an aikinka ba ko
kuma dan ka koshi zaka nuna halin naku
na talakawa, daga kunci abinci sai ku
ɓollo da salo na rashin mutunci.
Baba Audu babu abinda yake in
banda makyarkyata yana durkushe yana
bawa ubangidan nashi hakuri tamkar
zugashi yake, sai faman tujara yake yi
masa da tozarci, kala-kala, tsohon zai
baka tausayi mutuka saboda a kalla ba a
kasara ba zai yi jika da shi, sai wulakanci
yake yi masa, irin na zafin naman nan.
Hisham ya ci gaba da yarfa ruwan
rashin mutunci yace, "Saboda tsabar ka
isa tun jiya abaka dakardu ka bani dan.
tsabar raini kaki bani har sai da mutumin
yayo min waya saboda ya ji shiru, sam
baka da niyar bani, saboda ka fara
farfaɗowa daga cutar talauci, data kama
ka, yanzu kana jin aljihunka da nauyi shi
74
IZGILI JAMILA MUHAMMED
ne kake ganin dai-dai kake da kowa tsiyar
talaka ke nan, a ɗaukeshi ranga ranga a
taimake shi daya fara koshi kai zai
farayiwa rashin mutunci, shi yasa ni da
talaka babu wani tausayi, ban ɗauki
talaka a bakin komai ba, face,
kaskantaccen bawa, wanda zai min bauta
in biya shi, a duniya babu wata rana da
talaka yake da ita, bashi kuma da wani
amfani daya wuce mai kudi ya bautar
dashi domin shi bawansa ne.'
"
Shi dai Baba Audu in ban da ban
hakuri babu abinda yake yi sai da ya ji ya
ɗan tsagaita sannan ya fara bayaninsa ya
ce, "Wallahi yallaɓai sanda mutumin nan
ya kawo takardun nan ka fita kuma baka
sake dawowa ba zuwa kuma sanda ka
shigo na manta sai yanzu na tuna, ina
shirin kawo maka sai kuma ga ka, amma
75
IZGILI JAMILA MUHAMMED
dan Allah dan Annabi ka yi hakuri hakan
ba zata sake-faruwa ba, in sha Allahu.'
"
Cikin Izgilanci gami da wulakanci
ya karɓi takardun ya ce, "Kuma daga yau
sai yau muddin haka ta kara faruwa to a
bakin aikinka, sake kwatanta abinda ka
yi, yana nufin ka koshi dai-dai kake da
kowa. Dan haka yarage ruwanka, ka
kiyaye, ko ka sake, aikatawa.
Cikin takunsa na isa hade da kasaita
ya bar wajen baba Audu ya dade
tsugunne a inda ya barshi saboda tunda
yake ba a taɓayi masa wulakanci da
kaskanci irin na yau ba, sai kawai ya ji
wani irin zazzafan hawaye suna zubo
masa ace kamar wannan da yayi jika
dashi a ce dan Allah ya yo shi talaka yana
aikin a karkashinsa kan ya yi masa laifin
da bai taka kara ya karya ba, zai zage
76
IZGILI JAMILA MUHAMMED
haka, yana gaya masa irin wadannan
maganganun.
Ya mike daga durkuson da ya yi
yana sharar kwalla cikin mutuwar jiki ya
koma kan benci da yake kai dai-dai nan
yaji sallama akansa ya dago da sauri yana
amsawa Malam Saleh ne direban
kamfanin ne ya zauna kusa dashi yana
bashi baki ya ce, "Baba ka yi hakuri da
abinda yallaɓai ya yi maka tunda Allah
ya haɗamu zama dashi babu yadda zamu
yi sai dai hakuri shi fa a duk duniya babu
wulakantacce a gurinsa kamar talaka,
babu wanda yake kyama yake tsangwama
hade da kyara irin talaka, gani yake
takalmin kafarshi yafi talaka, daraja, a
gurinsa ka gan ni nan Baba yallaɓai ba
jin kunyar na yi sa'an mahaifinsa baya
iya cire hannu ya wanke min fuska da
mari.
T
By lay mida on ideol
77
:
IZGILI JAMILA MUHAMMED
Baba Audu ya ce, "Me yai zafi
malam Saleh?"
Malam Saleh ya ce, "Ranar kaddara
ce ta hau kaina ya aike ni ne to akan
hanyata ne karfan nasara da bashi da
tabbas sai kawai mota ta tsaya cak na yi
na yi taki ta shi na rasa inda zansa raina
dan yaja kunne na in yi sauri mutumin
sauri yake zai bar kasar ne, gaba ɗaya
hankalina ya gama ta shi kuskuran da na
yi na rashin kiransa in gaya masa tun a
lokacin kawai sai na fita ina ta 'yan
dabaruna ga mi da ‘yan jogane-jogane na,
na ma buɗe in jin motar ina ta
jagwalgwalawata na bar wayata a cikin
mota a she, shi mutumin da ya aike ni
gurinsa yana tai masa waya ya ce, ban fa
zo ba shi kuma zai yi missin din jirgin shi
dan haka shi ya tafi, sai kuma wani
lokacin, shi ne shima yallaɓai ya keta
78
IZGILI JAMILA MUHAMMED
kiran wayata ina ni ban sani ba, danni ina
waje ita wayar tana mota dan haka banji
kiran da yake tayimin ba.
Sai da akalla na yi kusan awa biyu
da wasu 'yan mintoci sannan cikin ikon
Allah sai ga shi ta tashi ai cikin sauri na
rufeta saboda sai da ya gargade ni da
lallai lallai in tabbatar duk yanda zan yi
nan da minti arba'in in kasance a gurin,
to gashi na kusanyin awa uku aikuwa
wanda na je domin sa yama daɗe da
tafiya cikin sanyi jiki naja motar na dawo
na riga na sani nashi ga wani hali, yau sai
Allah aikuwa tunda nai horn aka bude
min na ganshi yana ta zirga-zirga tamkar
mai nakuda na sanni kuma sai Allah,
aikuwa ina tsayawa na fito na durkusa
kafin ince wani abu sai jin wani
shahararren mari na yi akan kuncina ta
inda yake shiga ba tanan yake fita ba,
79
IZGILI JAMILA MUHAMMED
ashe takardun wata kwangila ce zan
karɓo masa da yake shirin shakar
makudan kudade bana wasa ba, shi ke
nan in ba wani ikon Allah ba ya rasa su.
A ranar na dandani bakin ciki bana
wasa ba wallahi da ina da yadda zan yi da
tun a lokacin zan baar aikin nan, to bani
da wata hanyar n