NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 42

in musulunci saboda cudanya da kafirai yasa al'adunsu suka fara sauya wa hatta masarautar ta rage tsananta wasu abubuwa da suka zama haramun. Abubuwan na faruwa da yawan yan Kasar suna kokawa musamman yan kauyukan da abin bai shafe su sosai ba, sai dai ta kai suna iya hana matan su da samarin su zuwa birnin Bahara saboda tsoron juyewar tunani to amma hakan ba kara min tauye su yayi saboda ya rage musu kasha hamsin cikin dari na tafiyar da kasuwancinsu saboda samari su ne masu karfi a jika wajen tabbatar da nasarar su a kasuwanci. Sun Kai korafi ga Sarki Muhammad farsi salahudden amma saboda kutse da nasara wa suka yi wa maasarautar ya kasa aiwatar da komai duk da cewar Sarki ne adali mai kokarin ganin ya tafiyar da adalci a mulkinsa Babban sakacinsa amanna da wasu jigajigan fadar sa wadanda sune suke tafiyar da komai na mulki, sai abin da suka so ya ji, Karku manta mun kira wata kabila a baya wacce ita ce kabila mafi yawan mutane a cikin birnin Bahara amma kuma ita ce kabila mafi riko da addinin musulunci saboda an samu manyan malamai da suka taso a cikin kabilar marasa adadi wannan kabila ana kiran ta da Kabilar Nur, dan haka ana kiran kauyen Annur. Kauye ne mai dimbin tarihi wadda ya bar baya mai cike da alfahari, basu kai sauran kauyuka birnin Bahara yawan mutane ba amma sun fi kowane Kauye karin suna hatta a fadar sarki baka jin kalmar kowane Kauye face Annur haka zalika munafukai masu yin zagon kasa suna ambaton bature 4|Page kauyen Annur a kowane lokaci, takororinsu kauyuka masu yin hassada da kauyen suma suna ambaton kauyen Annur. Abdullahi bin Sharjas Ibn Abdullahi kuwaif shi ne Hakimi kuma jigo a cikin Hakiman Kasar Bahara. Yana da shekara saba'in da bakwai. Yana da yaya takwas sai da ya haifi yaya har biyar mata sannan ya haifi maza uku. Kubra ita ce matarsa ta farko wacce suka yi gwagwarmaya rayuwa da ita, ita ce take da mata hudu maza biyu, sai uwar gidan da take da mace daya namiji daya, Ana mata lakabi da Humaira ibn Sa'ad Yayansa maza biyu gwarazan jarumai ne masu kaunar ci gaban musulunci, Babban shi ne Ahmad Abdullahi bin Sharjas Abdullahi Ibn Kuwaif sai Jarumi Umar Abdullahi bin Sharjas Abdullahi Ibn Kuwaif matasa ne masu karfi a jika, masu iya sarrafa duk wani nau'in makami, masu hikima da basira. Ahmad yana tsaka da horor da mata sa salon yaki a daidai lokacin da yake cewa "Duk lokacin da yaki yayi tsamari ya zamana kun, zamo yan kalilan a gaban abokan gaba kamar sun ninka ku sau uku a hankalce ba za ku tsaya ku ci gaba da fafatawa da su ba, domin za su yi galaba akan ku, abu na farko ku yi wa jagoranku inkiya don ya hankalta domin yayi muku izinin ja da baya" Da gudu wani mahayi ya shigo cikin filin a bisa ingarman Dokinsa, yana zuwa batare da dokin ya tsaya ba ya dira gaban Ahmad ya sallama gami da gaisuwa irin ta jarumai ya ce "Yarima sako daga Yarima Jarumi Umar cewa ya bi sahun wasu daukacin kekunan doki da suka fito daga Garin DURSA sun nufi babban birni, ya shaida min cewa lallai yana bukatar mayaka su biyo bayansa. Koda Ahmad ya gama jin haka sai ransa ya baci ya ce cikin bacin ra "yaushe ne Jarumi Umar zai daina dauko magana, menene abin da yayi masa zafi da kafiran Dursa da babbar birni". Kowa yayi shiru yana sauraren Jarumi Umarni Ahmad kadan ya ce "DAWAN yanzu shi da su waye tare na ga abokan tafiyar sa suna muhallin su". DAWAN ya gyara tsaiwa ya ce, daga ni sai shi muka fice tun safe ayarin ne suna da yawa akalla mahaya doki ashirin na kasa bature 5 Page goma, tare da makamai don haka ya ce lallai sai dai ni na zo don shi ba zai iya bari su bace masa ba don basu tare da`alkairi". Ahmad ya ce "Maza ka sanar wa da abokan sa, ku yi gaba ni kuma zan sanar da Sarki". Kai tsaye Dawan yayi sauri ya tafi wajen abokansa dan sanar da su hali da Umar yake ciki. *** Wani kyakkyawan saurayi ne, mai tarin kyawu da zati irin na mazaje yana da tsananin kwarjini shekarunsa za su tasarwa ashirin da hudu, Dokinsa wani ingarma ne ya zauna cif cif da shi kayan sulki ne a jikinsa da takobi rataye a kugunsa, sai kibiya a kafadarsa ya rataya ta. Ta cikin ciyayi yake bin sahun kafiran Darsun sannu a hankali yadda ba za su gane ana bin sahunsu ba, daga nesa yana hango yadda lamarin ke tafiya. ** Duniya dole ne ta zama tamu, idan har muka bar yakar musulunci muka juya baya tabbas za su ci gaba da yaduwa a doron kasa su ci gaba da mamaya, saboda haka dole ne mu kashe sarakunansu, manyan malumansu mu dasa mugun rikicin a cikin yankunnansu, mu kwashe dukiyoyinsu, mu zamar da su bayinmu abin bautarwarmu a doron duniya, Wannanshi ne yakin da zamu yi" Koda Sarkin JARMUR JAKUB ya tsaya a nan a bayaninsa da yake guduna a karkashin sarakunan Kiristoci sai ya dube su daya bayan daya yana mai nuna su da hannunsa cikin izza da isa gami da kasaita. An halicci duniya domin mu ne, ba domin su ba, domin mu ke da mafiya yawan Annabawa muke da yawan lardinai mafi kyau, muke da fikira, mu ke da gine-gine mafi kyau, su bayi ne namu,
🏠