NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 42

i haushin bakar magar da yayi masa cikin fara'a ya cc "Har nawa ne?" Daya bayan daya ya fadi farashin mu, duk da kudin sun yi ya kalli abokin tafiyarsa ya ce "Ka biya shi kudinsu” yawa saiWannan mutumin ya dubi Hakimi Abdullahi bin Sharjas a tsora ce ya ce "Ya kai dan uwana kana hauka ne, idan muka sayi bayin nan da wadanan nan kudin dukkanin kudin mu sun kare, ga shi ba za mu kara dawowa kasuwa mu sayar da amfanin mu ba, har sai bayan sati, wannan ba karamar barazana bace ga rayuwar mu da iyalin mu". “Ya dube shi ya ce “Ka biya su na ce da kai, Allah da ya halicce mu, shi ya hore mu da kyautatawa da abin da muke da shi, yayi alkawarin ninka mana, na ji tausayin matan nan kuma ina saka rai Allah zai ninka mana a nan gaba" Haka kuwa a ka yi ya saye mu ya kawo mu gidansa ya ba mu Kalmar shahada muka amsa matansa suka koyar da mu addini. In takaice miki a kwana biyu wani Sarki ya kawo ziyarsa a cikin mu Sarkin ya sayi bayi guda biyu, dukiyar da Hakimi ya samu duk da ya rangwantawa Sarkin akan yadda ya biya shi domin ba ciniki aka yi ba kawai y ace In an sayar masa zai bada ninkin biyar na yadda aka saye su, a su kadai sun dawo da dukiyar da Hakimi ya saye mu, kafin Sarki Muhammad farsi ya zo da tawagarsa don ziyarar Hakimi a halinsu na dawo daga tafiya ya biya kudin mu uku shi ma kuma ninkawar yayi kamar yadda waccan yayi,a duk da Hakimi ya so ya bada mu kyauta, amma Sarki Muhammad farsi ya ce ya kara ninka kudin. bature 26 Page 27 Page A zaman da nayi a cikin ahlinsa na so ace na ci gaba da zama da su, domin tun daga ranar da suka fahimci ya amshi addinin musulunci da gaske sai suka kasance da ni cikin kulawa a dan kwanaki da nayi mun saba sosai har sai da nayi kukan rabuwa da su. Yau shekara goma ke nan kin ji ta inda na san adalci da tausayi irin na Hakimi Abdullahi bin Sharjas, mutumci da karamci kuma ga iyalansa". Koda sarauniya Hauletu ta ji wannan batu daga bakin Hindu sai ta yi shiru tana nazari a cikin ranta daga bisani ta ce "Akwai babban matsala a cikin gidan nan yake aminiyar sirrina, ki yi sani cewa dana na cikin barazana da rayuwarsa akowane lokaci har maina jin tsoron, tsoro yana kamani yana hanani sukuni a duk lokacin da na kasance cikin wannan yanayi nakan dage karanta (LAHAULA WALAKUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZIM) domin danganta komai wajen ubangijin talikai, a kwana kusa zuciyata tana gaya min, dole na nemi taimako daga wasu manyan mutane da Sarki yake basu daraja, domin su kulamin da yaro na". Ta yi shiru a daidai wannan lokaci daga bisani ta dora "Babana yana cewa a duk halin da ka kasance ka da ka nemi taimakon kowa ka nemi taimakon Allah, amma kullum zuciya tana gaya min in nemi wani na bashi amanar dana Yarima Abbas da a yanzu ya kai kimanin shekaru a shirin da haihuwa tabbas zai zamo abokin gogaggayar Yarima Yazid na ganin yardarsu a wajen manyan kasa, a wannan lokacin, saboda makirci kina ganin yadda ba a bar Yarima Abbas ya saba da koda shugaban dakarun gidan nan ba, bare har ga ya saba ga Shugaban Dakarun kasa, bai taba kai ziyara Sansanin Dakaru ba, bare har a fara tunanin gwada shi a matsayin magajin Sarki, kamar yadda kika sani ni ma na sani, babu yadda za a yi a rashin adalcin da kirki irin na Abokan zamana Yarima Yazid ya zama sarki su kyale min dana a raye, dole sai sun kirkiri hanyar da za bature 13 Page Bahara, akwai dakaru a ko ina, sai dai duk tsaron bai hana birnin ya zama mahadar Kafurai wajen shirya tuggun yadda za su kawo karshen brnin da musulmai. A cikin kasuwa mafi daraja a kasar Bahara wacce ake mata lakabi SUKUL SA'A wasu gungun Kirista, shugabansu JARFIS na tafe yana duba kayan da aka kasa a kasuwa, yana duba wa wadanda suka yi masa yana siya tsawon lokaci yana cikin wannan lamari da dakaru a bayansa har suka isa wani babban shagon wani tsohon da ake kira Kirzalu, Kirzalu asalin dan kasar Bahara ne wadda jinin kasar ne shi wadda kuma ya rudu da dukiya saboda yana zaune ne domin ya zama idon Kafurai da duk wani abu dake faruwa, kuma a nan ne suke kitsa shirinsu na zalunci. Babban shago ne da shi. Dai-dai inda Jarfis ya iso sai ya fara kamar duba kaya da haka ya shige cikin shagon dakarunsa suka tsaitsaya a bakin shagon ko da shigarsa sai suka nufi wani guri da ba zaka taɓa tsammanin kofa bace amma Kirzalu yana dafa ta sai ya murza wani mabudi take kofar ta bude kawai sai suka shege ciki tare, koda shigar su ciki sai ga su a cikin wani kayataccen ɗaki mai dauke da kujerun zama da matasai a ɗaya cikin matasai wani hamshakin mutum ne zaune a gabansa akwai kayan marmari yana zaune yana dauka daya bayan daya yana tauna inibi, batare da ya daga kai ya kalli wadda yake shigowa ba. Har Jarfis ya nemi wajen zama zai zauna sai wannan hamshakin mutumin ya daka masa tsawa gami da dagowa ya dube shi "Waye kai da har zaka same ni a zaune ba tare da na yi maka izini ba ka nemi wajen zama, maza ta shi ko takobi na ta raba kanka da gangar jikinka" Jarfis ransa ya baci kamar yaki bin uma
🏠