sukwane shi bashi ya tsaya ba sai gidan Waziri Ja'afar, ai kuwa Waziri yayi matukar jin dadin hirar da ta wanzu a a tsakanin Yarima da Abdullahi bin Sharjas, ya zo kan gabar da zai ruru wutar gaba a tsakanin yarima da Sarki, ya kuma hada wutar gaba da Abdullahi bin Sharjas har ya ja a kashe Abdullahi bin Sharjas domin alaka da yayan Sarki ita hanya mafi sauki da zaka hallaka makiyinka. Don haka ya ci ka da farin ciki yayi kuma tura
bature
54 Page
wata Baiwarsa zuwa cikin gidan Sarki don ta kai labaringa Siyama
domin itama ta kwana tana farin ciki
Washe gari da safe gidan Sarautar Shamnun ta cika ta batse domin an yi sanarwa an kama daya daga cikin dan leken asiri za kuma a gurfanar da shi a rataye shi kamar yadda ake yiwa duk wani mai laifin cin amanar kasa. Saboda haka tun sassafe mutane suke
zuwa wannan filin.
Mu'az, Dawan, Kubait Saklahul dukkaninsu suna cikin wannan babban fili domin saka ido su ga waye maciyi amanar kasa, duk da zuciyarsa na dukan uku uku idan sun tuna cewar Jarumi Jarumi Umar ne da aka kama suka yank masa wannan hukuncin sai hankalunsu ya tashi har su rasa abin da za su yi, sun saka a ransa matukar Jarumi Jarumi Umar ne ba za su bari hakan ta faru ba, sai
sun yamutsa wannan waje yadda sai dai su gaba daya a kama su a
kashe su gabadaya.
Wajen awa guda ke nan suna tsaye suna jiran ganin abin da suke zargi, sai ga mahaifiyar Sarki ta fito a madadin Sarki wato Sarauniya Ruma, Waziri na beye da ita a baya da zabga zabgan karatan dakaru domin basu kariya, an tanadi wajen zamanta mai kawatarwa. A inda take zaune akwai raga raga yadda babu wani
mahaluki da zai iya cutar da ita.
Bata jima da zama ba aka fito da Jarumi Umar fuskarsa a rufe kuma an daddaure shi da sasari na bakin karfe ana tunkudo shi
dakaru ne suka baibaye shi.
**
A tsakiyar fili ga wajen rataya nan a bisa wani babban teburi
wadda sai mutane sun daga kawunansu sannan za su iya hango mutum an tsara wannan wajen tun shekaru dari uku da suka shude,
tun lokacin da kafurai ke mulkin kasar kafin kasar ta dawo hannun
musulmai.
bature
55 Page
Lokacin da aka gabatar da shi wajen ya rude har wasu da aka
biya kudade aka dauki nauyinsu suka fara jefansa da takalmansa
wasu da basu san hakikanin meke faruwa ba su ma suka dauki
duwatsu da wasu abubuwan kasazanta suna jefansu da shi
Tun kafin a cire masa abin fuskar da takalminsa da kafadarsa
suka shaida abokinsu ne kuma shugabansu, sai suka fara shiga
damuwa domin basu san hanyar da za su bi don yaki da wadanan
zaratan dakarun ba, nasihar Abdullahi bin Sharjas a kullum
kodayaushe, ka da ka yaki dan uwanka musulmi da takobi, ka yake
shi da zuciyarka, da kuma harshenka, iyaka iyawarka, idan kaga zai
cutar da kai ka guje shi. Babu abin da Hakimi ya tsana irin yakar
juna.
Tabbas suka zare makami sai an yi mutuwar kasko kafin su
kwaci Jarumi Jarumi Umar, to amma tunda har Jarumi Umar ya gaza
aiwatar da komai, dole su yi hakuri da shi dominn yin wani abu a
wannan wajen zasu tsinci kansu cikin rashin madafa, tabbas suka
kasha rayukan musulmi fushi zai tabbata ga Hakimi kuma za su mutu
a matsayin makiya musulunci.
Babu abin da ya fi musu a nan face addu'ar fadin
"LAHAULAWALA KUWWATA ILLA BILLAHILA ALIYUL
AZEEM.
Wasu majiya karfi suka tura Jarumi Umar izuwa wajen
igiyar, batare da sun bayyana fuskarsa ba suka saka masa igiyar
sannan suka tamke ta, suka koma da baya suna jiran Jarumi Umarni
Sarauniya Ruma. Duk abin da ake yi idonta na kai, tayi shiru tana
kallo bata bada damar a sake shi ba har sai da waziri ya ce "Ranki ya
dade muna kara bata lokaci".
Sannan ta dawo hayyacinta ta mike ta fuskanci jama'a
"Wannan da kuke gani, dan leken asiri ne, masu son haddasawa
kasarmu rikici, masu kaunar ganin jininmu na salwanta a banza, mun
bature
ค
kama shi ne da laifin kawo maganar karya da gaskiya akan abin da
ba zai haifar mana darashin zaman lafiya ba", saboda haka zamy
yanke masa hukunci na kisa bisa rataya".
Ta yi shiru mutanen gari suna nuna goyan bayansu da
amanna da abin da ta fadi, kai tsaye kuma sai ta daga hannunta sama
wadda ta ta sauke za a janye turbin da yake kai ya zama igiyar ta
shake wuyansa harya sheka barzaho cikin dakika daya".
Abokansa suka dora hannu a ka suka ci gaba da addu'a
neman dauki ubangiji a daidai lokacin da Sarauniya Ruma ta sauke
hannunta kasa, alamar Jarumi Umarni da cewar a aiwatar.
Jarumi Umar addu'o'I yake cikin zuciyarsa wadanda
koyowar Annabin Allah ce idan mutum na halin gamuwa da
azalumai da
A'AUZUBIKALIMATILLAHILTAMMAT
masharranta,
MINSHARRI
MAKALAKA
Aka ture wannan turmin Sadauki Jarumi Umar ya fara wutsil
wutsil bai fasa addu'a du'a'a a ba cikin zuciyarsa, jin an ture turmin
sai ya fara kalimatusshahada.
A lokacin da karfin wutsul-wutsul din ya fara ragowa,
idanuwansa, sun kunburo ya fara sakin wani kakari na mutuwa, gaba
daya idanuwansa sun saki, mutuwa na shawagi a ruhinsa, suma ya
gabato a gare shi. Kulli nafsin za'ikatulmaut.
Mutane da ke tsaitsaye suna dubansa wasu cikin tausayi wasu