NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 22

a ce, "Yau ko in ce ma yanzu, idan kuma kana mamaki ne to ka bude mana. " Ai da sauri Hisham ya cillar da wayarsa yai bedroom dinsa da gudu Farida Saraki da Kudurat zaune 'yam matansa da yake ji dasu dan duk gaba dayansu ba baya ba, suna iyawa dashi. Suna kwance akan gado haihuwar uwarsu da sauri ya daka musu tsawa ya ce, “Maza ku barmin gidana ga Daddy na nan ya zo." Cikin sauri ya zurma jallabiyar da yake sallah da ita ya bude dirowar gadon ya dauko kudi kowacce ya bata ya ce, 67 IZGILI JAMILA MUHAMMED “Sai na neme ku kada wadda tai gigin zuwa idan ba na kirata ba, yana gama fadar haka ya ce, Ku fito suka fito sai ya bude kofar. Kudirat ta saki dariya ta ce, "Handsome kalle kafa babu pant ana ganinka a haka zaka je gurin Daddy." Cikin sauri ya kalli jikinsa ai kuwa ana ganin nasa kasan cewar rigar ruwan madara ce kuma tana da yauki mannewa mutum take da sauri ya fada dakin ya sako gajeran wando ya fito dai-dai nan ya sake jin karar wayar ya san mai kiran batare da ya dauki wayar ba ya bude kofar yana washe baki daddy ya ce, "Ai ni da badan maigadinka ya ce, kana nan ba kuma naga duk motocinka suna nan da cewa zan yi baka gidan ko kuma ba ka yi murnar gani na ba my son?" Hisham ya ce, "Na yi murna mana daddy.' 68 IZGILI JAMILA MUHAMMED Daidai nan suka shigo cikin falon sosai Daddy ya kallu Kudurat da suke zaune a falon ya mai da kanshi ga Hisham din da yake tsaye da alamun tambaya a fuskarsa, Hisman ya ce, "Wadannan abokan aikinane wani aiki ne ya kawosu yanzu. Suka gaida daddy ya amsa musu fuska babu walwala su kai waje Hisman ya buɗe firij ya kawowa Daddy Ruwa da lemo yana kuma tambayar Mominsa. Daddy ya ce, "Tana lafiya.” Daddy ya gyara zama ya ce, “Wai ni shin Hisham sai yaushe za kai aure ne, ko yaushe akai maka magana daga kace wannan sai kace wan can kana ta faman zille-zille. Hisham ya ce, “Haba Daddy ni fa ba girma na yi ba, just 33 year ne fa ka ga da saura na. وو 69 IZGILI JAMILA MUHAMMED Daddy ya ce, "Da sauranka fa tunda ba kai sittin ba,mana tunda shi ne dai-dai lokacin ka ko?" Hisham ya ɓata fuska tabbacin baya son fadan nan ya ce, "Please Daddy ka bar maganar nan daga zuwanka ko hutawa ba ka yi ba, me ake da aure, aure ai takura ne. " Daddy ya saki baki yana kallan dan nasa tun ba yau ba ya daɗe yanayin dana sanin tura ɗan nashi kasar mai jan kunne karatu, tun yana tatsitsinsa gaskiya ya cuci kansa wannan Abu yana damunsa ya rasa yadda zai yi bai isa yai masa faɗa akan duk abinda yake yi ba sai ya ce, shi dai ana san a takura masa, duk ya dauko dabi'unsu na lalata. Daddy da idanuwansa suka fara canja launi saboda ɓacin rai ya ce, "To wallahi bari in gaya maka in dai ba kai 70 IZGILI JAMILA MUHAMMED wani abu kan maganar aure ba daga nan zuwa karshen watan nan tuni zan yi wani abu a kai, kuma sai na baka mamaki.' " Yana gama fadar hakan ya mike dan yın Alwala dan ya ji masallacin kusa da gidan suna kiran sallah. Alhaji Mansir kwangila shi da Alhaji Umar mai akwai suna zaune a falon gidan Alhaji Umar din bayan gaishe-gaishe irin na abokanai, Alhaji mansir ya ce, "Gaskiya ina cikin damuwa.?' Alhaji Umar ya ce, "Ikon Allah Alhaji me ke damunka Alhaji Mansir ya furzar da huci mai zafi ya ce, "Akan yaran wajena Hisham ne, wallahi ina cikin ɓacin ran kaishi turai karatu banda karatu har da shedana da duk wata lalata ta turawa duk ya kwaso, to shi yasa nake IZGILI JAMILA MUHAMMED san in yi masa aure, tun lokacin dana kama shi da giya a firji dinsa nake cikin damuwa shi yasa nake san yi masa aure kasan aure abu ne mai girma kuma yana gyara mutum to gaba daya daya na rasa yarinyar da zan zaɓa masa mai hankalin wadda zata juri halinsa ta dinga tuna masa idan taga yana abunda bai dace ba, to na yi tunanin na yi tunanin na kasa zaɓar masa to kawai sai sai nana tattara nabarwa Allah lamarinsa ya zaɓa masa mafi alkhairi na kuma dukufa da addu'a sosai. Wani ikon Allah banyi sati da fara tsaiwar daran nan ba na fara mafarkin wata yarinya, to amma banga fuskarta ba, tana sanye da dogon hijabi har kasa ta juya bayanta da yaro a hannunta to tun daga lokacin ya zama duk lokacin da na kwanta sai na yi mafarki, to kwanaki da 72 IZGILI JAMILA MUHAMMED na zo nan muna magana sai naga wata yarinya zata wuce Islamiyar." Alhaji Umar ya ce, Zawuya ke nan.?" Alhaji Mansir ya ce, “Ita, ya ci gaba da cewa "Wato ranar da na ganta sai naga nutsuwarta da hankalinta nasan ta fito daga gidan tarbiya shi ne nake san in tambayeka ko ka san 'yar inace tana saka nikaf." Alhaji Umar ya dan yi nazari ya ce, "Gaskiya ban san ta ba, sai dai akwai wani yarona kama sanshi dan Audu, to zan sa shi ya binciko mana in da take da kuma 'yar gidan waye." " Alhaji Mansir ya ce, "To shi ke nan suka ci gaba da hirarsu akan harkokinsu da kuma hirar duniya. Cikin wulakanci ya kalli mai gidan ya daka masa wata gigitacciyar tsawa ya IZGILI JAMILA MUHAMMED ce; "Saboda tsabar baka s
🏠