NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 22

i dai in bude tsarabar nan in raba kowa ya dauka 13 IZGILI JAMILA MUHAMMED dan naga dattijo na ya kagara kowa ya ci ko ba haka ba." Ya ce, "Hakanne Abbu su ka kuma yin dariya." " Malam Usman ya kalli Hadiya ya ce, "Zo ki dauka ki wanke. Ta ce, "To" Cikin nutsuwarta ta dauki ledar daya tureta gefe ta dauko wata 'yar madaidaiciyar roba ta juye abin dake ciki mangwaro nene lafiyayyo lafiyayyo masu kyau manya manya. Ta wanke su tas sannan ta kawowa Innarsu dan ta san ita zata raba dai dai nan Bintu tai sallama ta shigo mallam ya kalleta ya juyo da kallonsa ga Innar da take raban Mangwaron ya ce. "Wai shin Lariya bansa dokar fitar yaran nan waje ba, In dai fitar ta wuce cikin wuce wannan lokacin. 14 IZGILI JAMILA MUHAMMED Cikin tsananin ladabin Innar har da dan dukawarta daga kan kujera ‘yar tsugunne da take kai ta ce, "Ka fada.?" Ya ce, "To to raina ni a kafara yi da zance bana san abu ayi sanin kanki ne babu abinda natsana irin a dinga barin yara mata suna kaiwa magriba a waje, har nake kafa miki misali da cewar ko aike ne in har magriba ta sawo jiki to ki dinga hakura har na dawo ni sai in je, shi ma dattijo sai da nai masa faɗa, da har na same shi a waje yana wasa ke kuma babu ruwanki da kisa ayi kiransa ya dawo gida tun da yamma ta yi ko.?" Inna Lariya cikin ladabi gami da kwantar da harshe ta ce, “Ka yi hakuri Malam dan Allah Allah ya huci zuciyarka wallahi dole ce ta sa na aiketa kuma bama ta da lafiya ba, gidan babansu na aiketa dan dazu Iya Saude ta aiko min 15 IZGILI JAMILA MUHAMMED idan nadaka garafuni in bata to nai duban duniyar nan ban gan shiba sai bayan ɗan aiken ya tafi sannan na ganshi dan sai da na caje ɗakina sosai to shi ne da suka ta so Islamiya na ce tai maza ta dawo amma dan Allah ka yi hakuri insha Allahu haka ba zata kuma faruwa ba, ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Allah yasa." Ta yi saurin cewa "Amin" Tai wa Abbu Sannu da zuwa sannan ta mika ledar da Iya ta aikota ta kawowa Innarta su Innar ta bude taga curin fura ne da kuma nono mai kyau ta ɗaure ta kalli Malam ta ce, "Yau shi kenan ba za a ci irin tuwan nawa ba dan ga shi nan iya tayi maka haji da Umra." Malam Usman ya saki dariya ya ce, "Lallai kuwa yau tuwanki ko kallo bai ishe ni ba dan haka yi maza ki dama min 16 " * IZGILI JAMILA MUHAMMED kafin in dawo daga masallaci dan ga kira nan a na yi." Yana gama maganar ya karɓi butar da Hadiya ta miko masa ya fara alwala su ma gaba daya suka mike dan bada farali Aliyu auta ne yai zaune yaki ta shi. Inna ta ce, "Ya dai dattijo.?' Ya ce, "Inna mangwaro." Nan tai dariya ta ce, "Kayi sallar mana tukunna ko kaga nace su dauka kai kuma na hanaka.” " Ya mike da sauri damin yabi Abbansu masallaci dan in dai bai je ba zai iya cewa kada a bashi mangwaron tun da bai bi jam'i ba. **** Yau ma kamar ganin da yai mata kwanakin baya sai dai yau tana rungume da alkur'ani ta zo ta wuce ta gabansa cikin nutsuwar nan tata ya rakata da idanu 17 IZGILI JAMILA MUHAMMED tana dan yin yanga baya ya ji samarin da suke kofar gidan da yake makoftaka da gidan Alhaji Umar mai akwai daya saurayin ya san shi dangi tane ɗaya ne bai sani ba, ɗaya saurayin ya ce, "Gata nan fa mutuniyar taka." Kanti ya juya baya. Bashi ya saki dariya ya ce, "Wallahi Allah ya suturu bakui in ji kishiyar mai dorina ina zan iya." Kanti ya juya baya "Ai ba zan iya koyaushe dan cinikin da nayi akasuwa su kare akantin nan mutane ba. Nura ya ce, "Yanzu ina jin ta daina tunda yai mata illa." 29 Bashi ya ce, "Ta daina me? Kallo kafarta ka gani mana malam tamkar ta turawa saboda tsahar mankanti fuskarce dai dai ta ga ji da man shi yasa ta lalace take rufeta yarinya sai shegen jiji da kai 18 IZGILI JAMILA MUHAMMED ke da fuska ta riga tai dameji har kece me wani ɗagawa mutane kai." Su ka sake dariya suka tafa Alhaji Mansir ya ce, "To me ye ma'anar Kanti. Ya juya baya sun santa ne ko̟ ku ma dai ita ma bata da nutsuwa tamkar su, dan kallo daya za kai musu ka san su din kwararrun 'yan duniya ne, haka zuciyar Alhaji mansir ta dinga masa tambayoyi barkatai wanda ba shi da amsar su, dai dai nan Alhaji Umar mai Akwai ya fito hannunsa dauke da wasu takardu ya karaso inda Alhaji mansir yake tsaye jikin motarsa, ya mika masa hannu gami da cewa “Ga_su_nan ka duba su, jibi jibin nan nake son tafiya Kaduna akan aikin makarantun nan. " Ya ce, "Insha Allahu zan yi kokarin ganin na gama su jibin su kai sallama ya shiga motarsa ya tafi. 19 IZGILI JAMILA MUHAMMED BAYAN SATI UKU Hadiya ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta kai dubanta ga Jana data ke ta faman baza powder Hadiya ta ce, "Dan Allah Jana kibar saka powder nan haka kin ga yamma ta yi kada Abbu ya dawo ya tarar bamu dawo ba gobe ba zai sake barina fita ba." Jana ta dan dauke idonta daga kallon Mirrow ta ce, "Dan Allah kada ki takuramin ki barni in yi kwalliyata cikin nutsuwa dan na sanki da shegiyar hayyata in ke bakya abu sai ki ha
🏠