e a Alu Aɓenue sai
kuma abokina kuma aminina shi kuma
sunansa Alhaji Mansir kwangila haifaffin
124
IZGILI JAMILA MUHAMMED
garin Gombe ne amma anan garin shi
yake yana zauna ne a Sultan Road kuma
shi ne wanda yai dalilin zuwannmu nan.”
"
Malam Usman ya ce, "TO madalla
Allah dai yasa lafiya .?"
Alhaji Yakubu ya kuma sakin
dariya ya ce, "Lafiya kalau, alhaji Daman
dai yaga 'ya wajenka ne ya yaba da
hankalinta da nutsuwa gami da tarbiya
irin ta gidan nan shi ne ya yiwa dansa
kamu, in dai babu wanda akaiwa
* alkawarito yaran gurinsa yana son ta. "
Malam Usman ya ja shiru na lokaci
mai tsaho sai can ya ce, "To Alhaji
hakikanin gaskiya ban yi mata miji ba,
kasancewar ban bata damar sauraran
samari ba, saboda karatu, take duk da dai
ta kusa gamawa dan saura wata uku ne
kurum ya rage ta gama, to amma wani
hanzari ba gudu ba, kamar na so na ji
125
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kace shi Alhajin ne yayaba da ita ba shi
yaron bane, ya ganta, ya ga yana son ta ba.
Alhaji Yakubu ya cc, “Haka nace to
mu din mu na yi ne kamar yanda shari'ar ta
tsara gurin neman aure kuma muna bin
yadda addini ya tanadar cewar idan zaku
aurar da 'yar ku, hakkin iyaye ne su
nemawa ‘yarsu miji na gari haka ma mijin
suna iya zaɓa masa mata ta gari shi yasa
muka zo da karfinmu saboda tarbiya irin ta
gidanka mu kai kwaɗayin hada zuri'a da
kai."
Malam Usman ya sauke ajiyar zuciya,
Gaskiya ya gamsu da duk wani bayani da
kuka yi kuma shi ma zai so hada zuri'a da
su dan ya fahinci su din dattawan kwarai ne,
kuma ya gane su din ba daya suke da sauran
,masu kudin wannan zamani ba, da karan
gidansu yafi ye musu talaka sau dubu, basu
talaka mutum ba, ba wai dan kuɗinsu ba
sai dan kamala da mutuncin da suka nuna ko
126
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kusa ko alama bai ga wani wulakanci ko
tsantsanin da suka nuna masa ba tun
zuwansu lallai ku a cikin masu kudin su din
daban suke ya cc, su dan ba shi lokaci zai
tuntuɓi mahaifyar yarinya ko da wanda ita
yarinya take so suka cc to babu damuwa
kamar yaushe yake ganin zasu dawo dan su
ji yadda ake ciki ya ce idan Allah ya yarda
nan da kwan uku suna iya dawowa su kai
masa godiya ya ce, Ai babu komai ya rako
su har kofar gida gurin motarsu ya nayi
musu fatan alkhairi da addu'ar sauka lafiya.-
Suna karayin musabaha, Bintu ita da
dan Auta Aliyu suka dawo daga Tahfiz,
suka durkusa har kasa suna gaishe su, suka
amsa cikin fara'a gami da jin dadin yadda
aka karramasu.
Alhaji Yakubu ya fito da kuɗi a
aljihunsa har sun mike ya kira su, suka
farasa gabansa sosai suka kuma durkosawa
ya mifa musu sababbin ‘yan dubu dubun da
127
IZGILI JAMILA MUHAMMED
ya kirgo guda goma ya mika musu yaran
tamkar ashim film suka wani zabura a tare
gami da mikewa har suna hada baki gurin
cewar A'a mun gude su kai hanyar shiga
gida Alhaji Yakubu ya juyo da kallansa ga
Malam Usman ya ce, "Haba Alhaji ya za kai
min haka yanzu ba zaka sa baki su karɓa ba,
ni fa na niya ba wai rokona su ka yi ba,
cewa nake ka karanta babu mai mai da
hannun kyauta sai shadani, hakan yana da
kyau hana yaro amsar Abubuwa a hannun
mutane. Amma fa idan bai san su ba in dai
mutum ya san yaro ka ba shi abu bai karɓa
ba, sai ka ji babu dadi duk da yake karбar
ma ko da yaron ya san yanda ya ba shi to
hakan ma koyan kwadayi ne, cewa nake a
iya zaman da mu ka dan yi yanzu da kai ka
yarda damu din masoyanka ne, tunda har
muna son hada zuri'a da kai nan ba da
dadewa ba, insha Allahu, ai ina ganin mun
zama daya ko ba haka banc.?"
128
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Malan Usman ya cc, "Hakkun amman
ina ganin Alhaji kudin nan sun yi yawa."
Alhaji Yakubu ya ce "Ba wani yawa
da su ka yi in dai ka dauke mu da zuciya
daya, kuma 'yan uwa ka ɗaukcmu."
Malam Usuman ya cc, "Wallahi da
zuciya daya na dauke ku. "
Alhaji Yakubu ya ce, "To In dai haka
ne to ka sa su su karɓa tun da ni ma
babansu ne.
99
Malam Usman ya yi murmushi kawai
ya juya zuwa soran gidan inda yai kiransu
ya dawo gurin su Alhajin yana karayi musu
godiya su kuma suka ce babu komai sune da
godiya.
Bintu ita da Aliyu suka durkusa suka
ce, "Abbu gamu ya nuna su Alhaji ya ce,
"Alhaji ne yake kiranku.'
Suka karasa gurinsu ya mika musu
kudin ya ce, "Abbunku ya ce, ku karɓa.'
"
129
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Suka juyo suna kallon Abbun nasu.
Malam Usnam ya ce, "Ku yi musu godiya."
Ai fa yara suka dinga zararo godiya
sai da Alhaji Mansir ya ce, "ya isa ku je gida
ku sayi Buskit.'
"
Suka ta shi cikin nutsuwa suka shige
gida babu wata harguwa irinta sauran yara,
komai cikin nutsuwa suke yinsa nan dai
suka sake sallama sannan suka ja motar
suka tafi, da alkawarin za su dawo nan da
kwana ukun.
******
Da daddare bayan sun gama cin tuwon
dare sun baje suna shan iska suna kuma hira
Malam Usman yai gyaran murya ya ce,
"Lafiya baki tambaye ni in da dan autanki
ya samu kudi ba.?"
Inna ta yi dariya ta ce, "Malam ke nan
ai tunda Hadiya ta bani kudin ta ce su Binta
ne suka cc ka yi baki shi ne bakin suka basu
13