NOVEL SHARES -
awa irin ta aminan da suka yarjewa junansu." Salim ya ji dadi har cikin ranshi gami da sakin 'yar dariya A'aha, ashe dai ni din dan gata ne duk ni aka tanadarwa wannan gatan? Shi kenan na gode Allah ya bar Kauna da aminci sai na iso." Ya rufe layin. Makon da ya gabata Asma'u ta yi shi cikin
jin dadi da nishadi sabanin makonnin baya Salim
dai ya zo daga jihar Delta, kamar yadda ya yi mata alKawari. Yana isowa garin, wanka da sauya kaya
kurum ya tsaya yl gida, sannan ya nufo gdainsu Asma'u kai tsaye ya shigo ciki bai iske Goggo ba
sai Asma'u ya yi sa'ar samu kicin ya yi sallama ¢ikin muryarshi mai taushi da saurinta ta fito
taryarshi "A'aha mutanen Delta, saukar yaushe?" Ta fada tana dariya. Aina dauka ke ma Bayeraben
za ki ce min,
yadda Goggo ta sa min dan ita zatonta Kasar Yarabawa nake."
"Kai gaskiya Salim ka kyauta da ka zo
daidai lokacin da nake buKatar ganinka." Ya dan sakar mata murmushi "In dai damuwar ta ki duk ta rashin ganin Aminu ce to ki
sha kuruminki yana nan kan hanya don mun y! waya dashi yace gobe
zai biyo jirgi, don haka da
.gafe zan je airportna daukoshi. Ta rie baki "Ya aka yi ya yarda zai zo?"
"Ai na gaya masa ne kina nan kin kusa
haukacewa, idan bai yi gaggawar zuwa ba, muna nan zamu faso Kano kwanan nan." Ta doka masa harara "Haba Malam shi kenan
ka gama dani, yanzu yana can yana fasa kai ina hauka dominsa, ni kawai barin gidan ma zan yi kafin ya iso, ka san yanda za ka yi da shi." Ta
koma kicin wurin girkinta. Ya bita da gudu ya sha gabanta. "Wai yau ina ma Goggo tana nan, da ta ganmy rana. To bari ki ji Aminu bai ce zai zo Sokoto ba, dan ni ko maganar ki ma bai yi min ba."
razane ta dafe Kirj gami da jefa tambaya
wom
"Da gaske kake ba zai zo ba?" Ya dan kanne ido yana yi mata dariya "Ashe duk abin naki gulma ne? Gaskiya Asma'u son
gayen nan yana nema ya yi miki yawa kwanya." "Ka dai iya bakinka dan ko ina dauke da albishir,
ina so in fada ina so in Ki fada." "A haba da Allah gara dai ki fada." "Ni na ma fasa." Nan da nan ya shiga lallami har da durkusa mata ta ce "Bari dai na baka labarin Mina."
"Wacce Minar?" ya fada gami da zazzaro
ido. "Oh Minar suna da yawa ne?"
"O'o Kwaya daya gareni. Ta daga dan yatsanta
"To ka ga daya, biyu, uku...'"Me ki ke nufi?"
"Igiyar auren Mina gaba daya ta katse.... "Ki bari don Manzo?" Ya fada gigice. "Wallahi babu wasa, auren Mina ya mutu." nishadance ya dunkule hannuwa ya kai wa bango duka. "Lallai ashe zamu fasa zuwa Yola
"Ka ji ka da garaje, wa ya ce ma ana zance
akan idda? Ai ko za ka je gareta sai bayan wata uku, shi ya
sa Mommy ta Ki gaya maka,"
gobe-gobe.
24.
Ya ce "Wai tun yaushe auren Mina -ya mutu?" Asma'u ta ce "Ina jin zai kai kamar wata
guda.""Kai amma wannan miji na Mina akwai dan
arziki irin albarka."
"Nima sai da na zuba masa albarka." "Kin san yanzu abin da za yi, dole mu je
Yola bari Aminunki ya Karaso sai mu kai ki ki
gano min lafiyar mina, amma mu ba magana za Mu yi mata ba, sai mu dawo mi yi ta Kirga
kwanaki."
-. Ta dan yi dariya "Idan kuma ka tsaya sanya ~wani ya yi maka shigar sauri, dan kuwa bazawarar Kauye farin jini gareta." "Don Allah sunan nan ya fita daga bakinki, yarinyar 'yar baby da ita ki dinga kira mata wani bazawara." Asma'u dariya kawai ta tsaya tana yi masa
dan at san daga yanzu kuma basu da wata magana
in ba ta Mina ba, ya sake sakin dariya har da sowa
"Wayyo na gode Allah, nima aurena ya zo
gaskiya na ji dadi da ki ka gaya min ai da kin
Boye da kin cuce ni."
ys
Ta tsaya tana kallon shi, "Tun da na fada ina
tukwicina?" Of
oer "-©e a,'
"Kar ki damu ran ba ki tukwici, bari Goggo
ta dawo zamu tsara komai. Wai shin ina ma ta tafj ne?"
"Ta tafi gidan 'ya'yanta sai da daddare za ta dawo." "Kai gaskiya na so ganin Goggo yau din nan."
Salim ya je airport ya daukoshi kuma sam ya Ki yarda ya kai shi hotelya ce wannan karon shi ne mai masaukinsa, don haks kai tsaye gidansu ya
zarce dashi, ya yi breakfast can ya dan huta, sannan ya karkata hankalinshi da son ya je ya ga Asma'u. Tun da Salim ya lura Aminu ya matsu da son
ya je ga Asma'u sai ya yi ta tsokanarsa "Haba
kar ka ba da gayu mana, shin ba ka san
kai yaro ne maj tsada ba, ai bai dace ka yi gaggawar zuwa ta ganka ba. Kamata ya yi mu dan
ja aji sai mun ja mata rai sosai, irin zuwa gobe din
nan sannan miye gareta. "A haba da Allah an gaya maka zan iya wannan juriyar? In dai ba so kake na kwana ina maka kuka ba..."
Amunu ya iso Sokoto tun da sanyin safiya,
"Haba kuka? Sai ka ce wata Baby."
26
"Yo an gaya maka hawayen nawa tsada
greshi, in dai akan Asma'u ne ai kullum sai sun
kwarara. Salim ya saki
'yar dariya "Ba da kyau mutumina, ka ce ashe dai yau zan ga hawayen
soyeyya." Suka uifé suna dariya "Ka ga ni fa Malam
Kagauce nake bana jin zan iya kaiwa dare ban
dora ido kyakkyawar
fuskar mutuniyar ba." Salim yz ce "Ai ni vau dama ta samu dole ne na wana Asma'u ina jin ma sai na ga digon
hawayenta ko kuma sia ta durkusa min gwiwa bibbiyu da ta gan ka."
"Oh kai ka ce daman hawayenmu kake son
gani ba wan a