ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 16

ka ke min wahala." "A haba da Allah Malama ina wahalar take." Salim ya mike "To ranki ya dade mu tafi kin sallameshi?" Ta dan zumbura baki "Kuna iya tafiya, amma ka tabbatar ka dawo dashi." Suka yiwa Goggo sallama tare da alKawarin zai zo gobe kafin ya wuce zuwa Kano. Washe gari tun da wuri Asma'u ta shiga kicin ta shiryawa Amuinu breakfast sannan ta yi wanka ta shirya, tana ta Allah-Allah ta ga ya iso. Sanye take cikin wani yadi material pink colour an yi masa wani tsadadden dinki, da yake gwanar kwalliya ce, yadin ya amshi jikinta ta yi kyau sosal.Aminu bai iso ba sai kusan goma da rabi na safe, duk yanda ta so boye damuwar ta sai da Aminu ya gane, anan fa ya yi ta rarrashinta har da durKusa mata "Haba Gimbiya yi min afuwaa dan saki murmushin da zai sanyaya min zuciya don Allah ki yi hakuri, 'amma ko ina da laifi na Salim ya fi yawa, dan ko shi ya hanani fitowa da wuri, amma duk rabin hankalina yana gareki, yanda tunaninki ya hana mini barci daren jiya hakan na wayi gare dake zuciyata, bana son ki dinga damuwa kin sani ko ina nake zuciyata tana tare dakc." Ta dake cikin shan mur "Kenan kana nufin har ka zo ka tafi ba za ka ci rin abincin gidanmu ba ko? Shi kenan na gode." Ya dan ta6e baki cikin tsokana "Wane ni ai ban isa ba, in ban ci girkin Gimbiyata ba, na wa zan ci?" farin ciki Ahmed yakira Asma'u waya "Kin ga mutuminki ya gudo Sokoto ko sallama bai-yi min ba saboda na ce ya tsimaye ni sal satin sama mu taho tare." Ta fadada murmushinta "Yo. don me zai. jiraka har sai ka gama yanga." "To ai gashi nan ya ZO sai ku hadiye juna mu ga Karyar soyayya." "Mhm ai ba mu masoyan da suka yi,hakan-ba bare mu ma mu yi." "Yo 21 5a) fara ta kanku domin mu san kuna 38 Suka saki dariya gaba daya. Asma'u ta bawa Tabawa mai aikinsu umarni shiryo musu. breakfast bryosu dasht. Daga nan ta ja Aminu zuwa lambun gidansu ta shimfida musu darduma tsakiyar madaidaicin lambun suka zauna nishadance suka yi breakfast tare, duk yan soye-- soyen da ta yi mai babu wanda ba) ci ba. Sun yi hirarsu sosai, irin ta masoya zukatansu cike da rr rs soyayya." Ta saki 'yar dariya gami da kashe wayar. Sai bayan Azahar Salim ya zo ya kaishi airportya hau jirgi ya tafi gida. Asma'u dai ba ta so tafiyarshi cikin kwana daya ba, to amma da yake ya riga ya gaya mata uzururrukan da suke gabanshi dole ta Kyaleshi, ya tafi. Washe gari Salim ya zo ya sa ta gaba ya matsa mata akan sai sun tafi Yola sun gano Mina. Sai da ta wanashi ta gama ja masa rai sannan dan kanta ta dawo tana jin tausayinsa, saboda yanda ya matsu dole sai ya je ya ga yarinyar, hankalinsa zai kwanta. Lallai so masifa ne ta fada ranta. Yamma liKis ce ta kaisu garin Yola, sai da suka fara zuwa gidan Hajiya Binta yar mahaifiyarshi anan suka yi sallar La''asar suka ci abinci, sannan suka dauki hanyar Kauyen su Mina, ba laifi suma yanzu rigar tasu ta hade da gari. Al'ummarsu sun ci gaba, duk mutanen garin sun waye, musamman ma matasansu da suka dan yi karatun boko, har gasar sayen motoci suke yi, sai ยข\ka ga matashi ya sayar da shanu ya sayi motar thawa, ya yi ta yawo gari yana fantamawa. Suna isa gidansu Mina gaba daya mutanen idan suka yi ta murnar zuwansu. Asma'u ta sami akkyawar tarba daga gurin Mina, amma kunya 39 14 ta hanata yiwa Salim magana, tun da suka gaisa ba ta ce masa komai ba, sai dan murmushi da ta dinga jifansa dashi. Bayan sun dan huta ya shiga wurin Baffansa Mina ta ja Asma'u dakinta suka sake suka yi hira sosai anan Asma'u cikin hikima ta dinga nunawa Mina irin matsanancin son da Salim yake mata abin ya bawa Mina mamaki saboda ta ji wai har yanzu Salim sonta yake don ita zatonta tuni ma ya mance da wata Mina, anan ta shaidawa Asma'u dududu bai fi wata daya kacal ta gama idda ba. Salim ganin da ya yiwa Mina ba Karaminfirgitashi ta yi ba, domin Mina da ya sani tana Karamar yarinya gashi yanzu ta zama mace sosai ta dada kyau ta dada fari ta goge sosai, dama can ba ta yi kama da mutanen Kauyen ba, dan ko ruwan ta na wayayyu ne bare kuma da ta yi aure birni gashi myin da ta fito daga hannunsa mai kudi ne ranar dai kusan kwana suka yi suna hira Mina ta saki jiki da Asma'u sosai ta dinga bayyana mata irin yadda take jin Salim zuciyarta, da yanda sonsa ya yi tsamari zuciyarta, har ta kasa kyautatawa mijinta, har ya gaji ya sakota. Kwanan su Asma'u daya suka koma Sokoto daga nan kuma ta yi shirin tafiya Kaduna domin yiwa mahaifiyar ta sannu da zuwa, sun je Umra sun dawo ita da mijinta. Sai da Salim ya kai Asma'u Kaduna sannan ya dawo ya tafi da ita, cikin makonni biyu Mama ta shirya komai da komai sai da ta gama shirinta sannan ta sanar da 'yan uwan mahaifin Aminu Kannen Babansa su hudu ne suka tafi Sokoto nemawa Aminu auren Asma'u gaba daya dangin uban Asma'u. Sun kar6i iyayen Aminu mutunce wata miskila ko sa'in'sa nan take suka .e zasu bawa Aminu auren 'yarsu bayan sun koma Mama ma ta zo Sokoton ita da aminiyarta yayin da Goggo ta yi musu jagora gidajen iyayen Asma'u, suka yi musu godiya. cikin satin ne dai Aminu shi da Ahme
๐Ÿ