ILI JAMILA MUHAMMED
Ta gangara inda Jana take suka jera
zuwa titi Anty Meena yayar Jana ce uwa
daya uba daya ita cc a biyu a gidansu
tana aure a Yalwa bata taɓa haihuwa ba.
Jana suna tsaye abakin titin,suna
jiran adai-daita sahu kasancewar duk
wanda ya taho zaka same shi da mutane
saboda yamma ta yi tun daga nesa ya
hangota ya ganeta ita ce zuciyarshi ta
gaya masa ya tsura musu ido yau ma dai
irin shigar da ya ganta da ita ce sai dai
wannan ba hijabin Islamiyar bane shi
wannan kalarsa maron ne kalar flat din
takalminta ne kuma sanye take da Nikaf
dinta babu abinda kake gani sai kafarta
kasancewar Hijabin dogo ne sosai.
Idonsa ya kai ga wadda take kusa da
ita ya kalleta yaga irin shigar da ta yi
gaskiya ya yaba da nutsuwarta da
hankalinta yana. kallo sai tsaida abin hawa
27
IZGILI JAMILA MUHAMMED
suke amma ba su samu ba ya wuce ta
gabansu yana ci gaba da fadin kamun
kanta to shi dai duk ganin da yake yi
mata cikin nutsuwa yake ganinta bai ma
taɓa ganin fuskarta bato me yasa ya ji
wannan samarin suna fada mata wani
suna wai kanti ya juya baya mai hakan ke
nufi? Wata zuciyar ta ce, masa kawai dan
sunga ba kalarsu bace shi yasa suke jin
haushinta har suke Igaya mata wani suna
haka ya dinga tunani harya isa gida.
**
.
Hadiya tana sharar tsakar gida ta ji
sallamar babbar kawarta tata Jana. Jana
kawar Hadiya ce tun suna yara sun yi
mutukar shakuwa ta yadda babu wadda
za tai kwana biyu batare da ta nemi 'yar
uwarta ba duk da babu ta yanda za ai su
hadu batare da sun kafsa ba anan dai na
yi musu da maganar Malam bahaushe da
28
IZGILI JAMILA MUHAMMED
ya ce, sai hali yazo daya ake abota to
waɗannan aminan junan su sam ba haka
bane dan ko wace da inda ta dosa inda
hakan halaiyace inda Jana ta kasance mai
san gayu da kece raini tana da rawar kai
mutuka ga saurin fushi amma bata da
wuyar saukowa.
Tana da kirki bata kuma da kyashi
ko hassada ita in dai dan uwanta ya samu
to ji take tamkar ita ta samu sannan bata
da rufi duk abinda ya dameta kai tsaye
zata gayawa babbar aminiyarta bban
abinda yasa suke samun matsala da
kawartata shine ita dai Jana Allah ya yo
ta mai san saka kananun dinkuna ce
kuma idan tasa ba zata sami mayafi mai
yalwa ta rufe jikinta ba, sai dai irin na
'yammatan zamani ita tana jin bakin ciki
ganin yadda kullum Hadiya take faman
jibgawa jikinta dogayan hijab har da su
29
IZGILI JAMILA MUHAMMED
nikaf, sai kace a zamanin jahiliya ga dai
kyau dan asali kyau zalla amma bashi da
amfani tunda kullum ana rufcwa masu so
basu gani ba bare su yi sha'awa yayinda
Hadiya tata kasance kasance. marasan magana
sannan bata san raini ko wulakancin sam
bata da saurin fushi amma kuma bata da
wuyar saukowa tana da shagaɓa mutuka
da sangarta in dai a gaban Abbunta ne da
Innarta tana da tausayi ita abu kankani sai
ya sata kuka shi yasa Jana take ce mata
mai arhar hawaye, ita abu kaɗan sai ya
sata kuka.
Ta dago da sauri tana dariya Jana ta
kalleta ta dauke kanta ta karasa gefen
tabarman dake shinfide suna gaisawa da
Inna Hadiya tana sharar tana dariya dan ta
san lefinta ta san kuma shi yasa Jana ta zo
tana karasa sharar ta wanke hannuwanta
30
IZGILI JAMILA MUHAMMED.
ta karaso kusa da ita tana fadin "Kawata
ya dai.?"
Tana dauke kanta Hadiya ta guntse
dariyar da ta cika mata ciki ta ce, "To ta
so mu shiga ciki sai ingaya miki uzurina
da abinda yasa ban aiko miki da wuri ba."
Jana ta bita ɗakinsu ta zauna kan
'yar yalolowar katifar Hadiya wadda
saboda sidewa ta dawo tamkar tabarma,
ta kalleta ta ce, "Uhm Ina jinki faɗa min
dalilin da yasa da kika san ba zaki je ba
me yasa baki aiko min da wuri ba.?"
Hadiya ta zauna kusa da ita ta ce,
"Ai ya kawata ni ma ba haka na so ba na
san Bilkisu Ibrahim ba zata ji dadi ba,
babu daya daga cikin mu daya je."
Jana ta harareta ta ce, "Waya ja?
Idan bake ba da kika san ba za ki je
waliman nan ba tunda wuri ba sai ki
aikomin ba in sami abokin tafiya kawai
31
IZGILI JAMILA MUHAMMED
sai dana shirya ina ta jiranki sannan zaki
wani ce min Inna bata nan, shi yasa ni ma
Faina ya ɓaci kawai nace to nima na fasa
zuwa.
"
Hadiya ta ce, "Haba sister me yasa
kika fasa ai Amiru ɗazu ya gayamin dana
ce ya je ya gaya miki ki bani kayan
walimar ya ce ke ma ba ki je ba.
Jana tana faɗin ‘yar rainin hankali
bayan sai da kika bari duk 'yan tafiyar
sụn tafi sannan kika wani aikomin ai na ji
haushinki sai kuma daga baya na ji
daɗima da bamu je ba.
Hadiya ta ce, "Saboda me? Yanda
kika kwallafa ranki akan walimar nan. "
Jana ta tura mata wata leda da ta
ganta da ita ta ce, "Bisket da chacolate
din nan, na Bintu ne da Aliyu shi kuma
túraren naki ne.
32
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Sannan ta ɗauki post din ta ta ajiye
"ta a kusa da ita ta bude ta fito da wata
dalleliyar waya mai shegen kyau daga
gani kuma zatai dan karan tsada sabida
haduwarta, Nokia ce gaskiya ta hadu.
Hadiya ta ce, "Gaskiya mutuniyata
wannan wayar ta hadu karshe. Kuma
daga wa?"
Jana tana daga kwance sai