NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 42

da shawara mai kyau, dan haka bai jira wata wata ba ya koma ya sanarwa da masu gadin Jarumi Umar cewar lallai su tsaurara tsaro akan wannan bakon domin akwai hatsarin gaske a tattare da shi, ya kuma tsallaka ya kara gargadi kan cewar lallai a kara baza bincike a game da bakin ido, ko wadanda aka gansu sun nuna alamun tambaya a cikin birnin koda sun kasance yan asalin birni. Kai tsaye ya tura sakon ganawa da Sarki mai jiran gado wato Hilal domin sanar da shi karya da gaskiya. BABBAN BIRNIN BAHARA Lokacin da Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya fuskanci lallai akwai babban kalubale a game da ja da waziri, domin ya gama cutar masarauta, ya gama shiryawa duk wani makircin da ya tsara sai tsoro da fargaba suka tasarwa ransa ya fara tunanin makomar dansa, nan da nan hankalinsa ya karkata zuwa gida, don ya san cewar tunda har Waziri ya san zan taku zuwa ga Sarki to babu shakka ya san labarin zuwan dansa Shamnun, hankalin Hakimi Abdullahi bin SHarjasllah yayu matukar dugunzuma, nan take a dakin da aka sauke shi ya mike tsaye da niyar fita domin su koma gida sai kuma ya ji tafiya a na kokarin shigowa cikin dakin. Abin da ya dakatar da shi daga mikewa ke nan, ya na zaune wani bawa ya shigo ya durkusa ya gaida shi, gami da mika masa wata farar takadda, cikin mamaki ya amsa ya ce "Daga ina?" Bawan ya jinjina kai ya kalli takaddar "Idan ka karanta zaka fahimta, an bani ne kawai an ce na kawo maka”. Daga nan ya fahimci abin dan haka sai ya salami Bawan bayan fitarsa da kadan ya bude takaddar ya fara karantawa kamar haka bature 49 Page "Zuwa ga adalin Hakimi, mai yi domin Allah, da na zai kasance a bisa hanyar RUD, mararrabar da zata yanke zuwa tafiyar da Sarki ya Jarumi Umarce shi zuwa birnin SHamnun da kuma tafiyar kauyenka, idan hark a riga shi isa ka jira shi a can, idan kuma ya rig aka zai jira ka" daga Sarauniya Haulet ibn Abbas. koda jin wannan batu sai Waziri Abdullahi bin SHarjas ya fice daga dakin tarar baki kai tsaye ya nufi inda Abdallahi da tawagarsu ke tsaitsaye batare da bata lokaci ba kawai ya kama dokinsa ya haye suma suka haye nasu dawakan, cikin sauri ya zaburi dokinsa, suna fita daga masarauta dama akwai wani munafuki da waziri ya masa Jarumi Umarni da duk inda suka bi yabi sahunsu haka kuwa aka yi yana barin masarauta wannan munafukin ya ci gaba da binsu nesa nesa, har izuwa mararrabar rud, adaidai nan ne Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce mu dakata anan mu yi sallar la'asar kafin mu ci gaba da tafiya. Tun da munafikin yake biye da su basu taba tunanin su yi binciken hakan ba dan haka har zuwa wannan masaukin nasu basu iya gane wani na biye da su ba. Da suka samu wajen shi ma sai ya nemi wani waje nesa da su yayi kwantan bauna yadda babu wanda zai hango shi, Shi kuma yana hango su. Waziri Ja'afar kai tsaye ya sa a ka kira sarauniya Siyama domin hakansu na neman cimma ruwa. Lokacin da ta iso dakin gani yana tsaye yana jiranta don haka gaisuwa kawai ya gabatar mata ya dora da maganar da ta kawo shi, duk abin da ya faru ya sanar da ita. "Akwai babbar matsalar da zata iya jefa mu cikin rikici matukar Hilal bai zama Sarkin Shamnun ba saboda shi ne kadai Sarki daya da ya rage da zai bamu goyon bayan wajen dabbaka Yarima Hilal idan lokaci yayi, muna bukatar masautu shida, wadanda suke karkashin mulkin Bahara, wadanda mun kafa biyu bature 50 Page Shamnun zata zama ta uku, kin ga in mun samu Shamnu mun ci rabi kenan, ragowar za su zamo mana a saukake, to amma yanzu Sarki ya tura Yarima Abbas akan sasancin matsalar da take faruwa a birnin Shamnun". Siyama ta yi shiru tana jujjuya maganganun waziri Ja'afar bata ce komai ba har sai da ta yi nazari sosai sannan ta ce “Ja'afar ka yi dukkan me yiwu wajen kare mana mutumci a tun baya a yanzu ma kayi iya bakin kokarinka a gaban Sarki domin kahanashi ya fahimci mu ne muke da hannu dumu-dumu akan rikicin birnin Shamnun,abu daya za a yi yanzu ina a shi ne mu tabbatar da cewar mun samo Yarima Salman, domin mu hallakashi, na fuskanci matukar Salman yana raye sai yayi duk yadda zai yi wajen kwatar masarautarsa, kuma matukar ya gana da Mijina Sarki Muhammad farsi ka yi sani cewa Sarki na cikin halin kasala da rauni na dangane da maganin da yake kwana akai wanda muka samu dakyar, kuma ka san wa'adin wannan maganin yana daf da karewa matukar Muhammad farsi ya dawo cikin hayyacinsa, ba mu kafa kanmu ba akwai babbar barazana, lallai ka tashe manzo zuwa Shamnun da dinare masu yawan gaske don a kara rabawa tsoffin nan aka kuma karawa Hilal karfin gwiwa akan ya cire tsoro babu wani abu da zai faru, inda sun tsaya akan yadda muka dora su, to la shakka yarima Abbas ba zai fahimci komai ba”. Da wannan waziri Ja'afar ya baro dakin Gani da ya faru tsakaninsa da Matar Sarki Muhammad farsi Siyama, don haka kai tsaye ya koma gidansa don kara shiri na gaske. A lokacin da rundunar Yarima Abbas ta iso mararrabar Rūd sai ya sa aka dakata da tafiyar da ake yi, nesa kadan da inda su Hakimi Abdullahi ya yada
🏠