a shiga turakarsa duk wani abin bukatarsa
ya dauko ya fito, bai tsaya ko in aba sai wajen abokansa, da sun yi
shiri tafiya.
A dai-dai lokacin da suka haye dawakai sai suka rufarwa
hanya babu ji babu gani. A daidai wannan Lokacin Shamsu bin
Aujarbn Abdallahi ya na hangensa daga can saman gidansa koda ya
bature
(.
>
34 Page
ga sun fita sai yayi sauri ya sakko ya nufi cikin gidan dan sanin abin
da yake faruwa.
A lokacin da Sarki Abdullahi bin Sharjas ya gama kintsawa
sun fito tare da matarsa da kuma Gimbiya Suhaila bin Ababakari da
Jarumi Ahmad. A hankali ya matsa gare shi jiki a sanyaye. “Dan
uwana naga Da na Jarumi Umar tare da abokan gumurzunsa sun
sukwani dawakai, kai kuma ka fito cikin shiri shin akwai wani abu
ne da ba mu sani ba”.
Hakimi yayi murmushi ya ce "Kwantar da hankalinka yanzu
nake shiri na shigo Bangarenka na zayyana maka abin da ke faruwa,
sai kuma g aka, Amanar mutane na iyalina, da gari na na hannunka,
domin wata tafiya ce wacce ba a kimtsa mata ba ta same mu, dole
daga yanzu za mu wuce Bahara, zan gana da Sarki akan matsalar
gimbiya Suhaila bin Ababakari, sannan Jarumi Umar da ka gani ya
fita shi ma ya tafi Shamnun ne domin magance matsalar da ikon
Allah zuwa yammaci za mu dawo"
Koda Shamsu bin Aujarya ji wannan batu sai yayi shiru da ya
fuskanci shirun nasa zai kawo wani tunani daga dan uwansa sai ya ce
"To Allah ya dawo da ku lafiya, kuma za mu ci gaba da gudanar da
tafiyar komai har Allah ya dawo da kai lafiya".
ya
Daga nan ya bi su da kallo suka dunguma kusan dakaru
ashirin ne ke musu rakiya. Bai gushe ba yana kallonsu har sai da
suka bace masa da gani sannan yayi sauri ya nufi gida, ya sa a kira
wo masa babban yaron sa Alban koda zuwa Alban sai dube shi ya
ce "Maza ka je ka tashi ka je ka isar da dan aikin Waziri cewar lallai
dan uwana ya yi abin da yake zargi wato ya nufi Bahara, shi kuma
Jarumi Umar ya nufi kasar SHamnun, ka yi maza ka da ka bata
lokaci".
Alban ya fita da hanzarinsa don kai sakon maigidansa abin
sirrinsa gatan sa kuma.
bature
B
35 Page
Shamsudden wani mashahurin tsoho ne wadda yake adawa da
mulkin dan uwansa, bai yi amana da Abdullahi bin Sharjas ba domin
gani yake shi ne mafi cancanta da sarautar Annur, don haka kullum
cikin bakin ciki da zagon kasa yake yiwa Mulkin Abdullahi bin
Sharjas tsawon shekaru bai taba samun nasara ba, Abdullahi bin
Sharjas ya sha kama shi da hada baki da wasu maha'inta kasa amma
yana masa afuwa, saboda son a zauna lafiya domin abin da Abdullahi
bin Sharjas yake fadi kullum shi ne dukkaninsu sun zama dattijai
lokacinsu kalilan ne a duniya, baya son dan uwansa ya mutu a
matsayin mai ha’intar kasa, kullum yana gyara masa kurakurensa,
amma ya gaza fahimta, don haka duk lokacin da ake so a cimma
wata manufa a cikin kauyen Annur to da shi ake hada baki, don a
jiya da waziri ya bar kauyen sai ya sa dan aike zuwa gareshi ya sanar
da shi cewar yana bukatar jin duk wani motsi da ya ga dan uwansa
yayi.
Tun da Waziri Ja'afar ya bar Kauyen Annur bai tsaya ko ina
ba sai gidansa a babban birni saboda ya san cewar za a samu wannan
babbar matsalar, don haka washe gari da sassafe ya zo fada don ya yi
tsarin da zai warware kansa daga cikin matsalar birnin Shamnun
kafin a samu wata matsala
Ana zaune a fada kowa ya iso isowa Sarki Muhammad farsi
kawai ake yi. Wasu da dama a fadar sukan tattauna batutuwan da
suka zo wa da Sarki shi na yadda za su sanar da shi, wasu kuma na
kokarin gyara Kujerar Sarki wasu na gyatta tsayuwarsu, malamai
wasu daga cikin Hakimai da aka gayyata, Sarkin Kasuwa, Sarkin
gida, da na fada Shugaban Dakarun waje da na Gida duk sun hallara
suna jiran Sarki.
Kwatsam sai ga Busar Sarewa alamar Sarki ya taho,
‘ya'yansa biyu ne suka fara shigowa cikin takama da nuna izzar
mulki wato Yazid da Abbas. A nan take kowa ya mike a fadar aka
bature
ミ
36 Page
fara dukar da kai kasa ana gaida su. Sai da suka nemi wajen zama
sannan ne kowa ya zauna kuma waje yayi shiru. Jim kadai sai ga
Sarki nan shi ma nan aka kara tashi yana tafe wasu dakaru biyu suna
biye da shi kansa a kasa yake har ya isa inda kujerar mulki take
wadan an dakaru suka koma hagu da dama suka tsaya a bayan kujera
sai ya dago kai ya dubi duk inda mutane suke sannan ya daga hannu
ya fara addu'a domin fara zaman majalisa, a ka yi salati ga manzon
rahma, aka yi kirari ga ubangijin talikai aka nemi taimakonsa da goyan bayansa a game da daukaka Kalmarsa. Sannan aka shafa da
fatiha. A sannan ne ya nemi waje ya zauna.
To fa babu mai zama a wannan wajen har a tashi taro a haka
kowa zai tsaya.
Mai rubutun kundin mulki da kuma gabatar da abin da za a
fara jira yake Sarki ya daga masa hannu ya fara domin dole shi ne
farko adaidai lokacin Sarki ya daga hannunsa sai wannan mutumin
da ake cewa da shi Zarkifilu ya fito gaban Sarki da katon kundinsa a
hannu ya fara da cewa
"Allah ya ja zamani Sarki ya karawa Sarki lafiya kamar
kullum da kodayaushe, batu daga Sarki Jarumun Jakub cewa a karo
na biyu ya