unani jarumtakarsa gani
yake shi ke sama da shi”.
9
Abin da Jarumi Jarumi Umar ya lura da shi ya dubi dan uwan
nasa ya ce "Amanar mahaifina da kuma kai kanka tana hannunka, ka
da ka yi wasarere da rayuwarku duniya ta yi mana kunci"
Kalamansa suka sanyayyar da gwiwar Ahmad a dai-dai
lokacin da Kubrat da su GImbiya Suhaila bin Ababakari suka
bature
B
31 Page
tunkaro in da suke Jarumi Jarumi Umar ya ci gaba da cewa "Ya kake
tsammanin idan wani abu ya same Baba, da kai kana tunanin
tsohuwar nan tamu mai tsananin kaunarmu zata iya dauka, a
kodayaushe ka tuna da ita ka kuma tuna da al'ummar da suka jingina
da mahaifinmu"
Jarumi Ahmad ya ji dadi sosai har ya jawo Jarumi Umar ya
rungume shi suna masu murmushi so da kauna, Ahmad y ace "Ka ji
abin da Baba ya ce tafiyarka tafi ta mu hadari da taka tsantsan, ya
kamata a ce ka kula kuma ka dawo cikin koshin lafiya domin
rashinka kamar ragewa masarautar annur karsashi ne, rayuwar
mutanen Annur sun dogara da Allah da kuma kai, kai suke yiwa
kallon mahaifinmu, don haka ka kula dau uwana".
Dukkaninsu suna murmushi na jin dadi da kuma wata
karyewar zuciya har ta sa suka zubar da kwalla,dai dai lokacin
Kubrat ta karaso da ita da Suhaila bin Ababakari. Kowa yana saurin
goge kwallar don kar mahaifiyarsu ta fuskanci kuka sukeyi, kallo
daya tayi musu ta fahimci damuwa a tattare da su, da yake ta riga da
ta san halin da ake ciki tun a daren jiya ta yi nata kukan, sai ta share
ta kasance don karfafa musu zuciya.
Jarumi Umar ya dubi Gimbiya Suhaila bin Ababakarit ta
dukar da kai "Barka da safiya”.
Ya yi mata murmushi cikin kallon cikin idonta ya ce
"Dafatan kin tashi lafiya”.
"Ku yi kokari ku shirya domin ku isa a kan lokaci,kamar
yadda mai martaba ya fada, ina muku fatan alkairi yarana Allah na
tare da ku❞
Duk su biyun suka rungume ta "Insha Allahu"
Su ka furta tsoron da take ji shi ne ta fara kuka yasa ta sake su
ta dubi Suhaila bin Ababakari “Zo mu je wajen maimartaba yana jiran ki”.
bature
32 Page
Gimbiya Suhaila bin Ababakari cikin jin nauyi ta ce "Idan
babu damuwa zan gana da Jarumi Jarumi Umar na dakika daya kacal
Jarumi Jarumi Umar ya kalle ta ya kalli mahaifiyarsa Kubrat
ya kuma dubi dan uwansa, sannan ya dawo da kansa gare ta, yayi
shiru gami da cewa "Mu je"
Ya yi gaba ita ma ta dubi Kubrat gami da murmushi sannan ta
bi bayansa a nutse sai da ya bada tazara mai yawa sannan ya tsaya,
ya tsaya dai-dai inda abokansa suke zaune don haka suka tsira masa
ido sanin halinsu yasa ya fara kame kame ya dube ta ya ce "Ko zaki
bani dan lokaci zan Jarumi Umarci abokai na don su je su yi shiri
domin tafiya Shamnun”
Ba tare da ta ce komai ba ta jinjina kai alamar ta fahimci
uzurinsa".
Ta tsaya ta zuba wa bayansa idanu yana nufi wajensu kafin
yana isa suka amsa masa sallamar da yayi musu cikin zolaya yakalle
su daya bayan daya ganin idanuwansu suna kan Gimbiya Suhaila bin
Ababakari sai ya juya ya dube ta itama idanuwanta a kansu yake tana
mai mamakin kallon da suke yi mata. Ya dawo da dubansa gare su y
ace “Wai me ye haka kukeyi, komai wane abu yana da gurbi kar ko
dora giwa a kan dantsako".
Dawan ne mutum mafi maida hankali a cikinsu don haka shi
ko dariya ma bai fiya yi ba, babban burin Dawan ya ga ana batun
tafiya don aikin Allah don haka shi ya fara dakatar da su da cewa
"Me ke tafe da kai?"
Nan ne ya daina harararsu ya dubi Dawan y ace "Mu na da
babban aiki a gabanmu, ku je ku shirya yanzu za mu tashi zuwa
Shamnun don fara ni ma zan gama da gimbiya ne na tafi nawa shirin
watakilatana da sako ne yasa take son mu yi Magana"
Mu'az ya ce "Kowane lokaci a shirye muke ka je ka gama
muna jiranka a wajen dawakai"
bature
bature
B
33 | Page
Kubait kuma ya ce "A gaida gimbya"
Bai saurare shi ba ya juya ya koma ga Gimbiya Suhaila bin
Ababakari ya tsaya tana kallonsa sai da ya dan tsaya ya ga ta ki
Magana sannan y ace "Ina sauraren ki❞
Ta gyara murya ta ce "Dama na so na sanar da kai ne inda
yayana ya sanar da ni yana boye ko zaka taimaka ka ceto shi daga
zalunci dan uwansa?”
Ta fada cikin rudu da sunkui da kai kasa ya dan yi shiru ya
dago ya kalle ta "Ki kwantar da hankalinki Gimbiya, babu wani abu
da zai sami dan uwanki Salma, kuma da yaddar Allah Salman zai
zama Sarki in dai shi ne zababben mahaifinku, wannan alkawarin
Allah ne, domin na tabbata matukar mahaifina ya tattauna da Sarki
Muhammad farsi, ni kuma isa birnin ku, na kuma kai sako na, babu
wani taurin zuciya da zai saka Dan uwanki ya yiwa Sarki gardama
domin ya san ba zai taba yin nasara ba, don haka ki kwantar da
hankalin ki Gimbiya".
Ta yi wani murmushi jin dadi ta ce "Insha Allah, kuma na
gode bisa taimakon da ka yi min a jiya na kara gode maka bisa
wannan taimakon da z aka kara yi min, ina maka fatan dawowa cikin
koshin lafiya".
Shi ma ya dan yi guntun murmushi gami da cewa "Amin, y
ace za mu hau hanya Allah sa mu dawo da mu same ku lafiya”.
Daga gama wannan maganar sai ya juya ya bi hanyar
bangaren Maza na gida y