rsa, yanzu ba mu da
abin da zamu iya sai mu jira zuwa anjima mu ga ni".
Lokacin da Dakaren ya shiga wajen Waziri Adnan a lokacin
yana tare da wasu dattijan kasa ana shirin yadda za a cimma nasara
wajen dora Yarima Hilal a kan karagar mulki a gobe, sai ga sakon
zuwan dakaren kofa,, ko da jin haka sai ya dakatar da bayanin da
yake domin ya san akwai babban al'amari.
Koda ya fito sai shugaban dakaru ya zayyane masa duk abin
da ya faru har ya shaidamasa yanzu haka yana hannu mun tsare shi".
Koda waziri ya ji wannan batu cikin gaggawa yayi gaba don
zuwa kurkuku domin ya je ido ya gane ya kuma tabbatar da zargin da
ake yi.
Koda suka isa kurkuku sai masu tsare wajen suka fito da
Jarumi Umar suka gurfanar da shi gaban waziri suna mai dukar masa
da kai kasa. Waziri yayi dariyar keta yace "Ku kyale shi, ai bako ne
kuma ba mu da tabbacin abin da ke tafe da shi."
Suka sake shi Jarumi Umar ya dago kai ya dubi Waziri
Adnan ya ce "Ka sada ni ga Sarki Hilal domin ina da sakon gaggawa
a gare shi, kafin wata matsala ta biyo baya".
Koda Waziri ya ji wannan batu sai ya gigiza kai yana dariya
ya ce "Me ke tafe da kai ga Sarki?"
bature
?
46 Page
Jarumi Umar ya girgiza kai ya ce "Da ace sakon naka ne da
zan sanar da kai amma tun da har wannan sako ba naka bane, babu
dalilin da zai san a sanar da kai".
Waziri ya ce "Ashe ba zaka rayu ba, matukar baka sanar da ni
, to ka yi sani cewar rayuwarka tana kan gargara”.
sakon Sarkiba Jarumi Umar yayi murmushi ya ce "Kamar yadda taka
rayuwar take kan gargara, bari in baka wani labara kadan mu biyar
ne ke dauke da sako zuwa ga Sarki, ragowar hudun suna kokarin
ganawa da Sarki akowane lokaci idan sun hadu da Sarki za su bashi
labarin cewar kana tsare da ni, idan kuma suka koma ga Sarki
Muhammad farsi za su sanar da shi labarin cewar kai ne
ummul'aba'isin hana ruwa gudu kamar yadda Yarima Salman ya
sanar da shi cewar kun siye duk wani mai zaben Sarki a majalisa kun
basu dukiya don su zabi Sarki Hilal maimakon zababben Salman".
Koda jin wannan batu sai hankalin Waziri Adnan y abaci ya
tunzura wani gumi ya fara taso masa. Don haka sai ya fadi a fusace a
mayar da Jarumi Umar cikin kurkuku da ya fito kai tsaye yayi sirri
da dakarun don su yi binciken gidan kaf domin neman wasu baki da
ba a san kosu waye ba.
Sai da aka kusan yini har yammaci ana wannan kewayen ba a
samu su Dawan ba, aka zo aka sanar da Waziri hankalinsa ya kara
tashi, don haka sai ya tashi dan aike kai tsaye zuwa ga waziri Ja'far
domin ya tabbatar masa da halin da ake ciki.
Lokacin da Waziri Adnan ya koma majalisinsa ya kasa
sanarwa da Tsuffin fada abin da ke faruwa saboda dama yana kan
kara basu Karfin giwa akan zabar Sarki Hilal, don haka sai ya
sallame su ya ci gaba da nazari da safa da marwa yana cikin wannan
lamarin sai uwar Yarima Hilal ta fado masa a rai ita kadai ce zata
samarwa da lamarin mafita saboda tafi danta son ya zama Sarki
saboda tana tsoron Salman akan irin yadda ta ci zarafin mahaifiyarsa
bature
47 Page
da yadda ta yi sanadiyar barinta duniya, wadda ta san cewar matukar
Salman yah au kan karagar mulki sai ya daukarwa mahaifiyarsa
fansa.
A dakin gani suka hadu wani daki ne dake mararrabar fadar
Sarki da cikin bangaren mata wacce idan ana zaman fada aka so
matan Sarki su ji abin da ke faruwa suna iya hawa sama suna hango
mutane amma mutane basa hango su, saboda wasu raga raga a can
sama sannan suna jin duk abin da ke faruwa, haka dakin Gani yake a
kasa idan wani mai mulki ko wani dan aike ko mahaifin Sarauniya ya
zo wajen diyarsa idan za su gana suna amfani da wannan dakin gani
ne, babu kowaye kai idan ka zo daki ne guda biyu wanda aka tsaga
raga raga a haka za ku gana da ‘ya'yan Sarki ko wasu masu aiki a
gidan Sarki ba a yadda a hadu fuska da fuska ba, sannan za ka yi
kasa da kanka ko ta cikin ragar baka isa ka hada ido da matar Sarki
ba.
da
=
har zuwan Sarauniya Ruma, koda ta
iso bai bata lokaci ba ya zayyane mata duk halin da ake ciki, hatta
dan sakon da ya tasa zuwa wajen waziri Ja'far ya sanar mata. Koda
ya zo karshe sai ta ce "Lallai muna cikin tashin hankali, amma duk
da haka ka yi abu mai kyau, abin da nake so mu yi yanzu, lallai shi
ne ka samu Yarima Hilal ka sanar da shi, cewar shi wannan dan aikin
dan leken asiri ne ba wai aikoshi a ka yi ba, saboda ya bada damar
kashe shi, idan mun kashe shi, batare da Sarki mai jiran gado ya san
cewar dan aike ne daga fadar Sarki Muhammad farsi, ina maitabbatar
maka har yanzu akwai shakka da tsoro a zuciyar Hilal, saboda haka
kada mu bari ya ji wani labara Sarki Muhammad farsi don zai iya
tsorata ya hakura da wannan mulki saboda tsoron mutuwa, idan
kuwa muka kashe bakon nan babu wani abu da zai biyo baya koda ya
biyo za mu sanar da Sarki Muhammad farsi cewar cewa yayi damu
shi dan aike ne daga Yarima Salman.
A nan Waziri ya kasance
bature
48 Page
Koda jin wannan shawara da sarauniya Ruma ta bada sai
Waziri ya samu kansa yana mai cikin farin ciki domin lokaci guda ta
fitar