duk su biyu suka fara wata irin fara'a kamar wasu
ciwon hauka, "Yana raye yana raye yana raye, haka suka dinga
maimaita. Muaz ma hannunsa ya saka ya ji, yana tabbatarwa ya saba
shi, a kawo agaji yana daye yana raye.
Waziri ya karaso ga Yarima. Yarima bai dube shi ba,
idanuwansa na kan Jarumi Umar da ake kokarin ceton rayuwarsa.
"Yarima...."
دو
Yarima ya katse shi da cewa “Ka je ka yi kokarin ceton
rayuwar Jarumi Umar kafin ka zo mu yi Magana duk wani likitan da
ka san kwararre ne ka neme shi domin ku ceci rayuwarsa.
**
"Ki ta shi❞
Wata murya ta tashe ta, a cikin baccin da take cikin dare, ko
da ta mike zaune sai ta ga dakin babu kowa,tabbas kuma ta ji an
tashe wani haske ta hango daga bakin kofa tana tsayar da hankalina
wajen ta hango wata kyakkyawarmace sanye da fararin kaya sannan
bature
•
58 | Page
haske har daukar ido yake, ta mike tsaye budurwa ta ce "Ki zo in
sada ki da dan uwanki Salman".
Ta fada da daddar muryarta, kafin ta yi mata tambayar
budurwa ta yi gaba ita kuma sai ta ji tana mai bin bayanta har suka
fita daga cikin daki ta fito waje babu kowa a farfajiyar gidan Hakimi
Abdullahi bin Sharjas, abin da ya bata mamaki ke nan.
Babu masu tsaron dare bare na safe babu kowa sai kukan
tsuntsaye ta so ta gaza bin bayan budurwa amma tazarada ta bata ya
sa takeson ta ji me ke tafe da ita. Don haka ta kara sauri dan ta
cimma ta.
Koda ta ci gaba da binta a baya har suka yi nisa can nesa
kadan sai wannan budurwa ta kyakyace da dariyar mugunta. Jin
wannan dariya ya sa Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta dago da
kanta cikin mamaki sai ta ga wajen ya cika da mutane sannan ga
wani mutum a gaban rundunar dakaru sama da dubu sun sashi a gaba
daure yake da sassarin bakin karfe hannu da kafa, fuskarsa a rufe ba
a gane ko waye shi.
Tana tsaye ta zuba ido gabanta yana faduwa sai wani
mahayin doki mai suffar kafurci ya bayyana a bisa dokinsa yana
zagaye wannan mutum da yake a daure, har sai da ya zagaya shi sau
uku ana hudu ne ya tsaya ya saka kaifin takobin nasa ya cire wannan
hular da ta rufe wa mutumin fuska sai ga Jarumi Jarumi Umar ya
bayyana suka yi kallo kallo da shi idanuwansa na zubda hawaye.
Ta tawo da gudun don ta zo inda yake amma kafin ta zo
wannan Katon Sadauki ya saka takobinsa ya cirewa Jarumi Umar
kai, jinin yayi tsartuwa har ya bata mata fuska. Ta kwala wała
mahaukaciyar kara mai amsa kuwa da amon. Tana ji tana kallo
gangar jikinsa ta sulale kasa, haka kansa yayi katantanwa a gabanta,
da ta durkushe a kasa. Kafafuwanta sun kasa daukarta.
bature
59 Page
"Jarumi Umar Jarumi Umar! Jarumi Umar!! Ta kwala kiran
sunansa sau uku. Firgigit ta farka daga bacci mai nauyi ne ya dauke
Gimbiya Suhaila bin Ababakari bayan da ta idar da sallar asuba, ta yi
sa'ar gaske da ta samu wannan bacci tsawon lokaci da ta dauka bata
samu kanta a wannan halin ba, don haka babu ma wadda ya tashe ta
ko don ta je ta gana da Abdullahi bin Sharjas domin jiya ya dawo a
ciki dare.
Ta farka a razane a tunaninta abin da ya faru yana nan a zahiri
don hakada gudu ta fita, Kuyangarta Rumaisa, ta riko hannunta,
ammaina ta kwace tana za su kashe shi. Tana fita sararin tsakar gidan
taga ana ta aiki irin wanda aka saba yau da gobe batare da wani
tashin hankali ba. Addu'a ta fara yi tana sauke numfashi kasa kasa.
Kubrat dake bada Jarumi Umarni ta lura da ita. Gimbiya Suhaila bin
Ababakari tana ci gaba da addu'a har ta samu nutsuwa acikin ranta
ta tabbatar da ba gaskiya bane abin da ya faru da ita mafarki take yi.
Akwai wata budurwa da bata wuce sa'ar Suhaila bin
Ababakari ba, ana mata lakabi da Hamdiya, Hamdiya wato
kyakkyawar budurwa ce da ta zama ‘yar riko a hannun Kubra, tun
tana da kuruciyarta, yar aminin Abdullahi bin Sharjas ce da ya rasu
tun tan