a dawo da sati biyu suka
'koma saban gidan da Alhaji Mansir din
ya tamfatsa a sultan road a ciki ma a kai
bude saban kasaitacciyar walimar
kamfanin na Abuja da kuma murna
dawowar ɗan lelan Alhaji wanda Alhajin
ya sangarta shi ya taɓarashi, su ka kuma barshi yake yadda ya ga dama ba kuma
tare da sun tsawatar masa ba.
AN DAWO LABARI
Hadiya ce sun kuye bakin murhu
tana faman hura wuta taki ta kama kasan
cewar icen ɗanye ne saboda yana yi na
damina ta ɗago da idanuwanta da suka yi
jajir saboda a tsabar hayaki tana amsawa
118
IZGILI JAMILA MUHAMMED
yaron da ya shigo sallamar da ya yi,
yaron ya ce, “Wai wani Awaje ya ce, na
sallama da Malam Usman.?'
Ta ce "Kace yana zuwa.
Ta mike daga durkson da ta yi tana
karkade jikin ta ta yi sallama kofar ɗakin.
Innar ta su, in da baban nasu yake
kishingide yana sauraren gidan radio
kano suna gabatar da zaɓan yamma Inna
kuma bata nan ta tafi dubiya, amma ta san
tana hanya tunda yamma ta yi, duk da dai
bata wani jima da tafiya ba, dan sai bayan
sallar la'asar sannan ta tafi.
Malam Usman yasa hannu ya rage
radio yana amsa mata sallamar ta durkusata ce, "Abbu ana sallama da kai'a waje."
Ya ce, "Wa ye.?"
Ta ce, "Ni ma ban sani ba."
Ya dauki hularsa dake ajiye a
gefensa yana kokarin sawa ya ce, "To
119
IZGILI JAMILA MUHAMMED
'yar gidan Abbunta maza je ki ci gaba da
aikinki."
wata
Ta saki wata dariya mai ban
sha'awa ta tafi ta ci gaba da aiyukanta
shi ma Abbun fitowa ya yi dan ya ga mai
sallamar yana fitowa yaga
tsadaddiyar mota ta dallare masa idanu,
saboda kyau sabunta tai shurum a kofar
gidan nasa, tana hutawarta daga gefe
kuma wasu kasaitattun Alhazawan birni
ne tsaye a jikinsu sanye da dakakkun
danyin shaddodi, sai zabga daddadan
kamshin turare suke irin nasu na manya,
ya dan ja turjiya ya tsaya turus, yana
tunanin ina mai sallamar yake dan shi ko
kusa bai yi tunanin wadannan hamshakan
mutanan sune masu sallamar ba dan ya
san shi dai shehu Usman mai faci duk
cikin mutanan daya sani yake kuma har
120
IZGILL JAMILA MUHAMMED
kar dasu ba shi da irin wadannan balle
har yai tunanin su ne suke sallamar...
Sallamar ya ji an yi masa yai saurin
dawowa daga tunanin da yake yi, ya amsa
sallamar shi ma cikin sakin fuskar tamkar
dai suma da suke ta sakar masa,
murmushin. Shi dai shiru ya yi yana
kallonsu daya ne ya farayin magana ya
ce, "Mu ne muke sallama."
Ya ce, “To madalla Alhaji Yakubu
babban na hannu daman Alhaji Mansir
dinne dai har yanzu yake maganar ya cc,
"Daman Mun zo gurin ka ne da wata
muhimmiyar magana wadda take bukatar
zama dan ni din ba gwanin tsaiwa banc.
Ya fadi hakan yana dariya, wadda
ta bayyanar da hakorin farin gwal din da
yake bakinsa.
Malam Usman ya kalli rugujajjen
kofar gidan nasa mai dauke da jarkasa
121
IZGILI JAMILA MUHAMMED
tumumu irin jajur din nan ya kai dubansa
gurgurarriyar kofar shiga gidan ta katako
mai barazanar rusowa. Ya dan saci
kallonsu dubi irin danyun shaddojin dake
jikinsu yanzu haka zasu dansu a cikin
jarkasar nan wata zuciyar ta ce, to ya za'a
ayi ai sun kallo yadda gurin yake kuma a
hakan suke san su zauna. Ya dubi Alhaji
Yakubu ya ce, "To bara in kawo abin
zama.
"
Suka ce babu damuwa ya juya da
sauri çikin gidan ya same ni ina kwasar
tuwon dare ya ce.
"Hadiya maza shiga daki ki dauko
sabuwar tabarmar ledar nan cikin
girmamawa ta ce, "To"
Ta dauko da sauri ya ce, "Yauwa ki
zubo ruwan sha ki kawowa baki."
Ta amsa cikin girmamawa ta saurin
karasa kwashe tuwan ta dauko saɓanin
122
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kwanon sha sabo fil ta sake ɗauraye shi ta
tuttulo ruwan tulun Innar mai dan karen
sanyi ga shi ruwan dadi.
Farin fenti jikin kwanon shan sun
tai maka gurin fito da farin ruwan gami
da tsaftar sa tamkar irin ruwan da suka
saba amfani da shi, ta shiga ɗaki ta ɗauko
zumbulelen Hijab dinta da nikaf ta saka
ta ɗauki ruwan ta yi soro inda take jiyo
maganarsu duk da dai ba sosai ake jiyo
maganar ba ta yi sallama cikin siririyar
murya ta durukusa har kasa ta gaishe su
Alhaji Mansir da yake cike da fara'a gami
da wani matsanancin farin ciki ganinta a
zuciyarsa fadi yake tarbiya da dadi gami
da biyayya da sanin girman na gaba sai
gurin diyan talakawa dubi dai irin yadda
zube gwiwa bibbiyu saɓanin 'ya'yan
masu dà shi, wadda wata ma ko kallan
arziki abokanan babban nata basu isheta.
123
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Masu tarbiyar cikinsu ne zasu
gaishe su daga tsaye, ko kuma a ce,
sannunku.
Daddadar muryarta mai cike da
nutsuwa ce ta katse masa zancen zucin da
yake yi, ta ce, “Ga ruwa."
Alhaji Yakubu ya suri kwanan da ta
ajiye sanyin ruwan da ya ratsa kwannan
ya ratsa tafin hannunsa yayi saurin bude
murfin, ruwan garai-garai gwanin kyau
ya sha sanyin ruwan ya kwaranya a
tumbinsa yai hamdala Alhaji Mansir ma
ya sha su kai godiya ga Allah.
Alhaji Yakubu ya gyara murya ya
fara da gabatar da kansa ya ce "Ni suna
na Alhaji Yakubu Galadanci, ni haifaffen
garin nanne a galadanci iyayena suke
amman ni ina zauna n