NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 22

AMILA MUHAMMED da muke bukata buka, sannan yana da kamfanin Tumaturin gwangwani sannan yana da wani kamfani amma hadin gwiwa ne, a jafan da suke kera takalma masu shegen kyau, matar Alhaji Bawa, daya mai suna Rahina, ana kiranta da Hajjo Allah ya albarkace su da ‘ya'ya bakwai uku maza hudu. Mata ta farko mace ce mai suna Binta da ake kiranta Batulu, sai na biyu mai suna Mansir, daga mansir sai Barira sannan Hindu, sai najib, sai Safiya, da kuma dan autansu, Isma'il gaba dayansu, sun ta so cikin kulawa hade da tarbiya irinta addinin musulunci sam Alhaji Bawa shi da Hajjo basu saki yaran sun sangartasu ba, wai dan kasancewar mahaifinsu, wani ne, sun basu tarbiya ta gari dan gaba ɗayansu, sai da kowa ya sauke sun yi karatunsu na boko amma 93 IZGILI JAMILA MUHAMMED matan iyakar su secondry ake yi musu aure Inna Batulu anan Gombe take aure bata taɓa haihuwa ba. . Safiya Bauci take da yaranta Hindu Abuja ita ma dana ta yaran Barira ma anan Gomben take dan ita basu da nisa da gidan iyayan nasu maza ne ya ce, su yi karatu, duk anan gida Nigeria dan bai yarda ya tura dansa wata uwa duniya da sunan karatu ba, kuma garin da suka daurewa sheɗana da duk wata lalata kugu wanne karatun waɗannan makiya Allah zasu koyawa yaran da suke son musulmi ne su da a duk duniya basu da abokin gabar da ya wuce, musulmi, to wanne karatu zasu koya masa ban da su wayar masa kai, ya san ilimin lalata ni wallahi wannan abin yana damu na rashin sanin. ciwon kanmu, Nigeria wani bature ko ka taɓa ganin ya kawo dansa Nigeria ya ce, 94 IZGILI JAMILA MUHAMMED ya yi karatu, sai mu da bama kishin kasar mu zamu ringa jidar ‘ya'yanmu tamkar gyada muna kaiwa makiyanmu masu burin ganin sun karmu sun rusa mu, su zamu bawa yaranmu. Ai wannan damar suke samu su koyawa yaranmu duk wata sheɗana, sai sun gama lalata musu tarbiya sannnan zasu turo mana su dan su zame mana annoba, su buwaye mu, dan haka Alhaji Bawa yana daya daga cikin mutane masu kyamatar tura yaransu karatu waje, gaba dayansu mazan sun yi karatun su ne a nan gida Nigeria. Alhaji Mansir ya yi karatun sane a Jima'ar A.B'U A.B'U Zariya inda ya yi karatunsa akan kasuwanci wato Business. Mansir ya dade bai yi aure ba, dan har sai da dan Auta Isma'il ya fara haɓaka Alhaji Mansir ya haɗu da Zalifa ne a Misra 95 : IZGILL JAMILA MUHAMMED lokacin ya ji kan wasu harkoki da suka kai shi Zalifa balarabiya ce, gaba da baya mahaifinta shi ne Wazirin Sarkin na Misra. Mansir ya haɗu da Zalifa ne ta sanadiyar 'ya'yanta wanda Allah ya haɗa su anan garin Kamfanin Babanta ya je, domin gogewa da sanin makamar aiki, domin ya fada har kar Kwangila to wata rana ne shi ya yanta Alhaji bashir ya gaiyace, shi cin abinci gidansa to sai Akai sa'a Zalifan ta je gidan yayan nata ita da kanwarta Nadiya, tun daga sannan soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu ansha fama kafin kasancewarsu matsayin ma'aurata, saboda iyayanta basa son tai musu nisa dagewarta ce, tasa iyayen suka hakura suka aura mata wanda take so batare da ɓata lokaci ba aka sha biki amarya ta tare a Nigeriya a 96 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma a garin ‘iyayan mijinta watan Gombe da farko iyayansa da yan uwansa duk suna son ta amma daga baya duk sai suka canja canja mata su ka bi suka tsangwameta ta kuma rasa dalili sai daga baya ta gane kan rashin haihuwar da bata yi bane, a zuciyarta tai mamaki shekara uku ne kawai da auran su shi ne har ake gwada mata tsana irin wannan ta shiga tsananin damuwa ta yadda dangin miji suke tsangwamarta suka mai da ita mujiya a cikinsu, duk ta bi ta rame, sai hanci da manyan idanuwanta da suka karayin manya idanuwanta da suka karayin waje, gaskiya Zalifa kyakkyawa ce dan ko cikin larabawan ma ita din mai kyau ce, amma duk irin abinda suke mata bata taɓa gayawa mijinta ba sai dai ko yaushe ya nai mata korafin ramar da take yi, ta yi yawa, to dole ne ta rame babu 97 IZGILI JAMILA MUHAMMED 'yan uwa akusa dangin mijin da take san su zama 'yan uwanta sun tsaneta basa son ta idan ta je inda suke suna kyararta ai dole ta shiga wani yanayi to abin Allah shekararsu biyar da aure Allah ya bawa zalifa ciki wai murna a gurin Mansir da Zalifa ba'a magana har ma da dangin nasa da suke kinta sai duk suka saki aka shiga tarairayarta, shi Alhaji mansir Bawa ya yi mutukar murna da Allah ya nufeshi da ganin jika, daga Mansir da yake Mansir yaro ne mai hankali da biyayya ga taimakon marasa karfi. Akwana a tashi har Allah ya sauki Zalifa lafiya ta haifi danta namiji wowowo fadin kyau ɓata baki ne vare. daka ganshi kasan jinin larabawa ne, saboda tsantsar kyaunsa duk wanda ya zo barka sai ya tafi da zancen yaron nan, Hmm! Zo ka ga bakin Alhaji Mansir yaki ng IZGILI JAMILA MUHAMMED rufawa sai Hidima yake ya kawo wannan ya kawo wancan dangin Zalifa ma ba a barsu a baya ba, ana igobe suna suma suka diro nigeria dauke da kwaryakwaryar kayan arziki dan danginta sun zo da dama, dan jirgi sukutum kakan ya
🏠