rninsa amma dole tasa
ya tsaya saboda a kowane lokaci ana koyar da su da su bi musulmi
domin su samo lagon da za su kama su da sasari.'
bature
Data
28 Page
su kashe shi shi ne ya sa a wannan lokacin ba ni da wani sukuni tun
da Sarki ya fara ciwo yau gobe lafiya gabana ki faduwa".
Hindu ta yi shiru cikin dan gajeren lokaci har sai da ta ji uwar
dakin nata ta share hawayen ta ja shessheka sannan ta ce "Neman
taimakon Hakimin Annur daidai ne a gare ki, domin shi mutum ne
adali kuma mai matukar son gaskiya, idan Allah zai baka kariya ba
da kansa zai zo ya baka kariya ba, amma shi ne zai zama sanadin
haka, kin fi ni sani duk wani ilimi a wajen kin a samo shi, tsantsaini
da tsoron fadawa halaka yake sawa kike wannan tunanin ai saka miki
damuwar da kuma tunanin nemo wadda zai tsayawa danki ki dauka
ubangiji ne yake haska miki, a da can ban da karfin gwiwa a game da
Yarima Abbas amma wannan maganar take ta sa na fara jin karfin
gwiwa, tabbas mu yi hanzari ka da mu yi kasa a gwiwa”.
"Maganar ki gaskiya ce, wannan haka yake, to amma yake
Hindu ya kike gani za mu yi wajen ganawa da Hakimi Abdullahi bin
SHarjasllah, ki sani cewar matukar sun san wani shiri to za su gyara
na su shirin, abin da nake tunani wani amintacce za ki nemo min
wadda zai kai masa ziyara wadda shi da kansa Hakimi zai nemi
yarima ni kuma zan gayawa yarima sakon da zai je masa da shi”.
**
Lokacin da Jarumi Umar ya iso babban turakar mahaifinsa, a
daidai lokacin Hakimi na nazari game da bakuwar Suhaila bin
Ababakari da kuma tunanin sakon da Sarauniya Hauletu ta zo masa
da shi na son haduwa da Yarima Abbas.
A wannan lokacin ya yanke kai ziyara babban birnin domin
ganawa ta musamman da Sarki a game da sabuwar masarautar da ake
rigima a kai, sannan kuma zai yi amfani da wannan dama ya gana
Yarima Abbas.
da
29 | Page
Ya dubi 'ya'yansa biyu da suke durkushea gabansa ya fara da
cewa "Ya kai Ahmad ina son kasani za mu yi tafiya a safiyar yau
zuwa birnin Bahara, kai za ka yi min rakiya zuwa can".
Ya dubi Yarima Jarumi Umar da yake a tsorace daga furucin
Hakimi, domin idan akwai abin da yaki jini ya ji ko gani mahaifinaa
y acc zai yi tafiya ba tare da shi ba. "Ya mai martaba ka yi sani cewa
zuciyata tana shiga rudani hankalina baya kwanciya a duk lokacin da
na ji cewa za ka fita daga cikin wannan kauye, Ya mahaifina ka sani
cewar makiyan da suke son ganin bayanka a kasar nan sun fi
makiyan waje yawa, idan har za ka kai...."
Hakimi ya dakatar da shi da cewa "Ka kwantar da hankalinka
Jarumi Umar, ka sani cewa wani muhimmin aiki ne ya taso wadda
kuma yana bukatar na motsa, kai ma kumana tura ka wani aiki na
daban aikin suna bukatar a yi su a tare domin dole ne na je na gana
da Sarki Muhammad farsi dangane da matsalar Salman da Hilal, dole
kai ne zaka tafi izuwa kasar Shamnun domin ka gano mana halin da
ake ciki"
Ran Ahmad ya baci ya dubi Jarumi Umar ya cc "Akowane
lokaci kana jin cewar kai kadai ne kariya ga ahalin gidan nan, idan
har ba zan iya kare mahaifina ba, na tabbata ba zai yanke shawarar
tafiya da ni ba".
Jarumi Umar ya girgiza kai yace "Ba haka nake nufi ba dan
uwana, babu mai kare wa face ubangijin musulunci, abin da nake
tsoro da fargaba shi ne buguwar zuciya yayin da na tuno kuna halin
tunkarar birnin da yake cushe da makiyanmu, masu son ganin bayan
mahaifinmu da ahlinsa".
Hakimi yayi murmushi ya dubi Ahmad y ace "Iya abin da
dan uwanka ya fada shi ne kadai abin da yake gudu, amma ba ya
nufin cewar kai ba zaka iya bani kariya ba."
bature
30 Page
Sannan ya dubi Yarima Jarumi Umar ya ce "Aikin dake
gabanka ya fi wanda ke gaban mu hadari, dole sai kun yi kaffa kaffa
domin na san za a zuba dakarun da zasu hana ku ganawa da Sarki
Hilal, domin ba bukatarsu a yi sasanci ba bukatarsu ayi tashin
hankali a tsakanin kasashen musulmai, amma a zarar kayi tozali da
Sarki Hilal ka yi masa albishir da cewa na tafi zuwa babban Birni
don tabbatar da cewar shin Sarki ya san da abin da yake faruwa a
kasar Shamnun ko kuma bai sani ba, wannan kalamin shi ne kadai
zai sa Sarki Hilalya barku ku dawo gida lafiya, kuma idan yana da
hankali shi zai sa a barwa duniyar musulunci zabar Sarki mafi daraja
a tsakaninsu shi da dan uwansa Salman, amma matukar basu gan ku
kun gana ba, to ku yi kokari tsirar da rayuwarku domin sun shirya ayi
duk abin da za a yi, ka ga ke nan za su fara da kai”.
Jarumi Jarumi Umar ya jinjina kai ya kuma fuskanci lallai
akwai babban aiki a gabansu,don haka ya jinjina kai ya ce “Insha
Allahu komai zai tafi kamar yadda ka tsara Baba".
Hakimiya jinjina kai gami da cewa "Masha Allahu, yanzu ka
je ka yi shiri tun da har yanzu muna cikin duku-dukun safiya, don
haka idan kun tafi yanzu kafin la'asar za ku isa birnin Shamnun,
kuma lokacin mun fara neman hanyar dawowa daga Birni, duk ku
tashi ku je ku yi shiri".
Ahmad da Jarumi Umar suka fito daga babbar turakar
mahaifinsu cikin fushi da Ahmad yake ciki da dan uwansa domin shi
sam gani yake kanin nasa ya raina masa t