ro
mahaifin Zalifa watan Wazirin Sarki
Misra ya dira duk mai bukatar zuwa
Nigeria. To fa ga jirgi nan a kai ka a
dawo da kai, haka akai taron suna lafiya a
ka gama lafiya Jariri ya ci suna Hisham.
Hisham ya ta shi yaro mai-nutsuwa
gami da hankali amma fa miskili ne na
gasken gaske shekararsa biyu a duniya
Allah ya yiwa kakansa Alhaji Bawa
rasuwa, rasuwar da ta girgiza duk wani
mutum daya kwana ya ta shi a cikin garin
na Gombe jama'a sun ji mutuwar mutum
na mutane irin Alhaji Bawa, mai kirki
99
IZGILI JAMILA MUHAMMED
mai taimakon bayin Allah mai hidima a
gurin jadda kalmar Allah.
Ayyukan da yake gami da taimakon
da yake sai dai Allah ya biya shi
Islamiyyoyi da masallatai fanfuna
burtsatse babu wanda yasan adadin da ya
yi a cikin birnin na Gombe da ma
kauyikansu sai dai mu ce, Allah ya ji
kansa, halinsa na gari ya bishi, mutuwar
Alhaji Bawa da shekara Alhaji Mansir ya
tattaro ya dawo Kanon dabo mai mata
mai mota mai dala da gworon dutse.
saboda harkokinsa sun fi yawa a can kano
da Abuja, a inda ya kera gidansa a Zoo
road suka tare sai dai duk karshen wata
yake zuwa Gombe domin duba hajiyar,
sai da ya kaɗa ya raya ya ce, Hajya ta
dawo amma ta tubure ta ce, babu inda
zata saboda mutanan alhaji marigayi
saboda duk wani abu da ake yi da babu
100
IZGILI JAMILA MUHAMMED
wanda aka daina 'yan'yan ta maza sun
tsaya mata musamman Alhaji mansir dan
shi ne ya dauko kyauta irin ta
mahaifinsa, da son talakawa mararshi,
dan gaskiya yafi kannensa najib da
Isma’il taimako dan su da Hajjo tai musu
zancen duk wata ga abinda zasu kawo
cewa su kai kai a bari wanda Baffa ya yi
ya yi, ya isa, Allah ya bada lada.
Batai mamakin jin irin wannan
maganar daga bakinsu ba dan ta sansu ta
san halinsu suna kyamatar talaka sun ce
su da talaka ko a hanya, shi yasa
kwandalarsu ba zasu bayar ba, dama da
mahaifinsu yake yi ba asan ransu bane,
dan dai ba yanda zasu yi ne, kuma saboda
ba kudinsu bane, ko da yake shi najib sai
da ya taɓa gayawa Hajjo gaskiya ta
gayawa Baffa ya daina kashe musu kudi
haka.
101
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Ta kalle shi da alamar tambaya ta
ce, "Wana irin kudinku yake kashewa
aikuwa babu kun ya babu tsoon Allah ya
ce, Dukiyar Baffan nasu ai ta suce saboda
haka gaskiya Baffa ya daina raban kudi
da abinci ai sangarta su ake yi, su dinga
zaman banza, zuciyarsu ta ida mutuwa,
tunda suna da mai basu abinci har ma da
nace fane, dan kada ta Allah ta kasance
gadonsu ya zaru babu auki."
Hajjo sai ta saka salati tana
salallami fadi take oh ni Rahine yau naga.
abinda ya ishe ni najib Allah ya shiryeka
to ni dai ba za aji wannan maganar a
bakina ba, idan ka matsu kai ka same shi
sai kai masa maganar, shi yasa koda suka
ce su ficikarsu bazasu bayar ba bata damu
ba, ta gayawa Alhaji mansir ya ce, Dama
bata yi musu magana ba.
102
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Hajjo kin san dai kome ye kike
bukata zan yi miki su yarane daman niya
dace in yi ko meye Hajjo ta ce, "Duk da
haka kai ma ai zaka so su taimaka maka
tunda abinda ai da yawa, kuma kamar
yanda kudi suke zuwar maka suma haka
kawai dai su haka Allah ya yosu in dai
batu ne nasu bayar to fa ba za a ji bakinsu
ba, saboda Allah rayuwa kuwa zata yiwu.
a haka kana da shi ba zaka taimaki dan
uwanka marasa shi ba.
Alhaji Mansir ya ce, "Hajjo ki daina
ganin laifinsu suna fa da iyali ga yara da
wanne za su ji."
Hajjo ta ce, "Da yake kai baka da
iyalin ko haka dai ya dinga bata hakuri ya
ce, tunda ya ce, zai iya zai iya dinne
tunda mahaifinsu ya rasu, shi ya dauki
nauyin yin sadakar da aka sabayi, duk
safiya ana dama koko da kosan sadaka
103
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kuma kokon da sukarinsa bajau, da rana
kuma ana yin wake da shinkafa da mai
mutum sai dai ya nemi ya ji, kuma ba sai
almajirai ba ko waye in dai yake ko ya
kai kwanansa, duk girmansa sai an take
masa shi abinci, duk ranar juma;a ana can
ja kalar girkin da safe ana yin kunun
tsamiya da fanke, da rana kuma ana yin
tuwon shinkafa da miyar taushe, kuma
gaba daya Alhaji mansir ne yake komai
hatta da 'yan aikin da suke wannan
aiyukan shi yake biyansu, kwandala babu
ta wani dan uwansa kuma duk karshen
Iwata yake zuwa ya saurari talakawan da
mahaifinsa yake taimaka musu, wasu
bikin 'ya zai yi babu gaba ba baya.
Wani matarsa ce ta haihu babu
Ragon suna wau rusaune ya rutsa da su,
da dai sauransu duk kuma wanda ya
kawowa Alhaji Mansir matsalarsa to sha
104
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Allahu sai ya taimaka masa sai mutumin
nan ya yi farin ciki ya saka masa albarka.
Hisham ya yi Primary dinsa wata
tsadaddiyar makaranta dake cikin birnin
na Kano mai suna Attaufeek Iliman an
tahafees yaro ranar da ya gama primary,
to ranar aka masa bikin sauka to shi ma
Hisham haka daga nan sai alhaji Mansir
ya kai shi Germany gidan kanwar Hajiya
Zalifan watan Nadiya da take aure a can
suke zaune a can ita da mijinta sai dai
basu haihu ba a can yai Secondry dinsa
yai kuma jami'a.
Hisham ya zaɓi ya gaji dadinsu
watan dai yana san zama contr