gurin can, basa kansa.
Ya lura ya kurawa guri daya ido ya
kalli inda yaga yana kalla bai ga komai ba
sai kawai mutane da ya ga suna zirga
zirgarsu yawancinsu duk 'yan Islamiya ne
da suke ta tururuwarwar tafiya zuwa
gidajen iyayen su. Ya dan taɓa kafaɗarsa
gami da kiran sunansa.
Alhaji Mansir dan kimanin shekaru
saba'in da biyar, ya yi firgigit ya juyo
gare shi tamkar wanda ya ta shi daga
barci ya ce, “Am! Alhaji Umar me kake
cewa ne?"
7
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Alhaji Umar ya ce, "Ina hankalinka
ya tafi ne?"
Alhaji Mansir ya ce, "Na dan tafi
wani tunani."
Alhaji Umar ya ci gaba da yi masa
baya ni ya ce, “Mun yi dai dashi Nan da
sati hudu zai turo mana da cikwan kudin
dan wallahi sai da nai masa jan idanu, in
shi yana takamar dan zamani ne to ni
nashekaran jiya ne, dan na ga jiya naga
yau, kuma sai dana jaddda masa in har
lokacin yayi na ji babu labari to wallahi
kotu zan maka shege dan baka ga yadda
ya dinga bani hakuri ba da ya ga na je
masa ba sauki yana ta makyarkyata da ya
ji zancan Kotu yana bada hakuri nan na
taho na barshi. ".
Alhaji Mansir ya ce, "To shi ke nan
ni zan tafi yadda mu kai da Alha ji Auwal
game da aikin titunan nan zan ma waya.'
"
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Alhaji Umar mai Akwai ya ce, "To
babu damuwa,"
Su kai Musabaha. Alha ji Mansir ya
shiga dankararriyar motarsa ya tafi.
Zaune take atsakar gidansu tana
tankaɗan dawar tuwan dare Innarsu
Kuwa tana daga can gefe tana kaɗa miyar
Kuka, kuma suna ɗan taɓa hira
mahaifinsu ne Malam Usuman ya yi
Sallama gaba ɗaya suka amsa masa ya
shigo hannunsa rike da dan autan Innarsu
ɗaya Hannun kuwa bakar leda ce yake
rike da ita Inna Lariya ta saki Kadin
miyar da take yi ta shimfida masa wata
sabuwar tabarma da take jingine gefe
guda tana masa sannu da zuwa Hadiya da
sauri ta karɓi ledar da take hannunsa ita
ma ta nai masa sannu da zuwan Inna ta
dauko kofin silbar dake ajiye a gefe guda
9
IZGILI JAMILA MUHAMMED
wanda aka ci ka shi da sassanyar ruwan
Tulunta ta a jiyewa maigidan tana karai
masa sannu.
Ya sha ruwan sosai sanyinsa ya
ratsashi sannan yayi hamdala ya dire
kofin shima ya nai mata sannu da gida.
Aliyu dan Autan Inna yana daga
gefe sai murmushi yake faman dukawa
gaba daya ji yake tamkar an sakashi a gidan Aljanna saboda dadi ya san tunda
yaga Abbansu da leda yasan yau da cin
kayan dadi, shi yasa ji yake tamkar zai sume saboda murna, shi ma zai nunawa
su Abdul Abokinsa kayan dadin da
Abbansa ya siyo musu ko sa dainai masa
gorin babbansa baya siyo musu tsarabar
kasuwa kullum, Abdul sai ya yi masa
dariya saboda shi Abdul din babansu ko
da yaushe ya dawo daga kasuwa sai ya siyo musu kayan dadi su lemo, ayaba,
.
10
IZGILI
.
JAMILA MUHAMMED
abarba, Kwai, dafaffe, Biskit, youghort,
wata rana har da gasheshen nama ko
Kaza kuma ko babansu bai dawo da wuri
ba to da sassafe sai Abdul ya ajiye ya
nuna masa dan haka shi ma yau tunda
Abbansu ya siyo musu tsarabar kasuwa to
shi ma ba zai ci ba sai ya ajiye da safe ya
nunawa Abdul ya dai nai masa dariya
yana cewa babansu baya yo musu tsaraba
idan zai dawo daga kasuwa, kalubalenku
iyayan yara gaskiya da yawa iyayen yara
abinda muke bama kyautawa yadda
zamu dinga bawa yaranmu abu suna fita
da shi suna nunawa yaran makota ko
kuma yaran abokan zaman mu idan gidan
haya ne ta yadda zaki ga an bawa yaro
abu ya fita da shi cikin yaran gidansu
yana ci a irin haka ana samun matsala
babba, saboda wani yaran zai ‘yan musu
wani kuwa sai dai ya ɗagawa sauran
11
IZGILI JAMILA MUHAMMED
yaran hankali suna gani yana ci ba zai ba
su ba, haka za ki ga yara suna rusa kuka
duk su dagawa iyayen su mata hankali
dole sai an basu irin abinda wane yake ci
kun san yaro da gasa wata uwarma zaka
ga ita ke tura yaranta waje cikin yara ya
ci abin sai ka ga ta dauki abu ta ba shi sai
ta maza je ka gurinsu wane ku yi wasa
ko kuma fita tsakar gida gurin su wane ka
ci mana, to gaskiya irin haka babu dadi
ke dan asan kuna cin abu sai kin tura yaro
dan a gani alhalin yana dagawa yaran
mutane hankali.
Akwai matan da suke cewa yaransu
kada ka cinye duka mana ka rage da safe
ka nu̟nawą su wane, da dai ire-iren haka,
gaskiya mata mu daina irin wannan idan
ke kuna da halin cin abu bai ka mata ki
dinga turo yaranki suna dagawa wanda
12
i
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kika san basu da halin wannan abin dan
Allah mata mu daina Allah ka iya mana.
Inna Lariya ta juyo tana kallon
Malam din fuskarta fal da farin ciki ta ce,
"Malam yau dai da alamar dawa Tai
nama.? Tun da na ganka da leda.'
"
Shi ma murmushin ne akan fuskarsa
ya ce, "Yau kam Alhamdulillah babu
abinda zamu ce sai godiya."
Ta ce, "Gaskiya kuwa, ba ka ga
auta ba ma baki yaki rufuwa yarasa inda
zai sa ransa saboda murna sai wata dariya
yake ɓangalawa gaba daya su kai dariya
har da Hadiya wadda take kaɗe zaninta
ta matsar da garin tana cewa.
"Abbu Kalli irin zaman ma da yai
."
har da tankwashe kaafu.'
Suka kuma yin dariya.
Malam Usman ya ce, “Bar