NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 42

ka yi musu alkawarin ci gaba da zama a majalisa, batare da yi musu wani sharri da kagen da za a kore su daga kan karagarsu ba. A dai-dai wannan lokacin Sarki ya katse shi yana mai cewa "Ko Waziri ja'afar yana da wani sani dangane da Gimbiya Suhaila bin Ababakari?" Waziri Ja'afar ya amsa "Ina da shi ya Sarkin duniya”. Sarki ya nuna inda ake tsayuwa a yi bayani don Wazirin ya fito yayi bayanin kare kai. Batare da bata lokaci ba ya fito ya tsaya a gaban Sarki nesa da juna inda kowa zai saurare shi ya ce "Daga birnin Shamnun sako ya zo gare ni cewar Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta gudu daga masarautar Shamnun, saboda haka Sarki mai jiran gado Hilal maijiran gado ya bada Jarumi Umarni a kamo ta duk inda take, wannan labari ya iso min daga masarautar Shamnun cewar an nemi Gimbiya an rasa, dalili ke nan da na ji labarin cewar an bature 40 Page ganta a wajen Hakimi Abdullahi bin Sharjas, shi ne bai yi kasa a gwiwa ba na isa wajensa domin na gasgata”. Yadda Waziri ke maganar cikin ladabi da nuna tsantsar gaskiyarsa. Sarki Muhammad farsi ya jinjina sannan ya dubi Abdullahi bin Sharjas ya ce “Kaji bayaninsa, kuma shine na wakilta game da masarautar Shamnun, ka ga yana da ikon sanin komai”. Da Sarki ya gama wannan jawabin sai ya kara duba ga Waziri Ja'far ya ce "Me yasa Salman ya gudu ya bar Shamnun, me yasa Gimbiya Suhaila bin Ababakari tashiga hannun Arnan, me yasa baka zo min da labarin yanayin da birnin Shamnun ke ciki ba domin a yiwa 'ya'yan Sarki Sulhu?" Waziri Ja'afar ya hadiye wani yawo yace "Amsar farko Yarima Salman bashi da rinjiya a majalisar zabin Sarki, shi ne dalilin da yasa ya gudu saboda an same shi da bada dukiya ga wasu masu zabar Sarki, har sun fito sun bayyana, wadda hakan yana nuni da cewar kai tsaye kisa kai ne domi ya saba dokar masarauta, amsa ta biyu Gimbiya Suhaila bin Ababakari, eh Yarima Salman ya tura mata da sako ta barauniyar hanya domin ta gudo ta je gare shi, domin yana tsoron kada a hallaka ‘yar uwarsa, Yarima Salman yana tare da Kafiri Jaremi bincike ya nuna mana cewar kafiran da suka dauko ta za su kaita birnin Hairam, domin su haddasa yaki a tsakanin yayan Sarki biyu ta wannan damar kuma za su yi amfani da hakan wajen fuskantar matsaloli a yankin musulmai, dalili na uku kuma jiya na dawo daga birnin Shamnun ina son a zaman da za a yi yau na kawo maka bayanin duk da ya faru ya Sarki mai daraja. Bayan waziri ya gama gabato da labarinsa sai ya juya ya dubi Abdullahi bin Sharjas daga nan ya bawa Waziri dama ya koma ya tsaya. bature 41 Page Sarki yayi kusan dakika uku batare da ya ce wani abu ba, sai daga bisani ya dago kai ya dubi dansa Abbas da Zaid ya ce "Zaid ka tafi da dakarun sulhu zuwa birnin Haiman don fuskantar Benjamin a game da dalilin dauko gimbiya Suhaila bin Ababakari kai kuma Abbas na baka aikin bincike da tabbatar da gaskiya a birnin Shamnun, Waziri zai kasance da mu a nan saboda fuskantar wasu matsaloli, ina maka fatan nasara a farkon ayyukanka a masauta a yau. Da yarima Abbas ya ji wannan batu sai ya duka kansa kasa cikin girmamawa ya ce "Amin Baba, kuma da yardar Allah zai yi duk wani abu da zai gamsar da kai da kuma fitar da masarautarka kunya bisa tafarkin shugaban mu Annabi Muhammad farsiu Sallallahu alayye wassalam" Zaid shi maya dukar da kai cikin girmamawa ya ce “Insha Allahu komai zai tafi kamar yadda ka Jarumi Umarta". Sarki ya amsa a cikinsa gami da ci gaba da batu "Hakimi Abdullahi bin Sharjas, ka yi namijin kokari kuma a jinjinawa Jarumi Umar a gaya masa muna alfahari da shi bisa kokarinsa na ceto yar musulmi kuma Gimbiya daga gobar kafurai, sannan muna maka maraba da zuwa babban birni don shigo da abin da ya shige maka duhu, za mu yi aiki kai da fata wajen magance dukkanin abubuwan da za su kawo mana ci gaban kasarmu da musulunci". Daga nan Sarki ya nemi wani mai Karin bayani kowa yayi shiru bai ce ta tafasa ba haka ya tabbatar da cewa ba wani korafi don haka Zaman majalisa ya tashi". ** A tsakanin dagawa rana zuwa kwallewarta suka isa cikin birnin Shamnun, sun yi gudu da dawakai ba tare da yada zango ba, sun isa birnin dai-dai da lokacin da ake kiraye kirayen sallar la'asar don haka sai suka yada zangon farko a bakin garin kusa da wata bature 42 Page rijiya daga gefe ga wani gini nan na saukar baki akwai masallaci a wajen. Lokacin sallar ya riga ya kure shi yasa basu bata lokacin hutu ba suka yi sallar laʼasar sannan ne kuma suka fara tunanin abin da ya dace ayi. A dai-dai wannan lokacin ne suna zaune a bakin ganuwar birnin Shamnum suna hutawa tare da cin abubuwan don cika cikinsu. Jarumi Umar ya nisa ya dubi abokan tafiyarsa ya ce "Da akwai alamun tsaro a birnin nan mai tsauri, kuma ina kyautata zaton maganar mahaifina ta tabbata sakon zuwan mu ya riga mu kara sowa, yanzu dole mu sake shiri domin muka ce za mu tafi gaba gadi tabbas za su yi galaba akan mu a ka ma mu a rufe ko a hallaka a saka mu a lissafin masu goyan bayan rikicin masarauta don haka d
🏠