ole mu yi
aikin da hikima".
Suka shiru suka zurfafa cikin tunani domin gano abin da dan
uwansa ya hango a nan gaba. Ko da suka samu dan takin lokaci suna
wannan nazari sai Mu'az ya ce "Hikimar ka muke jira ya kai
gwarzon Karni domin ka san dai duk abin da za mu ce naka shi ne
mafita, domin ban hango wata dabara da za mu yi wajen shiga birnin
Shamnum batare da mu samu matsala ba".
Jarumi Jarumi Umar ya dubi kowa daya bayan daya domin
tunanin ko akwai mai Magana duk kowa ya girgiza alamar ba shi da
cewa sai da ya je kai Dawan sai Dawan yace "Mu'az shi ne mafi
hikima baya kai tun da har ya baka damar naka nazari ba mu da wani
abin cewa don haka muna saurarenka".
Jarumi Jarumi Umar ya dauki wani kara dake gefan kafarsa
yace “Ni ma bani da wata dabara, ta shiga gidan Sarauta har mu gaña
da Sarki sai hanya daya, hanyar daya ce dole a cikin mu za mu
rarrabu kashi biyar kowa yayi na shi kokarin duk wadda ya sha a
kokarin shiga gidan Sarauta to shi ne zai fanshe wanda aka kama in
kuma mun shiga dukkanin mu, to hakan shi ne fatan mu, Mu'az ka
bature
43 Page
tafi izuwa gidan Sarauta a matsayin dan aike daga bakin Mahaifina,
kai ma Dawan, Kai ma Saklahu, kai ma Kubait, kowa zai tafi da
ma'ana daban, idan Mu'az ya je bakin kofa in fadawa sun tutsiye shi
zai ce da su matafiyi ne shi daga Kasuwar ASSUK, ya zo ne domin
tallata hajjarsa ga sabon Sarki, saboda kaji labarin za a yi rantsuwar
don haka ka zo da bayanin siya da siyarwa ga Sarki.
Dawan kai kuma in ka is aka sanar da su cewar Manomi ne
kai da ka zo daga Zurkul domin kawo tallafin kayan noma ga Sarki
za ka je fada domin neman yaddar Sarki don gabato da kyautarka a
ranar bikin nadin Sarauta.
Kubait ka je a matsayin Malamin da zaka nemi yaddar Sarki
na yin wa'azi a ranar bikin sarauta, Saklahul kai kuma za ka je a
matsayin dan aike daga Birnin Bahara zuwa ga Sarki ka tubure sako
ne da kai da za ka kaiwa Sarki, ku tabbatar kun rike wannan dabarar
duk wadda ya samu nasarar koda an kama mu to tabbas shi zai
fanshe mu domin dolen Sarki ya gaza aiwatar da komai matukar in
ya ji da kunnensa cewar Sarki Muhammad farsi ya san da zuwanmu"
Da wanan shawara suka tasamma cikin birnin kai tsaye ba
tare da bata lokaci ba kowa ya waste ya nufi gidan gadan-gadan
gari guda, masarautar Shamnun
tsohuwar masarauta ce da wani hamshakin takadirin Sarki yayi mulki
a shekaru dari da suka shude, shi ya samar da masarautar tana da
girman gaske don a wancan lokaci a cikin masarautar dukka jama'a
birnin suke, saboda girmanta, a nan gidaje da kasuwannin birnin
suke, sai da duniya ta kara fadi aka samu jama'a da baki da dama,
sannan ne aka samar da wasu sasssa a cikin birnin. Saboda haka
yanzu idan ka ga wani a gidan to attajiri ne ko mai mulki a kasar,
amma duk talakawan gari da baki an tanadar musu waje a waje.
Babban gida ne ko na ce
bature
44 Page
Lokacin da Mu'az ya isa kamar yadda Jarumi Umar ya
Jarumi Umarce shi hakaya sanar da masu gadin wajen amma sai suka
nuna sam ba zai shiga ba, haka Dawan da sauran abokansa.
Duk Jarumi Umar na gefe yana kallon su, sai da ya tabbataṛ
duk basu samu nasarar shiga ba sai ya matso kusa da masu tsaron
kofar birnin da nufin shiga sai suka dakatar da shi “Kai ina za je?”
Jarumi Umar yayi shiru daga farko, sai da mai tambayar ya
kara maimaita tambayarsa sannan ya ce "Dan aike ne ni daga Salman
zuwa ga Sarki Hilal?”
Koda ji haka sai dakarun da suke tsaitsaye a bakin kofar suka
tsare shi da dogayen masu suna masu huci da kokarin sukar sa".
"Ka ce mene ne?"
“Ina so ku kai ne gaban Sarki domin ina da sako daga dan
uwansa?"
Dawan Kubait da sauran abokan tafiyarsa da suka ga an tsare
shugabansu da masu sai hankalinsu ya tashi suka yi niyar cire
makamin jikinsu, sai ya daga hannu daga nesan suka fuskanci abin
da yake nufi suka fasa aniyarsu.
Shugaban Dakarun ya ce "Mazak u rufe shi a kurkuku, ku ci
gaba da tsaro ni kuma zan je na sanar da Waziri halin da ake ciki".
"Ba wajen Waziri aka aiko ni ba wajen Sarki Hilal aka aiko
kuma ina da sako ne daga Sarki Muhammad farsi, zuwa gare shi, yin
ganganci da rayuwata tamkar yin ganganci ne ga rayuwar masarautar
Shamnun, don haka kai tsaye ku kai ne ga Sarki".
Shugaban Dakaru ya daka masa tsawa ya ce "Babu wani
wadda zai zo da sako makamancin wannan a bar shi ya shiga ya gana
da Sarki kai tsaye lallai sai dai waziri don haka za mu tsare ka aka
jira har Waziri ya bada Jarumi Umarni, saboda haka ku tafi da shin i
kuma ina nan zuwa”.
bature
45 Page
A haka aka tsare Jarumi Jarumi Umar Shugaban dakarun da
wasu masu dakaru biyu suka bi bayansa zuwa ga Fadar Waziri.
Hankalin abokan tafiyarsa ya tashi ainun suka rasa inda ke
musu dadi illa Mu'az ne kadai babu wani damuwaa tare da shi, daga
bisani ya ce "Ku kwantar da hankali, tabbas Jarumi Umar yana sane
da abin da yake yayi hake ne don a hana mu shiga, shi yasan yadda
zai shiga ciki, domin idan da bai yi haka ba duk ba za mu shiga ba,
kuma za a ka ma mu hakan da yayi akwai hikima