NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 16

a wasu watanni? "Amma dai kin sani wancan lokutan bamu da damar auren juna, yanzu kuwa babu wata miskila muna da damar yin hakan ya kamata mu yi amfani da damar da muka samu mu hanzarta yin aure, dan mu mallaki junanmu hankalinmu ya kwanta, kin ga sannan zamu gane waye ya fi son wani cikinmu." Ta dan Kura masa ido "Kenan kana shakkun son da nake yi ma?" "No ba haka bane Mamace take gardamar cewa son da nake yi miki ya fi wanda kike min to sai gashi kuma da na zo gidanku Goggo tana Korafin wai Kaunarki ta fi tawa, gashi nan sona zai illata ki." Ta saki 'yar dariya tana dubansa "Tunda abin zama mujadala ai sai nemo musu alKalanmu Ahmed da Zaliha ko Salim su zasu raba gardama. Ya Kura mata ido yayin da ya mayar da maganar wasa "Don Allah don Annabi Asma'u ki yi min alfarma guda daya?" "Wacce iri?" Ta buXata hanzarce. 32 ae rn neil "Ki amince da aurenmu yi cikin mako biyu zuwa uku, walldhi mahaifiyata ta damu Kwarai da halin da nake ciki. Yanzu ma jira take na je mata da KwakKwaran bayani. Haba Asma'u ai ko ban fada ba kin san ina son ki, son da ya wuce tunanin duk wani mai tunani, ina Kaunarki Kaunar da ta wuce kwatancen mai kwatance ko kina shakka akan hakan?" Ta dan girgiza "Kai ni ban taba shakka akan hakan ba." "To idan kuwa haka ne me zai hana aurenmu wannan lokacin tunda muna son junanmu bamu da haufi akan Kaunar da mu kewa juna tunda har mun yarda da kanmu dan me ya sa zamu tsaya muna azabtar da zuciyoyinmu? Ko ke kina ganin idan muka dauki dogon lokaci bamu mallaki juna ba ba zamu cutu ba? Ke tunaniki in wani ya cutu cikinmu mun yiwa soyayyarmu adalci kenan?" Ta yi shiru yayin da ta nisa cikin tunani. Aminu ya fiddo wayarshi ya kira lambar mahaifiyarshi, bayan ya gaishe ta cikm girmamawa suka fara tattaunawa. Ta ce "Abba in ce dai yarinyar nan ba ta ba ka matsala ba?" Ya yi murmushi "Wallahi Mama ki kwantar 33 -_ da hankalinki babu wata matsala, Asma'u ta kusan zama tawa ba ki ji ni cikin nishadi ba. Yanzu ma muna tare, ba abin da yake zukatanmu sai farin ciki da annashuwa, ga ta nan Mama don Allah ki yi mata addu'a irin wacce kike yi min." Ya mikawa Asma'u wayar, sai da ta dan rusuna sannan suka gaisa da Mama ta ce. "Haba diyata Asma'u ya kamata ki rinKa jin tausayin mutumin naki, ki dan rangwanta masa nima tausayi yake bani. Cikin dariya ta ce "Shi kenan Mama ki yi hakuri na tuba, ba zan sake ba." Ita ma ta yi dariya "To Asma'u yanzu mene ne magana game da aurenku? Sai da ta yi dan dam! Sannan kunya ce ta ce "Mama ai magana na hannunki sai yanda ki ka ce dan ni ko gobe ki ka ce daura aure shi kenan. Ta yi 'yar dariya "Shi kenan diyata na gode, tun da kika hani wuKa da nama in sha Allahu nan da sati biyu ma kin zama amarya. Suka yi dariya gaba daya, sannan suka yi sallama, ta ajiye wayar. Ya juyo ya dan dubeta tare da sakar mata wani shegen murmushi "Iye «vaya ga amarya?" Ita ma murmushi kawai ta yi, wayarta ta 34 dade tana Kara amma ko kula ta ba ta yi ba, har ta gaji ta katse, hirarsu kawai suke mai dadi, dan haka ba ta so wani abu ya katse musu hirar. Amma ko da ta ga an sake bugowa sai ta dauka tana ganin Salim ne ta kara kunne "Hello sorry please wallahi Salim ban san kai ba ne." Cikin dariya ya ce "Ku ji ni da mutane, wai shin ina ku ka shiga haka?" Ta saki 'yar dariya "Tun da baka san inda muke ba to buri in gaya maka, muna nan garin masoya." "Wai me kuke ne?" "Soyayya mana." Gaba daya suka kwashe da dariya. Aminu ya amshi wayar ya ce "Haba Malam kar Ka fa takura mana da yawan kira, kama zuwa Yola mun fasa ba zamu'ba." Ya ce "Ayya komai za ku fada ku yi ku gama za ka dawo hannu nan gaba sai ka durkusa min, ba kana son ganin Asma''u, ina so ka sanar da ita cewa maraki fa ba abokin tafiya ba ne." Cikin dariya ya ce "Ahaf, shime kake kafin lokacin da zan durkusa maka ai ni kuma ina garin angwaye." "A haba da Allah kun ma isa ai duk gaggawarku dole ma ku jirana..." "Kai ina ana maganar sati biyu yaushe zamu tsimayi mai watanni biyu, gaskiya ba zai yiwu ba." Asma'u ta fizge, ta katse layin "Manta dashi damunmu yake son yi." "Ba ruwana idan na tafi ke zai tsiya." Jimawa aka sake bugowa, Aminu ya dauka. Satm din ne dai Sorryplease ku daure ku dawo da wurl, ma nan gidan Goggo ina jiranku da Allah wata unguwa nake son ka rakani. Idan ka biyewa Asma'u ba za ta bar ka ka taho ba." Cikin murmushi ya ce "Shi kenan kar ka damu ga maw nan akan hanya." Yajuya ga Asma'v ne ya ke so mu fita yawo, dan Allah ki yi hakuri ma koma gida yana can yana jirana, kia san Salim ya fi Karfin komai gurina. Wallahi Asma'a dalilinki ina Kaunar Salim sosai, in baya ga Ahmed babu wanda ya wuce Salim gurina. Suna isa gida suka tarar Salim yana zaman jixansu yana gaban Goggo suna tattaunawa. Kaya ne tule falon Goggo wanda Salim ya zo da gaba daya tsarabar Turai ce, wanda Aminu ya yiwa Asma'u, bayan Salim ya nunnuna mata ta dan girgiza kai gami da kallon Aminu. "Gaskiya kar ka sake yi min hidima irin wannan, ni kai nake so ba wai abin hannunka ba, ka gane? Don haka bana so
🏠