bansa, sai dai fa baya so idan ke kina so
ya bar miki shi ke ka ɗai idan kema ba
kya so to ga gidan marayu nan kina iya
IZGILI JAMILA MUHAMMED
sadashi da can, idan kuwa ke din irin
barebarin nance, to uku ya yi yawa zai ce
waje road shi din bai dauki mace a bakin
komai ba face, ruwan kashe gobara, shi
yasa baya daukan raini, ko wulakanci
daga gurin kowa ce irin mace ba, da zaki
kawo masa shakiyancin banza zai gaya
miki ke din ba wata tsiya bace, agurinsa,
dan idan ya so ana fita da kayanki ana
shigo da na wata dan cewarsa mata sun
yi yawa, tamkar ledar pure water ne, ga
sunan burjik, duk inda ka zaga birni da
kauye, dan haka shi a gurinsa, canja mace
a gurinsa tamkar canja rigar jikinsa ne,
duk sanda ya bukaci yasha iska zai canza
ki da wadda ya ke so, shi yasa” yake
mutukar ganin bakin abokin nasa, ganin
tun wani shuɗadɗen zamani yake fama
da mata daya Aisha, wallahi ba zai iya
ba, sai wani ciwon ya shige shi, saboda
87
7
IZGILI JAMILA MUHAMMED
bakin ciki da takaicin kaɗaici,, kullum
babu wani canji sai kace masifa.
Alhaji Umar ya karkatar da kai,
yana kallon Abokin nasa ya ce, "Alhaji
Wai duk murnar wannan maganar ne,
yasa kake wannan rawar jikin hade da
wannan batun kudi, tamkar wani wanda
bai san ciwon su ba, akan wata can diyan
talaka, irin wannan kyautar ko ka manta
abinda dan Audu ya fada ne, ubanta ba
kowa bane, face, talaka, a cikin talakawan
ma na karshe a gun talauci ko baka ji
sosai bane cewa ya yi ubanta fa faci yake
yi, aini cewa nake daga jin baya nin Dan
Audu ko duban mai rin kamaninta ba
zaka sake yi ba, a matsayin Hisham na
dan mai kudi wayayye, kyakkyawa me
zai da wata Diyan talaka duk ‘ya'yan
manyan masu sukuni karasa wadda zata
zama sirikarka, matar danka, sai wata
IZGILI JAMILA MUHAMMED
‘yar mai faci, kai wannan abu da bakin
ciki yake, ina garin gami mai kuɗi da
talaka, da har za kai sha'awar hada
zuri'arka da ta shi.'
"
Alhaji Mansir Kwangila ya ce,
"Wai ni shin Alhaji Umar mai ka ɗauki
talaka ne, kaskantantacce, wulakantacce,
kuma mara 'yanci, wanda duk sanda mai
akwai (Mai kudi) ya mula yasha iska zai
ciwa zarafi, ciwa zarafi, ya tozarta shi dan
kawai Allah ya yishi mai shi, shi kuma ya
yo shi mara shi, to ba haka bane, talaka
mutum ne, tamkar kai, kuma ba'a bin
wulakantawa bane saboda dinbin daraja
da martabar da Allah yai wa bayinsa ‘yan
adam Allah da kansa yake faɗa a cikin
alkur'aninsa mai tsarki WALAKADI
KARRAMNA BANI ADAM!!! Hakika
ubangiji ya daraja ya girmama ɗan adam
sai kai dan kawai Allah ya huwace maka
89%
IZGILI JAMILA MUHAMMED
za ka wulakanta mutum talaka, waya sani
ma ko mutumin da kake wulakantawar ya
fika a gurin Allah dan haka wallahi
wallahi banga dalilin da zan kyamace
talaka ba, wai dan kawai ni me shi ne, shi
kuma mara shi, to haka Allah. ya nufin ya
ganshi, kuma ba zan taɓa kin saba, wai
dan yana faci, faci ai sana'ace, a gurin
kane da ka raina shi har kake kiransa da
al'amarin
duniya ba yadda ka zata bane. Dan kana
ganin kana da kudi to dare daya idan
Allah yai nufin nuna ikonsa da buwayarsa.
sai ya mai da shi kai da kake kiran
koma ya fika
sunan kaskantacce kuma
kaskantattace matsayinka kake kiran
kai kuma kadawo kamarsa, ko da yake ba
za kai jarumtakar da ya yi ba, tunda ance ya daɗe a nan anguwar amma baka san shi ba, kaga hakan yana nufin ya iya da talaucinsa, tunda bai taba takowa kofar
IZGILI JAMILA MUHAMMED
gidanka da sunan maulaba, ka ga hakan
yana nuni da cewar shi din mai
jajircewane, da kuma tsayawa iya
matsayin da Allah ya ajiye shi, kuma bai
yi bakin ciki da yadda Allah ya yoshi
marashi ba, bare ya dinga binbinin a
gurin masu akwai ba suna wulakanta shi,
kafin su dan watsa masa ‘yartsaba su nai
masa dagawa, suna hura hanci ka ga
kuwa akwai tarbiya a irin wannan gidan,
sakamako 'ya'yanmu da muke barinsu
babu tarbiya dan haka in dai ni Mansir ni
ne mahaifin Hisham to fa bashi da wata
matar aure idan ba 'yar gidan mai faci ba.
Alhaji Umar ya tsurawa abokin
nashi ido an ya kuwa kansa kalau, kai
anya kuwa ko da yake daman yasan
halinsa in dai akan talaka ne, yo mutumin
da zai zauna gurin mai gadi suna hira,
idan ka ganshi da ma aikatan gidansa
91
IZGILI JAMILA MUHAMMED
yana kwasar dariya tamkar ba mai
gidansu ba sai ka ga har wani share musu
bakin yake tamkar ba mai kuɗi ba, shi
yaga zai iya, shi yasa fa ko dariya baya
iya yi a gidansa, dan kar wata ta yi gigin
raina shi, in kaga dariyarsa, to yana
majalisar su ta masu akwai ne."
******
"
Shin wanene alhaji Mansir kwangila
Alhaji Mansir Asalinsa dan garin Gombe
ne mahaifinsa mai suna Alhaji Bawa,
shahararren mai arziki ne sannane a cikin
garin na Gombe, kai bama nan kadai ba,
har da sauran garuruwan da ke cikin
Nigeria ya shahara sosai dan kasuwa ne
babu irin kasuwanci da ba ya taɓawa, ya
kan sari Auduga ya sarrafa tata a
kamfaninsa yana fita da ita kasashen
duniya, idan ya ta shi dawowa shi kuma
sai ya saro shinkafa da wasu kayayyakin
92
IZGILI J