NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 14 of 42

na bukatar birnin nasa wadda aka kwace masa Birnin Hilayan, sanan yana bukatar diya ta rayuwakan da aka salwantar a birnin yayin gwabza yaki, ya kara tabbatarwa ba zai kara turo sako na hudu ba, kaifin takobi ne zai ci gaba da Magana. A bagaren Kauyen Dire Hakimi Suleman yayi batu a game da bullowar Hangalawa tsille tsille suna zuwa babbar kasuwar Kudu suna tare mutane suna kuma zuwa suna amsar haraji, lallai yana mai kira da babbar masarauta a dauki lamarin da gaske domin sun fara dawowa. A ziyarar da Waziri ya kai kasuwa jiya, ya ci karo da sabbin mutane wadda ya sa an yi bincike a kansu ya gano cewar lallai wasu bature 37 Page mutane ne da suke son haddasa husuma domin sun dauko 'yar marigayi Sarki Ababakari zuwa wannan birnin amma cikin ikon Allah Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya kwace ta daga hannunsu. yau". Wannan su ne bakin labarin da za mu fito da su a zauren mu Fada ta kara yin shiru bayan da Zirkifilu ya kammala kawo batutuwa kamar kullum. Sarki ya gyara zamansa kai tsaye idanuwansa ya dago ya dubi kafatannin ‘yan zaman fada kafın ya dora ya ce "Sako zuwa ga Kafiri Jarman Jakub a gaya masa cewar ba mu da lokacin mai kori, ba kuma da wata Magana da ta rage a tsakanin mu, idan har ya tabbatar Takobin ce kadai za ta yi Magana, to na mu kodayaushe cikin washi suke. Game da Hakimi Suleman lallai a tashi dakaru na gaske a je Kauyen a yi bincike na gaske. Kafin Sarki ya kara Magana ta gaba, sai ga Shugaban Fada ya shigo tun daga nesa ya duka yayi gaisuwa "Akwai sako na musamman ya Sarki mai daraja”. Tun da Waziri ya ga shigowar Sarkin Fada sai hankalinsa ya ta shi, ya shiga zare idanu amma tun da dai yay i aikin hankali tun a jiya ya shigar da batun kafurai a kasuwa karyar da zai yi za a iya gasgata ta, maganar Salman ce wajen binciko lamari wannan kuma ya san shi zai jagoranci zuwa birnin kuma ko ma waye a cikin fadar to maganarsa yake ji. Har Sarki Fada ya je kusa da Sarki yayi masa Magana da ba kowa ne ya ji ba. Ya bawa Sarkin Fada Jarumi Umarni ya fice "Batu a kan Yar Sarki Ababakari ga Hakimi Abdullahi bin Sharjas nan ya iso domin yi mana cikakken bayani". Kowa da ke wajen sai da gabansa ya fadi domin koda wasa aka furta sunan Abdullahi bin Sharjas sai mutane sun shiga hankalinsu sun fara tunanin wata badakalar ta su za ta iya ta shi, bature : | Page saboda tsoronsa da kuma, Sarki na rufe baki Abdullahi bin Sharjas ya bayyana cikin sallama bangaren ya tsaya cak yana kallon kowa cikin fara'a. "Bangaren Masarauta, Malamai, Hakimai 'yan uwana dakatai Wazirin ina muku sallama ta addini musulunci". Kowa ya amsa masa sannan ya nemi wajen tsayuwa ya tsaya a sahon Hakimai. Bayan yin shiru na dan lokaci sai Sarki yayi gyara murya ya ce "Abdullahi bin Sharjas, sako ya zo daga Wazirin Bahara cewa ka kubutar da 'yar Sarki Ababakari daga hannun kafura, z aka iya fitowa ka yi mana Karin bayani”. Abdullahi bin Sharjas ya fito daga inda yake tsaye ya tsaya y ace "Tabbas da na Jarumi Umar shi ne ya tare su ya kuma amso ta ita da wanda yake yi mata hidima, sannan bayan haka Waziri ya zo har Kauye nemanta da yunkurin a bashi ita. Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta sanar da mu cewar Dan Sarki Salman ya saye duk wani Dakare, da duk wani dan majalisar Sarki shi da mahaifiyarsa, na lalllai shi ne zai gaji Sarautar mahaifinsa, a yanzu haka ma ranar rantsuwa kadai ake jira domin shi yake gudanar da komai, sannan ta ce ya bazama nemo dan uwansa Hilal. Shi kuma Yarima Hilal shi ne yay i sako ga 'yar uwarsa cewar ta gudo daga birnin a kokarinta na guduwa suka kama ta kuma suka tilastata akan sai ta kai su ga inda Yarima yake, dakarun da suke tare da ita kafurai ne, kuma sun nufi, Birnin Bahara da ita, wannan dalilin yasa na ce ya dace na zo kada da kafa domin jin ba'asi ko sakacin da Sarki ya jima yana yi ya fara taba martabar Sarautar Bahara" x Wata tsawa Shugaban Dakaru da Waziri suka dakawa Abdullahi bin Sharjas, har da zare takubba. Sarki ya daga musu hannu alamun su dakata cikin tsawa. Shi kuwa ko gezau bai yi ba bature B 38 39 Page domin bait aba zuwa fada bai furta Kalmar sakacin nan ba, ba kuma su fasa kawo masa bar aba, sarki bai fasa dakatar da su ba "Muna bukatar ji daga gare ku, sannan kada ka manta Waziri Ja'far sa'a daya da kawo Suhaila bin Ababakari wajena ya biyo sahunta, shin me ya sani dangane da zuwanta, dole sai an sarewa maciji kai kafin a samu nutsuwa" Koda Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya zo nan a batunsa sai yayi shiru ya kuma koma ya tsaya jin ta bakin Sarki Muhammad farsi. Lokacin Sarki Muhammad farsi yayi dakika biyu yana nazari kafin ya ce wani abu, a wannan lokaci shi ma Waziri Ja'afar yana na shi nazarin da ya kwana yana maimaita amsar da zata fitar da shi daga zargi, don haka tun da dan aikin Shamsu bin Aujarya zo masa yayi tashi dan aiki zuwa masarautar Shamnun abu na farko ya gargadi 'yan majalisar masu zabar Sarki saboda su ne wadanda aka tilasta su, aka kuma cika musu aljihu da sulalla, sannan a
🏠