ta lumshe
idanta tana shafa dan gashinta, da gaba
daya tattalin arzikinta yake karewa
akansa tai wani wal da idanunta ta ce.
"Daga wa kuwa? In ba daga
Hubbina ba."
Hadiya ta ce, "Gaskiya ya burgeki
da waya, ana ji da wannan Salim din."
Jana ta ce, "Wallahi kuwa ai duk
cikin samarina babu wanda nake so
kamarsa, wallahi Hadiya in har narasa shi
ban san yadda zanyi ba na san sonsa
IZGILI JAMILA MUHAMMED
mahadin rayuwata ne kin ga in bashi ba
babu rayuwa."
Nan da nan Idanu Jana suka kawo
kwalla ta ci gaba "Har tsoro zuciyata take
bani ganin irin son da take masa ina
sansa har ban san yadda zan kwatanta
miki ba, jiya da ya zo tamkar zai yi kuka
yake gaya min babanshi ya zaɓa
mata 'yar abokin babansa wallahi tun
jiyan har yanzu bana cikin nutsuwa
hankalina a tashe yake dan idan narasa
shi komai yana iya faruwa."
."
masa
Sai hawaye ya wanke mata fuska
tamkar an bude famfo.
Hadiya ta ji waii matsanancin
tausayinta ya kamata, ita dai bata san so
ba dan bata taɓa jinsa ba amma zama da
Jana sarkin soyayya yasa ta fara fahintar
so, abu ne mai dadi amma idan an dace
kuma mai mutukar hadari idan anyi
IZGILI JAMILA MUHAMMED
rashin dace ta koma fahintar rabaka da
abin son ka ba karamin tashin hankali
bane.
Ta matsa a hankali ta dafa kafadar
Jana da take ta sharɓar kuka ji take
tamkar ta tayata, ita ma kwallar ta tarar
mata ta dai daure dan kada ta kara
dagawa Janar hankali ta ce.
"Dan Allah Jana ki dinga daukan
lamarin da sauki kuka ko tunani ba zasu
yi miki magani ba ki dage da addu'a a
yanzu ita ce magani in dai Salim mijin ki
ne to fa labudda sai kin aure shi, idan
kuma ba mijinki bane Allah yasa hakan
shi ne mafi alkhairi kin ji dan Allah Jana
ki sassautawa kanki dan kada ki saka
kanki a wata matsala.
Jana ta ce, "Na ji in Allah ya yarda
zan dage da addu'a har mu ga abinda
Allah zai yi."
t
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Hadiya ta yi dariya ta cc, “Ko ke fa
my sister tayi dariya.
Ya yi nisa cikin tunaninsa har bai ji
abinda uwar gida sarautar matan take fadi
ba, ta shafa fuskarsa ta ce, “Wai ni Alhaji
me ke damunka kwana biyu, duk ka
canjamin kana yawan zama shiru kana
dogon tunanin har baka jin me ake cewa
dan Allah idan wani abunene yake
damunka ka tai maka ka gayamin dan
wallahi idan baka gaya min ba ni ma
zaka sani a wani hali.”
Alhaji Mansir Kwangila ya sauke
ajiyar zuciya ya ce, "Babu abinda yake
damuna Zalifa kawai dai ina wani ɗan
nazari ne amma karki saka komai a
ranki."
Ta kalle shi kawai sai kuma ta mike
da sauri zata bar falon, ya yi saurin
IZGILI JAMILA MUHAMMED
janyota da karfi ta fado jikinsa please
Zalifa baki yarda da abinda nace ba ko, to
ki kwantarmin da hankalinki ba wani abin
tashin hankali bane amma ba zan gaya
miki shi yanzu ba sai dai na miki
alkawari da zarar na gama bincike zaki ji
komai."
Ta yi sauri sauke ajiyar zuciya ta ce,
"To Allah ya mu ji alheri.'
"
Ya ce "Alherin ma za ku ji”
Ta ce, "Shi muke fatan ji a duk inda
muke"
Ya ce, "To yanzu hankalinki sai ya
kwanta da har za ai min fushi dan kawai
ki sani a uku.”
"
Ta saki wata irin dariya mai kara
mata kyau ta ce, "To Ai ban ji dalilin
sauyawartaka ba a 'yan kwanan kin nan
ka ga kuwa hankalin nawa bai kwanta ba
zai dai kwanta.
37
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Ya ce, "Tun da na ce zan gaya miki
to zan gaya miki da zarar lokaci ya yi ta
cc, "Allah ya nuna mana lokacin nan. "
Ya ce, "Amin"
Ta ce, "To ta so mu je dinning dan
abinci ya dade da kammaluwa kai kawai
yake jira."
Ya mika mata hannunsa wai ta
tashe shi ta ce, “Kaima kasan ba zan iya
ba in ba so kake ai haihuwar guzuma ba
ɗa kwance uwa kwance yadda kake
ɗinnan kace in dɗaga ka, kai ma kasan ba
zan iya ba."
Ya tashi yana dariya ya ce,
"Laifinwa bake kike dirkamin abincin da
zan karuba na zata santi kike tun da banji
kina complai din ina sakar miki nauyi ba,
ya karashe maganar yana daga mata gira.
Ta yi dariya tana faɗin Alhaji Kafa
girma."
38
IZGILI
WHY JAMILA MUHAMMED
Ya ce, To bara in gama cin abinci
sai ki yi bayanin girman da na yi."
Suka yi dariya.
****
Yau kimanin sati uku ke nan yana
yin zuwa na musamman domin ya san
shin ita din wacece so yake ya wani abu
game da ita yana so ya san gidansu,
amma shiru kake ji babu ita babu
labarinta jiya akan idansa aka shiga
makarantartasu kuma yana nan aka ta shi
ya dinga baza ido ko zai ganta amma
komai irin hijabinta bai gani ba, gaba
daya kansa ya dau chaji to me yasa bata
zuwa makarantar a yan kwanakin nan ya
rasa wanda zai tanbaya labarinta to yau
din ma haka ya gama zagayanshi daga
farkon titi na koki har karshensa, amma
duka baba dantela dva va shiga
damuwa.
IZGILI JAMILA MUHAMMED
To ko dai alhaji umar zai samu ne
akan maganar gaskiya yana san sanin
wani abu daya danganceta dai-dai nan ya
ji wayarsa tana ringin ya dauka Alhaji
Umar ne ya dauka bayan sun gaisa ya ce,
"Kamar kasan yanzu nake tunanin
kiranka sai kuma ga shi ka ri gani alhaji
Umar mai akwai ya yi dariya ya ce,
"Daman