na masu
yi suyi."
Hadiya ta ce, "Yanzu duk wannan
baza eye shadow da wannan jam bakin da
kika gabza ba ki yi minti sha biyar kina yi
ba, ai ban miki magana ba, to sanin ki da
nayi naga ko kin gama fentefenten naki
ba gama kwalliyar bace dan sai ki kara
20
IZGILI JAMILA MUHAMMED PROSTY
wani minti sha biyar din kawai kina
kallon madubi kina kara baza powder ja
na ta ajiye sosan da take shafa powder ta
kara gyara zaman ɗaurin ɗankwalinta ta
ce, "To da zaki ishe ni da Ina ta shafa
powder ca nake ke ma kin shafa ko ke
naki ba sai ni zaki hurawa wuta.'
"
baki gaAnty Meena ta shigo tana fadin ita
ai shafawar masu hankali ta yi ba irin taki
ba da sai a kusan karar da ita ashafawa
daya, ke in dai zakiyi kwalliya sai ki
shafa powder wajen sau goma. "
Jana ta cuno baki tana kunkuni ita
kuwa Hadiya dariya take mota ta ɗauki
Hijabinta ta saka gami da ɗaura nikaf
dinta ta ce, "To fi'ili madi ai sai mu tafi
ko?'
Jana ta kalleta wani takaicinta ya
kamata tace dan Allah dubeta haka kawai
kisa kanki a Uku ki dinga yawo cikin
21
IZGILI JAMILA MUHAMMED
wannen zirmemen Hijah ki wani rufe
fuska ke ba matar Liman ba zafi duk ya
damc ki, dan Allah dubeki duba kayan
dake jikin ki Hadiya tai saurin daga Nikaf
dinta tana kallon Jana ta ce "Mc kayan
nawa su ka yi.?"
Jana ta ce, "Riga da siket ne ajikinki
sun yi miki bala'in kyau sun yi cif-cif a
jikinki tamkar ajikinki a ka dinka su
saboda kyan da kayan su kai miki amma
zaki kassara rayuwarki ki rufewa mutane,
to ba a haka bane zaka samu mai son ka
wanda zai ganka ya ga ka yi masa amma
ke kullum zurum-zurum cikin hijab har
da su nikaf shi yasa har yanzu baki da
saurayi ko daya, to yaushe mutum zai ce
yana sanki alhalin bai ga abinda yai masa
a jikinki ba bare ya ce, yana son ki.
Ta cije gefen danyatsanta ta ce,
"Wayyo Allah garin dadina nesa in ji
22
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Angulu da ta lefa masai ai wallahi da ni
Allah ya bawa farin ki gashinki, dirinki
idanunki muryarki, wallahi ba karamin
yaki zan yi ba don sai na saka samari
runtsċ ido sai na daga musu ganye da duk
wankan da nai sai na sumar da samari
warwas Allah yai miki kira ba ta Allah
Sarki ba ya yi miki halitta ba wadda miji
zai ce shiga daka na yi ba, Amma kina
cutar da masu sanki ni na tabbatar ko sau
daya kika cire Hijab din nan da wannan
Nikaf din na tabbatar sai kin saka maza
karo."
Anty Meena ta kaiwa bakin Jana
duka ta ce, "To taki yin yadda kike so ke
ganin fito da tsiraici waje shine wayewa
to wallahi ba wayewa bace, sai ci baya
wanne namijin ne kin gama tallar Nono
da kugu awaje zai kwashe ki sai kace
mara mafadi to bara in baki misali ke ce
23
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kika ga a titi ana sai da cincin ga wani
abude kura da iska duk sun koɗashi ga
kuma wani a cikin glass a rufe sai mai
cincin zai baki nawajen nan wanda
saboda kura da ta badeshi har ya fara
canja kamannin shi, "Ai na san babu ta
yanda za'ayi ki yarda ya baki
wannanAlhalin kina ganin yarda yake sai
dai ki ce na rufen nan kike so, saboda yafi
mutunci to haka ma maza suke kallan duk
wata mace mai bayyanar da jikinta mazan
titi suna gani haka suke kallanta tamkar
wannan buɗaddan cincin din da dattin
duniya ya gama badeshi..
Hattara dai mata masu irin wannan
hali masu gani cinyewarke nan to wallahi
ci baya ne ba cinyewa bane bar ganin a
nayi miki layi a gidan ku dan kina irin
wannan shigar to ina mai tabbatar miki
duk cikin masu zuwą gun naki babu
24
IZGILI JAMILA MUHAMMED
wanda yake zuwa da zummar aure sai
dai da niyar wata bukata ta shi, kuma da
bukatarsa tabiya ba zai kara ko kallon
inda kike ba to talla ki kai shi kuma ya
taya kika sallama to kin ga kuwa taya zai
kai ki gidansa harki zama uwar ‘ya'yansa,
ke ma kin san (Impossible)
Jana ta dauki ɗan yalolon
mayafinta daya dace da atamfar jikinta
da akaiwa dinkin riga da siket sun kamata
dan-dam ta dauko post dinta ita ma kalar
kayanta. Ta ce, "Sai mu tafi Sayyada."
Anty Meena ta ce, “Ko baki faɗa ba
mutane zasu fada su ce ita din Sayyada
ce ke ko kunyar jerowa da ita baki ji ba,
ita ta yi shigarta ta kirki mutum duk na
cinsa ba zai ga ko ina nata ba, amma ke
dubeki dan Allah wallahi Jana ki yiwa
kanki faɗa, ki yi koyi da Hadiya ki dinga
komai na ki da nutsuwa."
25
e.
2
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Jana ta figi ledar da Anty Meena ta
shigo musu da ita, turaren wuta ne da
Humra da take siyar da su ta basu turaren
wutar ta kaiwa Iya mahaifiyarsu da kuma
Inna mahaifiyar Hadiya Humrar ta suce ta
basu sannan ta mikawa Hadiya dari biyu
ta ce su hau adaidaita sahu.
Hadiya ta ce, "Wallahi ki barshi
Anty muna da kudin Mota."
Anty Menna ta dan zare mata ido ta
ce, "Karбi mana ai na san kuna da kudin
motar na baku.”
Hadiya kasancewarta mai da'a
kuma ba a ai musu tarbiyar jayayya dana
gaba, yasa ta karɓa tai mata godiya ta
rakota har soro. A kokafar suka ga Jana ta
cuge tana ta faman kumbure-kumbure.
Anty Meena ta ce, "Ku gaishesu."
Hadiya ta ce, "Za su ji."
26
IZG