NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 42

zango. bature 51 Page 6 Bayan ya sauka daga kan dokinsa wani Bawansa da ake kira Banu, ya ja doki izuwa wata inuwa ya daure shi a jikin bishiya ya dawo domin bin Jarumi Umarnin Yarima Abbas. "Ka je ka nema min iso wajen Hakimi Abdullahi bin Sharjas". Jim kadan ya dawo ya sanar da Yarima cewar Hakimi yana jiran zuwansa. Shi kadai batare da wasu dakaru sun rufa masa baya domin sun nufo shi ya dakatar da su. Shi ma Abdullahi bin Sharjas sai ya baro sansaninsa sai da suka zo tsakiya sannan suka hadu a karkashin wata bishiya a kuma daidai inda wannan munafukin yake labe wanda zai iya jin duk wani abu da za su zanta. Yarima Abba ya yiwa Abdullahi bin Sharjas murmushi gami da durkusawa da niyar ya gaida shi... Abdullahi bin Sharjas ya rike hannayensa ya tashe shi tsaye gami da cewar "Idan Allah ya so a yiwa wani gaisuwa makamancin haka to Manzon Allah ne, idan ma'aikin Allah ya so mu yi haka wajen gaisuwa mai koyi da bautar Allah,ba zai hane mu ba, ba kuma zai bawa dukkanin makusantanshi hannun dan yi musabaha ba. Ku ne mafi daraja domin ku ne sarauta, amma gaisuwa da addini ya tanadarwa bayin Allah shi ne su yi musabaha shi ne ladan hakan yake a rubuce". Wani kayataccen murmushi Abbas yayi gami da cewa "Wannan koyarwa ce da Kakana, yake yawan sanar da ni, Abban bin Zubair nagode kwarai". Abdullahi bin Sharjas yayi murmushi gami da tunawa da Abbas. Ya ce "Allah ya kai rahama kabarinsa... Mahaifiyarka ta sanar da ni zamu yi ganawa ta musamman da kai, ina fatan dai lafiya kuma babu wani abu da na kuskure da muka aikata”. Yarima Abbas yace "Astagfirilla, babu wani zargi mara kyau, daga gare mu zuwa gareka sai tsantsar fahimtar da kuma soyayya, Mahaifiyata ta turo ni wajenka ne domin muna da bukatar samun bature goyon bayanka, a game da duk abin da yake faruwa a masarauta, ta turo ni ne a madadinta saboda idan har ta yi gani da kai to munafukai zasu fahimci wani abu, za kuma su iya kulla sharri da zai jefa mu cikin tsananin Sarki da azabarsa". Abdullahi bin SHarjas yayi murmushi gami cewa “Me ke tafe da kai, me kuma kuke bukata daga gare ni?" "Goyan baya kamar yadda na fada a farko, kasancewar ba mu da wasu masu goya mana baya a gidan sarauta ta saurari labarinka daga wajen wata Baiwarta da ka taba kyautar da ita ga Sarki wacce ka musuluntar ka saka mata suna" Hakimi yayi shiru yana tunani daga bisani Yarimaya rage masa dogon nazari ya ce "Hindu" Hakimi Abdullahi yayi murmushi yace Baiwar Allah, na tuno ta kwarai da gaske. To abin da zan sanar da kai Yarima shi ne birninku yana cike da kalubale, munafukai mahandama, ba zan fahimci wane daure bane ya mamaye masarauta amma daga bangarena ina da tabbacin Waziri Ja'afar yana daga cikin matsalolin masarauta wanda a yanzu na fahimci zahirin abin ba badini ba, na baro babban birni da haushin Sarki Muhammad farsi saboda gabaki daya Sarki Muhammad farsi ya sauya daga babban rikon da ake yiwa Daula, ya zama kamar amsar Jarumi Umarni yakeyi daga jama'ar da yake mulka, abin da nake nufi sam Sarki ya sauya. "Tabbas akwai abubuwa da dama wadanda suke da daure kai ammayin fito na fito da a zauren Majalisa babban kalubale ne malamai da dama sun rasa rayukansu, duk bautar da suka yi wa kasa sun mutu a matsayin maciya amanar kasa, duk kuma ba don dalilin sun gaza ba sai kulla sharri" "Ina son gaskiya, ina son aiki da amana kuma ina son ayi komai domin Allah ba domin rububin sarauta ba, sai domin cancanta bisa gaskiya, a wajena da kai da Yarima Zaid duk daya ne banbancin bature 52 Page 53 Page da zai kalla a tsakaninku waye shugaban waye adalcinsa ya fi tabbatuwa ga Al'umma saboda haka ina bayanku, aikin ka na kwarai shi ne zai banbanta kada shi, dan haka ina bayanku ku duka Allah mafi sani ya zaba mana mafi alkairi, abu daya ne yanzu yake damuna, lallai idan ka je kasar Shamnun na sani cewa akwai dana Jarumi Umar da ya je domin ya gano min abin da yake faruwa don tabbatar da gaskiya, ku yi aiki na gaskiya a birnin don wanzar da zaman lafiya, sannan ka rike Jarumi Umar matsayin da kake son ka rike ni domin shi ne abin kallo a yanzu a kabilar mu, mu tamu ta kare muna kan gaba da ta kowacce fuska da makiya ta kowane fuska neman rayuwar mu suke yi, shekaru, a sun saka mu a gaba a kowane lokaci mutuwa na iya riskarmu, daga karshe ina mai sanar da kai ka rike gaskiya da amana, ka kai kukanka wajen ubangijin da ya halicce ka, duk rintsi duk tsanani, tabbas za kasamu babban rabo, zan wuce ina maka fatan Nasara a inda zaka je domin sassancin". "Nagode kwarai, na ji dadin maganarka, Allah ya daukaka musulunci da kasarmu baki daya". "Ameen, Allah ya dawo da kai lafiya, kuma ka bi a sannu, domin duk takunka daya bayansa makiyinka ne ke saka kafa". Daga nan kowa ya juya yana mai jin dadin tattaunawar da suka yi, Abbas ya haye dokinsa, shi ma Abdullahi bin Sharjas ya haye nashi dokins suka tasarwa hanya shi kuwa dan munafukin Waziri Ja'afar sai da ya tabbatar kowa ya baci da gani sannan ya zo ya hau nashi dokin ya
🏠