NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 22

eman kudi, ga kuma iyali, dan ba karamar wahala na sha ba kafin Allah ya datar dani, na samu wannan aikin dan haka dan Allah Baba ka yi hakuri kuma ka dinga kiyayewa abinda zai ja ya ci mutuncinka, tun da shi baya ganin mutunci da kima hade da darajar talaka ba. Baba ya ce, "Kada ka damu insha Allahu haka ba zata sake kasancewa ba, zan kiyaye, tunda abin babu mutunci sai kai ka alkinta girmanka dan kada a sake ci maka mutunci.' 95 80 IZGILI JAMILA MUHAMMED Malam Sale ya ce, "Wannan gaskiya ne dole ne ka dinga kiyaye abinda zai sa a wulakanta ka." ****** Dan audu ne yake ta faman korawa Alhaji Umar mai da akwai tare da abokin nasa labari. Fuskar alhaji Mansir ta cika da annuri ya godewa Allah tunda ya taimaka aka samu gidan dashi har ya shiga damuwa da yasa yaji shiru bai sake ganinta ba, kuma ya ji dadin yadda Dan Audu ya bincika ya gama cika shi haka nan Allah yasa ka masa kaunarta tun ganin daya ke ta mafarki yana yawan ganinsa yana zaune a wani dokar daji ya nata kuka shi kaɗai sai ya ganta ta zo tana bashi hakuri tana lallashinsa duk da baya ganin fuskarta wani sa in kuma sai ya ganshi yana cikin fain ciki yana ta yin mrmushin amma ita tana kuka shiya sa ta 81 IZGILI JAMILA MUHAMMED tsananta da addu'a ya kuma sa'a taya shi saukar karatu duk juma'a akan dai Allah ya tabbatar da Alkhairi idan ita ce, mafi alkhairi ya kuma kawo sauki ciki lamarin ya kade fitina dake cikin al'amarin. Dan Audu ganin irin tarin fara'ar dake fuskar alhajin yasa ya kara kaimi yana kara koro wasu kuskuren zancen duk dai akokarinsa na ganin Alhaji yaga kokarinsa aikinnasa. hade da kwazansa akan Aikuwa kwalliya ta biya kudin sabulu dan kuwa Alhaji ya yi masa kyauta ta mu samman ya yinda Alhaji ya ce, tukukaicin ka ka gobe ka jira zai a kawo maka mashin shi ne tukuicin binciko min gidansu, da ka yi ya kuma dantso kudin da bai tsaya kirgawa ba ya ce, "Wannan kuma kasha ruwa ka ji, ladan kyakkyawan labarin. 82 IZGILI JAMILA MUHAMMED Dan audu tamkar zai shiɗe saboda murna godiya yake gami da jero dogayan addu'o'in tamkar wani saban maroki, yana karkawa yayi durkoso a gabansa yana faman jinjina masa hannu tamkar yanda akewa sarakai. Alhaji Mansir ya ce, "To dan Audu sai gobe ke nan. " Ya ce, "To ya alhaj." Alhaji ya fita yana kwararowa ‘ya'yan har jikoki dama tattaɓa kunnan alhaji kasan zuciyarsa yana ta kakkabin halin kwarai irin na wannan alhajin shi sam ba matsolo bane tamkar uban gidan nasa, da bai ajiye komai ba sai shegiyar rowa ta bala'i duk yanda kake da shi babbar kyautarsa ita ce, ya bawa mutum gudar dubu ɗaya, to lallai wata dakwalar budurwa ko bazawara ya kawo masa labarinta to kuwa zai samu gudar dubu ko 83 1 IZGILI JAMILA MUHAMMED kuma yinin ya yi yana wahalta masa, to idan ba daya daga cikin wannan ba ne to tsakaninsa da kai dari biyu ne sai kuwa idan yasan kanai masa wata ranar ne. Zai iya baka dari biyar shi ba abin kunya bane ka zo neman taimako gurinsa amatsayinka na yaransa ko kuma dan uwansa ya tattakura ya fito da naira hamsin ya ce, a sai wa yara garin rogo (kwaki) Duk unguwar Koki babu wanda bai sanshi ba, koda karamin yaro ne, ka tambaye shi gidan Alhaji Umar mai akwai to zai nuna maka sai fa in mai shan nono ne. Kowa yasanshi saboda tsabar son kudinsa da matsolancinsa uwa uba kin talaka ya ce, talaka ba shi da wani alfanu a gurin mai akwai. (Wato mai kudi) face, hidim ta masa shi kuma ya biya shi shi ne IZGILI JAMILA MUHAMMED kawai amfanin talaka a gurin mai akwai, alhaji Umar mai akwai ya yi mutukar tsanar talaka gani yake tamkar shi mutumin shi ya ɗorawa kansa talauci ba Allah ba, Alhaji Umar mai akwai shaharar ran mai auri saki ne gaba ɗaya kudinsa suna tafiya ne aa gurin aure aurensa mutane da dama sun ce auran dandano yake ga shi kuma baya san 'ya'yan abin Allah sai ya yo shi daga cikin masu rabon samun 'ya'ya, ko ya ya taɓa mace, sai ta samu rabo da shi kuma abinda yake ba kanta masa ke nan. Shi fa gani yake a duk duniya babu babbar matsalar irin zama da mace ɗaya yasha yiwa abokansa fada idan yana jin suna fadin matarsu daya ta ishe su ya kance ba kuda hankali ba kusan ciwon kanku ba, in banda rashin sanin me duniya take ciki, ya za ka zauna da mace, 85 IZGILI JAMILA MUHAMMED daya sai kace jaraba aini ko mata huɗu ba zan iya zubewa ba in yi shekara dasu batare da na yi can ji ba, ai gara adinga yi ana sabuntawa, aikuwa Alhaji Umar mai akwai ya auri mata kusan ashirin da uku, a kun dade da shi kina iya masa so sai shi ne zai barki ki yi shekara, to daga nan zai ɗaga miki jan kati idan ciki ne dake zai ce ya bar miki abinda yake cikinki duniya da lahira kada ki kuskura ki doso shi da wata matsala ta dan zai kuma yi miki ba, razanar ranku daga ke har yaran in dai kika kuskura kika danganta shi da wata matsala ta yaran zai kuma gaya miki zai fara rufawa yaran asiri, dan kada ai masa gorin ko yaran shege ne zai kuma gaya miki yana nan a amaṭsayinsa na u
🏠